Matar Aurena

Matar Aurena
By Mahmud Nagudu

Matar aure na mai siffar da nike nema
Mai kyawo sannan ga kyan halayya mai girma
Mai addini don duban ga duba iyaye na

[Chorus]:
Mata mun taro mai halin ka muke nema
So kai alfarma domin mun zo neman dama
Jin dadin mata aure babbar sunna

Aliya suna na zabiya mai tarin waqe
Laifi na rtuba halayya ta na sake
Ban qara gudun ka alqawari ni na dauke
Ko ma dai kin sake zuciya ni tun tuni ni na wanke
Rai na na miqa wa Hajar don ta yi raino na

Chorus

Ke kuma yan mata zo ki gaya mani sunanki
Sunana Sahaira mai kyawon ban mamaki
Bayan kyan sura sai ki gayan addininki
Ina sallolin na biyar ba na qaran aiki
Ai Hajar ta fi ki da nafila ga maqagi na

Chorus

Zainabu yar boko ni ce wacce ake zance
Babana akwai naira ba sama duk sun tantance
Har dai ka ga na nace aure na sai mai dace
Ai ko kin nace Hajar ni na tantance
Ita dai ce buri na mai share mun kuka na

Chorus

Ni Aisha suna na yar dangin ku ku karbe ni
Ni kyakykyawar ya ce yar boko mai addini
Zan yo tarbiyan yaya in har ka aure ni
Tarbiyya ta fi ki Hajar har ma addini
Ko mai na yi mun muni in Hajar na dama na

Chorus

Mata mun taro mai halin ka muke nema
So addini don duban ga duba iyaye na

Mata mun taro mai halin ka muke nema
So kai alfarma domin mun zo neman dama
So addini don duban ga duba iyaye na

Choirus

Ni kau Fatima suna na ya ta fulani kyakykyawa
Nunan domin ki idanu na jujjuyewa
Na riqe addini boko ba qaqqautawa
Na yo gurin auren wannan ya kyakykyawa
Ai Hajar ta riga ki daki na sai tai kwana

Chorus

Hajar ba komai gun mu abu biyu nai riba
Dukkan mata gefe na basu dosa ba
Tunda kin ce sai ni alqawari ba kwancewa
Ka zamo tsani a madubi na kai nai duba
Godiya nai wa Allah ya rataya mani sulke na

Chorus

Matar aure na mai siffar da nike nema
Mai kyawo sannan ga kyan halayya mai girma
Mai addini don duban ga duba iyaye na