Ala Gidigo

Ala Gidigo
By Fati Niger

[Chorus]:
Ayyare iye ala gidigo
Ayyare iye ala gidigo
Ala gidigo ala gidigo babu rodo
Ala gidigo

Ku yan mata muje wanka
Ku yan mata muje wanka
Ba dai wankan ba kar a ci rogon mutane
Ala gidigo
Rogo da kudi saiwa daya naira talatin
Ala gidigo

Chorus

Wayyo Allah zaqi na jiyo
Wayyo Allah zaqi na jiyo
Zaqi na jiyo in ji barawon zumata
Ala gidigo
Tilas ki biya in kin qi a daure ki gobe

Chorus

In da nice matar kyartai
In da kece matar kyarta
In na yi tuow sai in kasha kwaryar da gangan
Ala gidigo
In ya dinke mu yi aure
In bai dinke ba bakin aurensa kena

Chorus

In da nice matar kuturu
Toh in da ke ce matar kuturu
In baya nan sai in cika dakin da tsaidau
Ala gidigo
In ya taka mu yi aure
In bai taka ba a bakin aurensa kenan
Ala gidigo

Chorus x 2

Ke yarinya zabi dogo
Ke yarinya zabi dogo
Zabi dogo na dan wure dokin iyani
Ala gidigo
Ita mai wada turmi ta tuno
Turmi ta tuno zuwa gaba tad au kujera
Ala gidigo

Chorus

In da nice matar kurma
In da kece matar kurma
Sai yai nuni sai in gwada ban son kwatance
Ala gidigo
In yai Magana mu yi aure
In bai Magana ba bakin aurensa kenan

Chorus

In da gurgu ke aurena
In yau gurgu kika aure ke
Sai babu ruwa gidanmu in ce dauki tulu
Ala gidigo
In ya dauko mu yi aure
In bai dauko ba bakin aurensa kenan
Ala gidigo

Chorus

In makaho yaka aurena
In makaho kika aure ke
Sai za shi bara in ce masa kai bani sanda
Ala gidigo
In ya damqan mu yi aure
In bai daukan ba bakin aurensa kenan
Ala gidigo

Chorus x 2

Ayyare iye ala gidigo

Ala gidigo

Ayyare iye ala gidigo

Ala gidigo