Yar Hilani

Yar Hilani
By Sule Konko

Wai kayi kida na yar hilani
Waka ta yan hilani

Wai waka ta yan hilani
A nanidi yan filani

In nayi haka yanzu babu laihi
In kayi haka yanzu babu laihi
Da guda guda zani yin kida na
Nine Sule Gwangwani na Jari
Nine Sule Gwangwani na Balkisa
Ai yaro rawa ya koya
Bai koyi rangwada ba
Don nima da kyar na koya
Da gudu da tsalle tsalle

Yar Filani
Wayon ki ya hana ki ki samu kudi
Wai ta gani tana so babanta ya hana ta ta sami kudi
Ko idan kana hanawa wata ran ba ka hana ba ta kwalhi ruwa
Ke in dai kudi kike so
Ai bari keya ta kwashi rairai ki samu kudi
Sule ba don hwarin wata ba da na chi yar hilani
Ko ga kalgo ko ga sabara ne in taushe yar hilani ta kwalhi ruwa
Ai ni na so diyar hilani sanda nike ma tsoro
Wan tabashedi yar hilani
Nace in kudi kike so
Ai bari keya ta kwashi rairai ki samu kudi

Bana bincike muke yi
Shekaral bana bincike muke yi
Mun bunciko mun ga na Jari
Ai mata kudi suke so ba hwarhwarin ido ba

In da hwarhwarin ido ne
Nono muke sawowa

Maza a hito a zo mu kara
Maza ku hito ku zo mu kara

A zo a buga
Mai karhi ya buga
Marar karhi ya kare kwarhi

Lallai yaro sai yaro rama
Yaro sai yaro rama
Yarinya sai yaro rama

Wai yal kwaraka
Haba yal kwaraka ki zo ki taba
Da Shahuda ma ta raya
Tazarya sai ki taba
Maryama don Allah ki raya
Aisha ma sai ta taba
Mangu doguwa ki raya
A’a gilgiza gindin ki yarinya zakuda zunbutu (yawwa)

Kyal dai a wuce mata iko
Kyal dai mu wuce mata iko
In gano na Gambo a gaishe ya ya biya kidana na gode

Dalliya nike yi Lawali yana riqo na
Na Alhaji Ilolo na Hauwa
Salisu Rabe ga ya nan dauka
Salisu Rabe na ta yin dauka
Niko Sule ga kida ina yi
Gidan radio muke malam
Ga shi nan muna yi (yawwa)
Umfani yana da kyau tsari na tana da kyau sam

In nayi kida na yar hilani
Isuhu Gwanda ina yininka
Isuhu Gwanda ina yininka
Ina kwana saboda gobe
S Sule Allah ya qara qauna
Birezi Allah ya bar mu tare
Nau Amadu godiya nike yi
Haruna da godiya nike masa ba don ina kida ba

Umfani ce ta dauki mai waka
Masauki na inda nike kwanci
Haruna kullun ya bani banti
In sha iska ina ware wa
In taba ya sosai Allah ya qara qauna (yawwa)

Yaya wasa
Yaya wasa

Daure yaro
Karye waka take aiki yaya nene

Wakar Mutuwa

Wakar Mutuwa
By Shatan Niger

Ashe mutuwa ke ba ki da sabo
Mutuwa ke ba ki da tausai
Ba raba kullum da da mahaifi

Ashe mutuwa ke ba ki da sabo
Mutuwa ke ba ki da tausai
Ba raba kullum so da masoya

Dan mu abin tausayi
Mutuwa ta dauke shi
Inna sai kiyi hankuri
Baba sai kayi hankuri
Mamman sai kayi hankuri
Aishar laraba sai kiyi hankuri

Ranar mutuwa ta Dirko
Ranar rasuwa ta Dirko
Tau da malam Madun
Uba na da ranshi yana gida
Amma ma da ranta tana gida
Amma yana yi maraye cikin gida

Ranar mutuwa ta Dirko
Ranar rasuwa ta Dirko
Tau da malam Madun
Uba na da ranshi yana gida
Amma ma da ranta tana gida
Amma yana yi maraye cikin gida

Bayan rasuwa ta Dikko
Bayan rasuwa ta dikko
Mutanen da sun san mu tare
Da sun ganan sai suyi ta hawaye

Mutawa ke ba ki da sabo
Wallahi mu mun so ki raga shi

Mutawa ke ba ki da tausai
Wallahi mu mun so ki raga shi

Ka ga raqumi kaga buzu
Ka ga raqumi kaga buzu
Yau sai ga buzu ba raqumi
Tun da yau bani da abun kai na

Lokacin da Birko na nan
Kullum muna a tare
Aiki tare mu ke yi
Tuhwahi muna iri dai
Har ma ana ce mu na tagwaye
Har ma ana ce mun ka ije mu

Ga Birko bai maka laihi
Ga Birko bai zagin ka
In ma kai mashi laihi
Ga Birko sai dai yayi murmushi
In ma kai mashi laihi
Ga Birko sai dai yayi dariya

Ubangiji ni kai na roqa
Allah Rabbi ni kai na roqo
Ka sanya kwantawa hutawa

Ubangiji ni kai nika roqo
Allah ni kai na roqa
Ka sanya kwantawa hutawa

Haka

Dan mu da abin tausayi
Mutawa ta dauke shi
Inna sai kiyi hankuri
Baba sai kayi hankuri
Mamman sai kayi hankuri
Aishar laraba sai kiyi hankuri
Mu duka sai muyi hakuri
Tunda mai dauka ta daukai
Mu duka sai muyi hakuri
Tunda mai dauka ta daukai

Ashe mutuwa ke ba ki da sabo
Mutuwa ke ba ki da tausai
Ba raba kullum da da mahaifi

Ashe mutuwa ke ba ki da sabo
Mutuwa ke ba ki da tausai
Ba raba kullum so da masoya
Dan mu da abin tausayi
Mutawa ta dauke shi
Inna sai kiyi hankuri
Baba sai kayi hankuri
Mamman sai kayi hankuri
Aishar laraba sai kiyi hankuri
Mu duka sai muyi hakuri
Tunda mai dauka ta daukai
Mu duka sai muyi hakuri
Tunda mai dauka ta daukai

Ubangiji ni kai nika roqo
Allah ni kai na roqa
Ka sanya kwantawa hutawa

Ubangiji ni kai nika roqo
Allah ni kai na roqa
Ka sanya kwantawa hutawa

Ma su saurariyo amfani
Ma su saurariyo fereye
Ma su son bonjour le Niger
Ba zaku jin kuma muryar dadi
Ba zaku jin kuma muryar dadin…