Mai Akwai Da Babu

Mai Akwai Da Babu

By Dan Maraya Jos

Amma mai akwai da babu duka danganta kanku dai dai
Allah ne yake fadan haka ba ni nake fada ba
Da ni nake fadan haka da sai ku karyata ni
×2

Kai mai akwai ka gane
Idan kai gida talatin cikin guda za ka je ka kwana
A daki guda ka kan kwan
A kayin gado guda dai
Haka nan wanda bai da komai
Gida guda za ya je ya kwana
A daki guda ikan kwan
A gefe guda ikan kwan
A kayin Karauni-Fallai,
Toh in gari ya waye
Ta nan duka dangantakan ku dai dai

In baku dan misali
kai mai akwai ka gane
In kana takamar akwai ne
Ba ka sanya hula goma a kanka kai dai
Ai da an gano ka sai ace wane ya tabu
Sai dai kasa guda dai
Hakanan Wanda bai da komai
Shi ma isa guda dai
Matukar in yana da hali
To malam idan ka duba
Ta na duba dangantakan ku dai dai

In baku dan misali
Da agogon jika talatin
Da agogon sule talatin
In wannan i bada loto dai dai wannan i bada loto dai dai
In za a dai kira su sai ka ji sunansu duk agogo
In baku dan misali
Da nonon sule talatin da nonon kobo talatin
In za ka dai zuba sai ka ga ai duk farinsu dai dai

Kai mai akwai ka gane in kana takamar akwai ne
Ba ka sanya takalmi goma akanka kai dai
Ai da an gano ka sai ace ga mahaukaci nan
Sai dai kasa guda dai
Hakanan wanda bai da komai
Shi ma isa guda dai
Matukar in yana da hali
To malam idan ka duba ta nan duka dangantakan ku dai dai

Kai mai akwai ka gane
In baka dan misali
Shi Allah huwallazina
Bai aiki da duk gidanka
bai aiki da arzikinka
sai dai da zuciya fa
Hakanan Wanda bai da komai
Allah huwallazina
Bai aiki da babu dinsa
Sai dai da zuciya tai
Shin malam idan ka duba
Ta nan duka danganta kanku dai dai

Allah huwallazina,
Kai mai akwai ka gane
In baku dan misali ,
Ran komuwa ga Allah
Kai mai akwai ka gane
In baka dan misali
Ranar komuwa ga Allah
Yadi biyar fari dai
A ciki za a nannadeka
Rami guda akan tona
Ka tuna ba a tona goma
Don wai kana da hali
A ciki za a turbudaka
Hakanan wanda bai da komai
Ran komuwa ga Allah
Yadi biyar fari dai
A ciki za a nannadeshi
Rami guda akan tona
Ka tuna ba a tona goma
Don wai wai bai da komai
To malam idan ka duba haka duka danganta kanku dai dai

Kai mai akwai ka gane
In middin kana da shi ne,
In middin kana da shi ne
Burinka shirya hairi
Kai taimako ga kowa
Ka taimakawa kowa
Ka agazawa kowa
Ka kyautatawa kowa
Ran komuwa ga Allah
Wallahi ka ji dadi
Bayanka sun ji dadi

In middin kana da shi ne
Burinka dai a bata
Ba ka taimako ga kowa
Burinka cin mutunci
Ko burinka cin amana
Malam akwan a tashi
Gidaje gami da mata
Sannan gami da mota
‘Ya’ya su zo su kare
Mota ta zo ta kare
Ka ga ran komuwa ga Allah
Kai ma kazo ka kare
Kaga ranar da kai da babu
Wallahi babu banban

Allah huwallazina,
Allah huwallazina,
Yayi Larabawa
Yayi Ingilishi
Yai wo mutan Amurka
Yayi Indiyawa ,
Allah huwallazina
Yai haka domin mu gane juna

In Baku dan misali,
Allah huwallazina,
Allahu yayi Gana
Yai Ethiopia ai
Yai Najeriyarmu muma
Ga shi duk bakake
Wani bai jin batun wadansu
Allah huwallazina yai haka domin mu gane junta

Amma mai akwai da babu duka danganta kanku dai dai
Allah ne yake fadan haka ba ni nake fada ba,
Da ni nake fadan haka da sai ku karyata ni