Auren Soyayya

Auren Soyayya
By Aminu Rinji Bagwai

Auren soyayya da dadi yake Allahu ya bani
Alkwarin qauna ki riqe ni amana don Allah yar’uwata

Chrous:

Auren soyayya da dadi yake Allah ya cishshe mu (wayyo Allah)
Ku rungumi junanku
Riqo na amana don Allah yan’uwa

Assalamu alaikum ya masoyi hasken alkhairi (wayyo Allah)
Annurin raina farar inuwa da zaman sirri (wayyo Allah)
A sansanin qauna da masoya da kai nake fahari (wayyo Allah)
Sonka nake nachi masoyi kai ne ka ceto rayuwata

Chorus

Na je ni ziyara gun qawaya wadda ta sha kurumi (wayyo Allah)
Na tarar da angonta a dakin sai suka koro ni (wayyo Allah)
Ga shi garin ya dau hadari ai kau ruwa ya doke ni (wayyo Allah)
Kafin gida na jiqe sharaf yau dole na bayyana damuwata

Chorus

Yau ga shi nima na kasance ni da abun raina (wayyo Allah)
An mani aure na yi bankwana da qawayena (wayyo Allah)
Fata nike Allah ya bar mu a tare da mai so na (wayyo Allah)
Allahu ya baka masoyi ka riqe ni aman dan’uwana

Chorus

A cikin lamari na zama na aure share hawayenki (wayyo Allah)
Abun da kike nema na soyayya yau na baki (wayyo Allah)
Yana deban kewa duk randa na kalli idanunki (wayyo Allah)
Ga ki da kyan sura abun da kike so kin samu yar’uwata

Chorus

Yawan kallonki yana zamewa annashuwan raina (wayyo Allah)
Kece mabodin sirrikan qauna da suke raina (wayyo Allah)
Ina fatan Allah ya hada mu a tare a Aljannah (wayyo Allah)
Tunani ya qare ya tattare sonki da qaunarki yar’uwata

Chorus

Ehh ki tashi ki bani ruwa ki kashe inji ki rage fitila (wayyo Allah)
Mu je mu ga jan barchi duhu na maraice ya tsala (wayyo Allah)
Mu gode wa Allah gwani da ya yo mu cikin daula (wayyo Allah)
Ga shi muna sallah muna azumi mu hade kanmu yar’uwata

Chorus

Abun da kake nema inai maka shi komai wahala (wayyo Allah)
Ba ni da kowa ban da komai sai kai sai Allah (wayyo Allah)
Inai maka albishiri zama na mutunci mun qulla (wayyo Allah)
Na kunno fitila kuma na kashe inji zo mu wuce dan’uwana

Chorus

Ina dimaucewa idan na ga kyawun surarki (wayyo Allah)
Bare in dago kaina in kalli fararen idanunki (wayyo Allah)
In gan ki fara santal tsarin surarki na mamaki (wayyo Allah)
Kuma ga ki da kyan gashi yana walwali da adon ribbon na mata

Chorus