Niger Nigeria

Niger Nigeria
By Fati Niger

Masoya makusanta
Alaqa ba cuta
Kusanci mai tsafta
Hulda ta mutunta
Adala da nagarta
Kusanci mariqanta

Niger Nigeria makwabta makusanta
Eh Niger Nigeria masoya makusanta
Niger Nigeria alaqa ba cuta

[Chorus x 2]:
Niger Nigeria masoya makusanta
Niger Nigeria alaqa ba cuta

Allah mai zamani madubin dubawa
Allah alfarmarka ba ta qarewa
Niger Nigeria na ke son waqewa
Yard a na yo azama ya zam ba qosawa

Chorus

Sannu ala khairul khalqillah dan baiwa
Gagara gasar mai gasa mai kintsewa
Wanda nake son biyarsa sau da qafa ta wa
Mai tsarkin zuciya na bude kan kowa

Chorus

Ehhh ya Allah Qadiri gwani masanin kowa
Yau danqo na zumuntaka zan zam qullawa
Niger ta zam qasar uba gun haifawa
Sannan Nigeria qasa gun zaunawa

Chorus x 2

Ehhh Niger Nigeria uwa daya gar Abba
Har Abadan abidina babu batun gaba
Soyayyar da’imun da tafi ta yan uba
Na zan Nigeria da Niger ba gaba

Chorus

Ehhh Masoya nay an uwa na mawaqa yan baiwa
Wanda zumuncin su da Niger bai qarewa
Ala alkannawi madubin dubawa
Adam na gudu har Nazifi na zam jerawa

Chorus

Hadiza diyar Mai Kano da Murja na sakawa
Maryam din fantimoti sangandalewa
Abdullahi maki har da Sa’a ta wa
Ibrahim El Sagir da Auwalu da baiwa

Chorus

Ni Binta Labaran ina son mai so na
Sani Hassan gaisuwa gareka na ke yi wa
Ga Ali mai jita ya zo ba kushewa
Nafisatu Sani tana bidar tai waqewa
Auwalu dan India masoyi son kowa
Abubakari Chika ya zo ba kushewa
Dalle buga mani ganga don nai wakewa
Mustafa a laffazi yak e yin waqewa
Mahhamudu na gudu gwani gun rerawa
Ga Zaharaddini Allah yai yo masa baiwa
Hauwa ta zo ta Ali baba yar baiwaaaaa

Masoya makusanta
Alaqa ba cuta
Kusanci mai tsafta
Hulda ta mutunta
Adala da nagarta
Kusanci mariqanta

Niger Nigeria makwabta makusanta
Eh Niger Nigeria masoya makusanta
Niger Nigeria alaqa ba cuta

Chorus x 3

Ala Gidigo

Ala Gidigo
By Fati Niger

[Chorus]:
Ayyare iye ala gidigo
Ayyare iye ala gidigo
Ala gidigo ala gidigo babu rodo
Ala gidigo

Ku yan mata muje wanka
Ku yan mata muje wanka
Ba dai wankan ba kar a ci rogon mutane
Ala gidigo
Rogo da kudi saiwa daya naira talatin
Ala gidigo

Chorus

Wayyo Allah zaqi na jiyo
Wayyo Allah zaqi na jiyo
Zaqi na jiyo in ji barawon zumata
Ala gidigo
Tilas ki biya in kin qi a daure ki gobe

Chorus

In da nice matar kyartai
In da kece matar kyarta
In na yi tuow sai in kasha kwaryar da gangan
Ala gidigo
In ya dinke mu yi aure
In bai dinke ba bakin aurensa kena

Chorus

In da nice matar kuturu
Toh in da ke ce matar kuturu
In baya nan sai in cika dakin da tsaidau
Ala gidigo
In ya taka mu yi aure
In bai taka ba a bakin aurensa kenan
Ala gidigo

Chorus x 2

Ke yarinya zabi dogo
Ke yarinya zabi dogo
Zabi dogo na dan wure dokin iyani
Ala gidigo
Ita mai wada turmi ta tuno
Turmi ta tuno zuwa gaba tad au kujera
Ala gidigo

Chorus

In da nice matar kurma
In da kece matar kurma
Sai yai nuni sai in gwada ban son kwatance
Ala gidigo
In yai Magana mu yi aure
In bai Magana ba bakin aurensa kenan

Chorus

In da gurgu ke aurena
In yau gurgu kika aure ke
Sai babu ruwa gidanmu in ce dauki tulu
Ala gidigo
In ya dauko mu yi aure
In bai dauko ba bakin aurensa kenan
Ala gidigo

Chorus

In makaho yaka aurena
In makaho kika aure ke
Sai za shi bara in ce masa kai bani sanda
Ala gidigo
In ya damqan mu yi aure
In bai daukan ba bakin aurensa kenan
Ala gidigo

Chorus x 2

Ayyare iye ala gidigo

Ala gidigo

Ayyare iye ala gidigo

Ala gidigo