Mata Ku Yi Aure


Mata Ku Yi Aure
By Mamman Shata

Don Sallah da Salatil Fatih
Don darajar kakan Tijjani

[Chorus]
Don Sallah da Salatil Fatih
Don Allah mata kuyi aure

Don Sallah da Salatil Fatih
Don Allah mata kuyi aure

Chorus

Don Sallah da Salatil Fatih
Don darajar kakan Tijjani
Kun ji kidan da nayi wa mata
Kado ya so ya wulaqantani

Chorus

Alhaii bai taba yin zambo ba
Ni kuma bana zagin kowa
Kun ga dugunzuma ya sa nayi
Allah ya isa Kadon Bauchi

Chorus

Wai don na ce mata suyi aure
Shi ko ya ce masu kar suyi aure
Mun sabani a Jos
Mun daidaita rannan a bikin Babangida
Sai a Kaduna ta koma danya
Ya zagi su Lalo gidan Mai-koko

Chorus

Amma fa uwata in za’a yi mani aure
Goggo idan za’a yi man aure
Inna idan za’a yi mani aure
Baba idan za’a yi man aure
KAwu idan za’a yi man aure
A bar ni in zabi fari kyakykyawa
Kar da a bani baqi mummuna
Auren tilas ba aure ne ba
Shi kesa wasu yawon banza

Chorus

Don na taba jin a wurin babana
Shima ji yayi a wurin kakana

Chorus

Bashar Dan Musa

Bashar Dan Musa
By Mamman Shata

[Chorus]:
Na gode wa Bashar Dan Musa
Mamman nai mulkin Daurawa

Babba Bashar Dan Musa Mamman
Za ka fa gaba toron giwa

Chorus

Gaba gaba toron giwa Mamman
Mai mulkin Daurawa

Chorus

Yau tsakanina da Bashar Dan Musa
Allah shi ya sani, ni sai shi

Chorus

Yau tsakanina da Bashar Dan Musa
Allah dai ya sani ni sai shi

Chorus

A wajen da Bashar ke ban mamaki
In da Bashar kuma ke ban tsoro
In ya tashi yana raba kaya
Mamman yana rabon nairori
Muhamman nihar tausai nai naj ji

Chorus

Yace mani, mai waqa ta Shata
Mamman kul kada ka ji tausan sarki

Chorus

Idan na dauki kidan gangata
Ga makadana
Ga yan amshi
Duk da maroka na biye baya
In na dau wakar Dan Musa
Mamman wai har tausai yaj ji

Chorus

Ni ko nace wa Bashar Dan Musa
Ga waka, kada ka ji tausan shata

Chorus

Kai! Yara sai da nace wa Bashar Dan Musa
In dai an ce sallar gani
An ce sarki na nema na
Matukar na zo birnin Daura
In aka ce maka sarki ya hau
Kana ga sarki ya sauka
Ya sauka lafiya Dan Musa
Ya hau da lafiya Dan Musa
To ga ni gare ka ka ina bankwana
Mamman sai badi rai kuma ya kai

Baba ga ni gare ka ina bankwana
Muhamman sai badi rai kuma ya kai

Chorus

Muhammadu sai badi rai in ya kai
Koko san da kake nema na

Chorus

Muhammadu sai badi rai in ya kai
Koko san da kake nema na

Chorus

Na Abdu zaki ka kadi mai dan karhi
Mamman jure kwaram sai gogai
Muhamman mai dauke dafi sai bauna
Mamman mai jure dahi sai bauna
Mamman jure fari sai tofa.

Chorus

Gama wata rana Alhaji Shata
An ce sarki ya yi kira na
Ya yi kira na birnin Daura
Har na gabaci birnin Daura
Mamman sai na wuce Dabiran
Zatonmu ka tahi bakin gulbi

Chorus

Mutanen Dabiran suka ce mani
Ya tahi sarkahi babban gandu

Chorus

Mutanen Dabiran suka ce mani
Ya tahi kar kahi babban gandu

Chorus

Mutanen Dabiran suka ce mani
Ya tai sai kahi babbar gona

Chorus

Kai! Yara saida na ce wa Bashar Dan musa
Ga ka gabanmu magajin Audu
Ga mu gabanka Bashar Dan sanda
Kana kallon mu, muna kallon ka
Muhammadu ban tuna komai baya
Mamman sai mutuwa sai tsufa

Chorus

Yau Muhammadu sai mutuwa sai tsufa
Sai kau in na rasa baban Sa’i

Baba ruwan dare baban Sa’i
Mai game duniya baban Sa’i
Muhamman jikan Abdu tsoho

Chorus

Na Abdu jikan mai kai gaba rugga

Chorus

Fada wa Mamman duk wata Magana sai na zo

Chorus

Fada musu in tafiya tai nisa
Yaro kauce ga manya nan

Chorus

Wajen da Bashar yabban mamaki
Ran nan ne na kwan kakabi
Zuwan ka Potaskum baban sa’i
Da ka gama yaka Bashar Dan Musa
Mamman ka yi ta mai dan karfi

Chorus

Sarkin Fika yace Dan Musa
Mamman wata maganar sai dai ku

Chorus

Shehun Borno y ace Dan Musa
Muhamman wata rigimar sai dai kai

Chorus

Uhm! Sarkin Zazzau in a Dan Musa
Muhamman mai dauke kwaram sai goga

Chorus

Shehu Nagwaggo ya ce Dan Musa
Mamman namiji madaukin fansa

Chorus

Uhm! Sarkin Gumel yace Dan Musa
Mamman da dai ne kuma sak chif

Chorus

Uhm! Har mai Hadeja ya ce Dan Musa
Daukar Shatan nan sai dai kai

Chorus

A inda Bashar ya ban mamaki
Ga rigunan yaran mai waka
Ga rigunan makadan mai waka
Duk da marokana ya ba su
Ga taguwoyi ga wando nan
Ga huloli
kowa ya sa
Har ga kuddi a bai wa kowa
Balle ni makadin Dan Musa
To ! har na tafi can nay nisa
Nan sai na waiga daga baya
Tsaya kada in maka zancen mata
Mamman saura riga kurma

Chorus

Basher ya kawo rigar kurma
Can har nay tafiya nay nisa
Nasake nak domo daga baya
Shingin kada in maka zancen mata

Chorus

Muhammn sauran matar Bebe

Chorus

Baba yanda ya kawo rigar kurma, to haka
Turmin matar kurma
Ya Allah shi ma albarka mamman shi in ji matar shata
Yau abin da kake mamman DanMusa
Ya Allah shi ma albarka
Kuma Allah shi ma sakayya
Ya Allah ya ji-kan dattijo
Muhamman kuma in ji yaran shata

Chorus

Ni ko abin da yake DanMusa, Mamman ba ni fad’I sai dai ku
Irin fatan da na wa DanMusa, Muhamman sai Allah sai ko ni

Chorus

Mhm baba abin da kake wa DanMusa
Allah dai ke ma sakayya
Muhamman jikan Abdu tsoho

Chorus

Baba Bashar DanMusa
Mamman ja-gaba-gaba toron giwa
Mamman mai mulkin Daurawa

Chorus

Yau tsakani na da Bashar DanMusa
Allah shi ya sani ni sai shi

Chorus