Sana’a

Sana’a
By Dan Maraya Jos

Allaahu Mafiificin bayi
Shi yai sana’a yay yo aiki

Kadda mu daukaa har kullum
Aikinmu kawai shi ne aiki
Aikin wani ba aiki ne ba
Kada mu daukaa har kullum
Sana’anmu kawai ita cee sana’a
Sana’ar wasu ba san’aa ce ba

ldan muka dau wan nan hanyar
A kwana a tashi too wallahi
Na san sana’armu tana baya
Sannan aikinmu yana baya
Sannan ko qasarmu tana baya

In baa ku misali dan kima
Sannan ga wani dan yaro
Yai makaranta ya qare
Ya je shi Amerika zuwa London
Yazo gida nan ya zauna
Ga office ga littafi
Gaa masinja kofar office

Wanga wata ai yai aiki
An qi biya nai albashi
Yai haquri kuma ya qyale
Wanga wata ya danno ko
San nan yai musu dai aiki
An qi biya nai albashi
Yai haquri kuma ya qyale
Wanga wata in ya zo shi
Aka cee masa yaka taho aiki
Sai i ce musu ba ni iyawa don
Ko ba’a san darajar aikina ba

In ba ku misali kan sana’a
ldan kun lura da dan fenti
ldan kun lura da teloli
Mai faskare in kun gan shi
Haka dan amalanke da dan lodi
Duk wannan sana’a ce fa
A lokacin mota ta zo

Mai amalanke ka kirawo shi
Malam je ka kai man lodi
Yai lodi
Ya zo ya sauke
Ka qi biyanshi kudin lodi
Yai haquri kuma ya qyale
Gobe kace fa ije lodi
Ya je yay yo ma lodi
Yai haquri kuma ya qyale
Don ka qi biyansa kudin lodi
Jibi idan fa ka ce fa ije
Sai i ce ma ba ni zuwa domin
Ba ka san darajar sana’ata ba

Kadda mu dauka har kullum
Aikinmu kawai shine aiki
Kadda mu dauka har kullum
Sana’armu kawai ita ce sana’a
Sana’ar wani ba sana’a ce ba

Idan ka kalli dan taxi
In ka karbe shi a kan hanya
Baicin rana ta doke ka
Wait wait dan taxi
Yajja burki kau ya tsaya
Lambar gida fa ka bashi
Layi duk ka bashi
Ya kai ya sauke
Ka qi biyanshi kudin aiki
Yai haquri kuma ya qyale
An ko raba ku da kyar
A kwana a tashi ko wallahi
Rannan rana ta doke ka
Ga yunwa nan ta doke ka
Kak karbe shi a kan hanya
Wait wait da taxi
In ya leqa ya san kai ne
Sai ya ce ma ba na daukan ka
Domin baka san darajata ba
Ba ka san darajar sana’a ta ba

Mai Akwai Da Babu

Mai Akwai Da Babu

By Dan Maraya Jos

Amma mai akwai da babu duka danganta kanku dai dai
Allah ne yake fadan haka ba ni nake fada ba
Da ni nake fadan haka da sai ku karyata ni
×2

Kai mai akwai ka gane
Idan kai gida talatin cikin guda za ka je ka kwana
A daki guda ka kan kwan
A kayin gado guda dai
Haka nan wanda bai da komai
Gida guda za ya je ya kwana
A daki guda ikan kwan
A gefe guda ikan kwan
A kayin Karauni-Fallai,
Toh in gari ya waye
Ta nan duka dangantakan ku dai dai

In baku dan misali
kai mai akwai ka gane
In kana takamar akwai ne
Ba ka sanya hula goma a kanka kai dai
Ai da an gano ka sai ace wane ya tabu
Sai dai kasa guda dai
Hakanan Wanda bai da komai
Shi ma isa guda dai
Matukar in yana da hali
To malam idan ka duba
Ta na duba dangantakan ku dai dai

In baku dan misali
Da agogon jika talatin
Da agogon sule talatin
In wannan i bada loto dai dai wannan i bada loto dai dai
In za a dai kira su sai ka ji sunansu duk agogo
In baku dan misali
Da nonon sule talatin da nonon kobo talatin
In za ka dai zuba sai ka ga ai duk farinsu dai dai

Kai mai akwai ka gane in kana takamar akwai ne
Ba ka sanya takalmi goma akanka kai dai
Ai da an gano ka sai ace ga mahaukaci nan
Sai dai kasa guda dai
Hakanan wanda bai da komai
Shi ma isa guda dai
Matukar in yana da hali
To malam idan ka duba ta nan duka dangantakan ku dai dai

Kai mai akwai ka gane
In baka dan misali
Shi Allah huwallazina
Bai aiki da duk gidanka
bai aiki da arzikinka
sai dai da zuciya fa
Hakanan Wanda bai da komai
Allah huwallazina
Bai aiki da babu dinsa
Sai dai da zuciya tai
Shin malam idan ka duba
Ta nan duka danganta kanku dai dai

Allah huwallazina,
Kai mai akwai ka gane
In baku dan misali ,
Ran komuwa ga Allah
Kai mai akwai ka gane
In baka dan misali
Ranar komuwa ga Allah
Yadi biyar fari dai
A ciki za a nannadeka
Rami guda akan tona
Ka tuna ba a tona goma
Don wai kana da hali
A ciki za a turbudaka
Hakanan wanda bai da komai
Ran komuwa ga Allah
Yadi biyar fari dai
A ciki za a nannadeshi
Rami guda akan tona
Ka tuna ba a tona goma
Don wai wai bai da komai
To malam idan ka duba haka duka danganta kanku dai dai

Kai mai akwai ka gane
In middin kana da shi ne,
In middin kana da shi ne
Burinka shirya hairi
Kai taimako ga kowa
Ka taimakawa kowa
Ka agazawa kowa
Ka kyautatawa kowa
Ran komuwa ga Allah
Wallahi ka ji dadi
Bayanka sun ji dadi

In middin kana da shi ne
Burinka dai a bata
Ba ka taimako ga kowa
Burinka cin mutunci
Ko burinka cin amana
Malam akwan a tashi
Gidaje gami da mata
Sannan gami da mota
‘Ya’ya su zo su kare
Mota ta zo ta kare
Ka ga ran komuwa ga Allah
Kai ma kazo ka kare
Kaga ranar da kai da babu
Wallahi babu banban

Allah huwallazina,
Allah huwallazina,
Yayi Larabawa
Yayi Ingilishi
Yai wo mutan Amurka
Yayi Indiyawa ,
Allah huwallazina
Yai haka domin mu gane juna

In Baku dan misali,
Allah huwallazina,
Allahu yayi Gana
Yai Ethiopia ai
Yai Najeriyarmu muma
Ga shi duk bakake
Wani bai jin batun wadansu
Allah huwallazina yai haka domin mu gane junta

Amma mai akwai da babu duka danganta kanku dai dai
Allah ne yake fadan haka ba ni nake fada ba,
Da ni nake fadan haka da sai ku karyata ni

Gulma Wuya

Gulma Wuya
By Dan Maraya Jos

Sannan kun san boka dabam
Yar koren boka ma dabam
Gulma-wuya mai sha’anin tsiya
Mai son raba sunnar Rabbana
Kwatsam! O sai gat a cikin gida
Mai gidan nan na nan kin jiya
Shin a a ko ko ya fita
Sai ka ji dai matar gida
Ta cane O ai malam ya fita
Ta sami kujera nan da nan
Ga labara dan kadan
Na jiwo ne can ko a anguwa
Malam zai maki kishiya
Sai ka ji dai matar gida
Ta buga kirji nan da nan
Yanzu malam zai min kishiya?
Sai ka ji yar kore kuma
Ta ce mata lalle ai kuwa
Malam zai miki kishiya
Wannan ba shakka kuwa
Dagan an sannan in na tuna
Sai ka ji dai matar gida
Ta ce o yaya za na yi
Yar kore ta fada mata
Akwai wani bako nan a can
Can layin su magajiya
Ki tambayi mai gida
Za ki je kuma barker haihuwa
Mu hade layin su Magajiya
Mai gida in ya zo nan gidan
Sai ka ji dai matar gida
Ta chane
Malam zan tafi anguwa
Zan je barker haihuwa
Sai ta dauki gyalenta ta lulluba
Su hade layin su Magajiya
Rankai rankai in ka jiya
To da ma tun kan su zo
Yar kooren boka dada
Ta je ta wajen boka kuma
Ta gaya masa kome ya sani
Ga can sun ishe boka kuwa
Assalamu alaikum
Ai da ma na san za ku zo
kasan nan ta nuna mini
Kasa ba ta karya kuwa
Abin da dai kasa ta gaya mini
Wai malam zai miki kishiya
Kina kuma neman Haihuwa
Wannan ko lallai haka yake
Ba shakka kuwa
To sai ka ji mata ta chane
Malamin nan lallai ina gani
Abin day a daman wajibi
To shi ne ya gaya mini
Sai ka ji malam ya chane
Sai ka ji da matar gida
Ta ce
Malam yaya za a yi
Akwai ko yadda za a yi
Lalle zan miki magani
Ki ba ni farin rago biyar
Turmin alawayyo guda biyar
Ki ba ni kudin ki sule dari
Ki bani karauni guda biyar
Yanzun zan miki magani
Sai ka ji dai matar gida
Ta chane masa
Wannan abu mai sauki kuwa
Bari zan je chan ko cikin gida
Ta koma can gida
JAwo kwalla sayar
Jawo bokiti ma sayar
Ta tarar ta mika kudin
An kai wa boka nan da nan
Boka ya tattare
Boka ya handame
Je ki Allah zai mana magani

Auren Dole

Auren Dole
By Dan Maraya Jos

Uwa da uba ga gargadi
Uwa da uba ga gargadi
Shi auren tilas babu kyau
Shi yakan saka yara gantali

Uwa da uba ga gargadi
Kun ga aure tilas babu kyau
Shi yakan saka yara gantali

Domin Allah ba ya so
Annabin Allah ma ba ya so
Domin yai hani a yi

Malam wannan yar ka ce
Malam wannan yar ka ce
Ga wanda take so tun tuni
Tun suna yan yara kankana
Domin ta saba da shi
Shima ya saba da ita
Mutumin kau da ka saba da shi
Ai yana da wuya a raba kuwa

Sai ka ce mata ba ka bata shi
Sai wanda kake so za ka ba
In kai auren ka jiya
Kai mata auren dole wai
Sai ka ji lalle ta chale
Baba ya mini auren dole ne
Tunda an min auren dole ni
To zama a gidan ba dole ai

Sai ka ga ‘ya kuma ta fita
Ta je gantali
Kan a jima ta je Kano
Sai ka ji ta kai Samuru
Sai ka ji ta je har Gusau
Kan a jima in ka tuna
Sai ka ga ta kai har Kuta
Ko da kudin mato ta je
Ko babu kudin mato ta je

Uwa da uba in kun tuna
Wannan abu ku kuka haddasa

Idan da kudin moto ta je
In babu kudin ma to ta je
To uwa da uba in kun tuna
Wannan abu ku kuka haddasa
Kun san wannan laifin ku ne

Uwa da uba in kun tuna
Ni dai rokon ku nake ta yi
A bar auren tilas dada
Tunda da dai Allah ba ya so
Kuma Annabi yayi hani a yi