Mandula 3

Mandula 3
By Ali Makaho

Zan koma nan
Ai tunda mandula ce
Sabuwar shekara
Hauwa yar mutan Nabaye

Wayyo Allah Marabar Jos

In na tuno Marabar Jos

Ii Hauwa mai Fura mai Koko

Ai tana burge ni

Hauwa mai Fura mai Koko

Hauwa mai Fura mai Koko
Da Ya’u Bala mai taba

Mai Ermon mai Rothman mai Benson

Da Qoqabu Uban Zaituna

Mai kwana rawa wuni sakarchi

Godia madallah

Bawan Allah
Sani Dan Ige mai nama

A nan muke samun Alhaji Ado Roti
Ii…. Alhaji Ummaru na Mududi

Ado Roti
Ni na tuna Ado nawa
Ado Roti
Ni na tuna Ado

Kaduna birnin gwamna

Yaka na baban Bawa
Dan da ya fada ya fasa

Na Ummaru Madobi

Ni dai a gareni
Wallahi Ali bai saba ba
Kuma bai fasa ba

Kwarai

Na je Maraba ya ba ni
Sannan ya bi ni Turayam
Ado yana qara mani
Unguwar Bawa
Ado ya bi ni ya ba ni

Allah Sarki malam

Na zo ni Birnin Zaria
Ado ya bi ni ya ba ni

I..

Da ka dube ni
Sai Murtala tane mani kyalli
A nan gaban goshi na
Daga nan har nai wani haske
Har ma na qara babban tumbi

Har ma ka kara babban tumbi na Zulai da malam Ya’u
Toh dama haka kake

Ado Roti
Na Halilu a gaishe ka
Toh na tuna Sanin Mani
Uban Commander Audu

Kaicho

Godiya madallah

Baba na Ado Roti
Ai wane Ado na Jamila
Godiya madallah
Ta Dandume sannu Jamila

Jamila Dandume

Na Dandume sannu Jamila x 2

Da Hauwa Maradi jikar Jauro

Hauwa Maradi jikar Jauro

Mai ban tumatari

Sa mutum tara kuka
Ka ji mai fari ba kwailin
Na gode mata ban raina ba

Chali boyi yaro

Kai fa da ne malam

Mun tafiya ba ka nan
Ni da Jaji Kilago
Da A. D. Gurmi
Da baba Dan Uche mai towul

Kaicho
Yane
Mai mata Zulai da malam Ya’u
Duk dunia kai take saurare a cikin cassette din Mandula na malam dan malam

Mun tafiya ba ka nan
Muka je mu sallah daura
Alhaji Wada Bursar
Ya bani kudi mai dama

E ye… ko.. kwarai..

Haka aka yin a samu labara nima

Ya bani kudi
Lissafa mani Chali

Toh malam

Ya ba ni forty naira

Daya…

Ya qara forty naira

Biyu malam…

Ya qara forty naira

Ukku malam…

Sannan ya bada fifty naira

Hudu malam…

Sannan ya qara forty naira

Hudu malam…

A. D. forty naira

Biyar…

Gilago forty naira

Shida bakwai…

Yar rawa forty naira

Takwas malam…

Su Merry yar Bangola
Kuma a baku forty naira

Goma kenan dan Zulai da malam Ya’u

Sabon ruwa kuma a baku forty naira

Arba’in sau goma sha daya

La ilan ha illallahu
Mai halin sarakan yanka
A yaba wa Wada Bursar

Alhaji Wada Bursar

Baba Uban Sailuba

Uban Sailuba

Uban su Farida
Baban Binta
Baban Aminu ban raina ba

Uban Binta uban Aminu uban Sailuba
Uban Farida

Da Ummarun Engineer
Na Mairo yar Kunama wannan

Kaicho

Mairo yar mutan Dutsanma
Shi kuma in ya zo
Naira dari yake miqawa
Dari yake qarawa
Kuma dari yake qarawa

Halinsu ne wannan

Adangwale suna na
Da ta bani rikodan nan
Amma a cikin Daura (x 2)

Ni tare da Dan Liti
Da Ummaru dan Dalle

Gidan ta ga yanmata lubu lubu

Taushe wuya ka naushe baki
Ga yanmata nan jijjiga mai kwai tunbul kaza
In ji ni Ali mai kunbe na Garba

Ga na Adangwale su Daura

Sai naje ni Kazaure
Garba dan Kano na Kazaure
Ya nuna mana halin qauna

Jikan na Gwamatse Dodon Gwari uban Basiru uban Basira Uban Jamilu uban Jamila

Kyan tafia dawowa
Chali boyi yaro
Wanda ya tafi bai dawo ba
Ai tafiyar sa ba tai kyawo ba

Toh ai tunda kace Kazaure sai kai maganar Alhajiya Fatsima BintaLadi yar Matsara
Eh…

Binta Fatsima Ladi
Ladi yar Matsara
Na gode maki ban raina ba

Kwarai kuwa
Ta Haladu Wazirin Alhaji Ado

Sai na gangaro Danbatta
In na zo Danbatta
Shugaban samari Alto
Na gode maka ban raina ba

Alto tuwo mai jin dadin zama da Hadiza da HAdiza yar Tambara Danbatta

Amma nai kunbi
Ni kuwa na yi tunani
Jama’a taro
Wanda bai ji sunansa ba
Sai yai haquri fa da mu
Don abun ne dai da yawa
Mutuwa da ta leqo kasuwa
Ko ba haka ne ba

Amma na duba
Idan na dau kunbe na
Wajen ina zan leqa
Za ni koma Sara
In tuna Isah Galadima

Alhaji Isah Galadima manya maganin qanana qanana

Buhun gero da na dawa
Da ni da A’i qanwar Dija
Y ace mu je mu sha shagalinmu
Haji Isha Galadima na Sara

Haka Allah ya yarda ya ga dama ya baka

Alhaji Dauda Ningi

Haji Dauda Ningi

Shugaba dan Marka

Na alhaji Shugaba dan Marka

Mu gaida Alhaji Dauda Ningi
Mai sa wuta na Yalwan Dutse
Na shugaba dan Marka
C. M. D. Alhaji Mashasha
C. M. D.Ah ah..
C. M. D. Alhaji Mashasha

Manya maganin qanana na Chiroma Isa Aliyu

C. M. D. Alhaji Mashasha

Uhhn..

Chiroma Aliyu mijin Asabebe

Chiroma Aliyu mijin Asabe uban Batula baban Ummi uban Sa’a
Chiroma Aliyu mijin Asabebe
Uhhm…

Chiroma Aliyu mijin Asabe
Ina C. M. D. Alhaji Mashasha

Ii..

Zani sauka Ukari
Don na gano C. M. D.
Dan sarkin Yesawa
Maganin Buhari da Sambo
Ranar Gora
Maganin mai kwarin kaye
Godiya madallah
Sai rabbana ya qaro qauna
Gobir jikan Gobir

Mandula 2

Mandula 2
By Ali Makaho

Wallahi sai Tunbi kake qarawa dan Zulai da Malam Ya’u da kyallin goshi

Ga gari da musulmi ni Ali ban ji kiran sallah ba
Gari da mahauta ni kuma ban ji a sai nama ba
Gari da kawarawa ban ji ana tallan suya ba

Yau ga ni a nan a Plateau
Na tuno Ibrahim Kura

Alhaji Ibrahim Kura na Kura masu naman wawa

Uban Sama’ila baban Rabi
Na kura ma su naman wawa

Na Alahaji Gidado Jari

Gaodiya Madalla
Na Gidado na Jada na gode maka ban raina ba

Na Alhaji Adamu Dan Kiyashi gwamnan nama

Na Dan Kiyashi gwamnan nama

Shine fa

Mai martaba na Garba na Kundum
Garba mijin Iye Hauwa
Wancan na can mahautar Bauchi
In ji ni Ali mai dan Gurmi Yaro

Sakkatare na Nafisa
Haba na Nafisa x 2

Uhh Sakatare na Nafisa

Haba na Nafisa x 2
Angon Delu
Yaka angon Jummai
Haba nawa na Delu nag ode maka baban baba

Dogon Yaro x 2
Wanne na mijin yawa Bauchi
Godiya madallah

Jedi mai Gurmi
Na tuno da Abdulqadir

Audu jikan Audu

Mijin yawa Bauchi

Audu mijin yawan Bauchi

Audu jikan Audu
Audu mijin yawa Bauchi

Audu jikan Audu

Chali boyi yaro

Kuma da ne malam

Za ni kai ka ka dan duba su

Allah Sarki dai toh malam dan Kana

Abdulqadir
Mijin yawa Bauchi
Shugaba na local government
Ni yana burgeni in ya bani yana qarawa

Ai a nan a Plateau
Ina da Alahji Musa Kurma
Godia madallah
Wannan na kamfanin tabar nan

Alhaji Musa Kurma na kamfanin Tobacco masu saida Rothman har Landi

Adamu gadar Sugai ma na gode maka ban raina ba

Mun tuna Adamu Sogai ma mai bamu yane mana qari

Sai Tudun-Wadar Dan Kadai

Allah Sarki malam

Tunda nan muka taso

Eh babu shakka malam

Tudun-Wadar Dan Kadai
Alhaji Isa Wayo

Manya maganin qananan yara

Na Zulai jikan Zulai
Wane Alhaji Isah Wayo
Godiya madallah
Allah yai masa sakayya

Alhaji Muhammed dan Alhajiya Baturiya ba

Ahmed Muhammed Sani

Ahmed Muhammed Sani

Kanen sarkin Gumel
Da yana Wudil gun wanki
Aiki ya dauke shi
Ya kai shi kafin Hausa
Sai Tudun-Wadar dan Kadai
Yanzu a chan fa yake zaunawa

Shi Ahmed Muhammed Sani fa yaro da gari tsarar manya

Dan Alhajiya Baturiya
Dan sarki Jikan sarki
Goyon Mamman Dan Kakale
Na gode maka ban raina ba

Allah Sarki kamar Ibrahim P. R.

Audu Dan Asabe x 4

Na Alhaji Isah Wayo
Na gode maka ban raina ba

Ai muna da Ummaru P. R. P ma dan Alhaji jikan Dodo

Ummaru bawan Allah
Dan Alhaji Dogara
Na gode Ummaru ye madallah
Na tuna dan Lantambai
Wanne Tambai baina
Na gode maka ban raina ba

Kwarai malam dan malam

Sannu dan Dalma x 2
Hamidu dan Dalma x 2
Na Muntari Qiru na gode
Wanne Muntari na Binta
Zakin Tudun-wadar dan Kadai

Manya maganin qanana qanana

Mandula
Yaro nada mandula

Tudun-wadar dan Kadai

Murde moli
Made angawila
Ina mai auna ruwa
Mijin na Delu mai ganganchi

Mijin na Delu mai ganganchi

Tafarnuwa yar hoyi

Allah Sarki malam

Na gode muku ban raina ba

Da Habubakar Garba direban motana Alhaji Audu

Da Garba mai spare
Ali ya gode maka bai raina ba

Garba mai spare yar Bauchi

Za ni je na Mapole
In ga uban dakina
Saje Muhammadu Rabi’u

Muhammadu Rabi’u

Saje Muhammadu Rabi’u
Na Kabiru nawa
Dan day a bani fegi kyauta

Allah Sarki malam

Da rijiyar gwan gwan
Na gode maka ban raina ba

Gwanin Azumi yarinya
Ai kwarya ko ta tsage
Na tabbata da sauran zane

Toh ai anan muke samun su Babangida Dan Gwangola na
Babaye mutan Ana Gandu Na Muhammadu mai Ulu

Saje Muhammadu Rabi’u

Allah Sarki

Saje Muhammadu Rabi’u
Na gode maka ban raina ba

Na gwamna ma su maganin munafiki da barawo

Saida ku kasa ke doka
In babu ku fat a lalace
Ko ba haka ne ba?

Haka ne dan Zulai da malam Ya’u

Ma’arun Jalo

Mai unguwar Habuja

Ma’arun Jalo

Wanda ba shi da mata shi kuma yaro da kwana gwauro

Bawan Allah Ma’arun Jalo x 2

Da A’i yar mutanen London

Mutumen kirki Ma’arun Jalo
Na shiga ban dauka ba
Bat a fidda barawo rannan

Chali boyi yaro

Mai Kaba da ne malam

Na ga abun mamaki
Abun day a dame ni
Abun da yake ban tausai

Ni fa ban gane ba
Irin haka ban gane ba
A sai fura ba a sai nono ba
Sare sarin a chi gaya kenan

Allah Sarki malam dan malam
Alhaji Tsoho Abdullahi
Na Alhaji Bawa dan mutan Arugungun
Na Alhajiya Maimuna a chi gyada