Mandula 2

Mandula 2
By Ali Makaho

Wallahi sai Tunbi kake qarawa dan Zulai da Malam Ya’u da kyallin goshi

Ga gari da musulmi ni Ali ban ji kiran sallah ba
Gari da mahauta ni kuma ban ji a sai nama ba
Gari da kawarawa ban ji ana tallan suya ba

Yau ga ni a nan a Plateau
Na tuno Ibrahim Kura

Alhaji Ibrahim Kura na Kura masu naman wawa

Uban Sama’ila baban Rabi
Na kura ma su naman wawa

Na Alahaji Gidado Jari

Gaodiya Madalla
Na Gidado na Jada na gode maka ban raina ba

Na Alhaji Adamu Dan Kiyashi gwamnan nama

Na Dan Kiyashi gwamnan nama

Shine fa

Mai martaba na Garba na Kundum
Garba mijin Iye Hauwa
Wancan na can mahautar Bauchi
In ji ni Ali mai dan Gurmi Yaro

Sakkatare na Nafisa
Haba na Nafisa x 2

Uhh Sakatare na Nafisa

Haba na Nafisa x 2
Angon Delu
Yaka angon Jummai
Haba nawa na Delu nag ode maka baban baba

Dogon Yaro x 2
Wanne na mijin yawa Bauchi
Godiya madallah

Jedi mai Gurmi
Na tuno da Abdulqadir

Audu jikan Audu

Mijin yawa Bauchi

Audu mijin yawan Bauchi

Audu jikan Audu
Audu mijin yawa Bauchi

Audu jikan Audu

Chali boyi yaro

Kuma da ne malam

Za ni kai ka ka dan duba su

Allah Sarki dai toh malam dan Kana

Abdulqadir
Mijin yawa Bauchi
Shugaba na local government
Ni yana burgeni in ya bani yana qarawa

Ai a nan a Plateau
Ina da Alahji Musa Kurma
Godia madallah
Wannan na kamfanin tabar nan

Alhaji Musa Kurma na kamfanin Tobacco masu saida Rothman har Landi

Adamu gadar Sugai ma na gode maka ban raina ba

Mun tuna Adamu Sogai ma mai bamu yane mana qari

Sai Tudun-Wadar Dan Kadai

Allah Sarki malam

Tunda nan muka taso

Eh babu shakka malam

Tudun-Wadar Dan Kadai
Alhaji Isa Wayo

Manya maganin qananan yara

Na Zulai jikan Zulai
Wane Alhaji Isah Wayo
Godiya madallah
Allah yai masa sakayya

Alhaji Muhammed dan Alhajiya Baturiya ba

Ahmed Muhammed Sani

Ahmed Muhammed Sani

Kanen sarkin Gumel
Da yana Wudil gun wanki
Aiki ya dauke shi
Ya kai shi kafin Hausa
Sai Tudun-Wadar dan Kadai
Yanzu a chan fa yake zaunawa

Shi Ahmed Muhammed Sani fa yaro da gari tsarar manya

Dan Alhajiya Baturiya
Dan sarki Jikan sarki
Goyon Mamman Dan Kakale
Na gode maka ban raina ba

Allah Sarki kamar Ibrahim P. R.

Audu Dan Asabe x 4

Na Alhaji Isah Wayo
Na gode maka ban raina ba

Ai muna da Ummaru P. R. P ma dan Alhaji jikan Dodo

Ummaru bawan Allah
Dan Alhaji Dogara
Na gode Ummaru ye madallah
Na tuna dan Lantambai
Wanne Tambai baina
Na gode maka ban raina ba

Kwarai malam dan malam

Sannu dan Dalma x 2
Hamidu dan Dalma x 2
Na Muntari Qiru na gode
Wanne Muntari na Binta
Zakin Tudun-wadar dan Kadai

Manya maganin qanana qanana

Mandula
Yaro nada mandula

Tudun-wadar dan Kadai

Murde moli
Made angawila
Ina mai auna ruwa
Mijin na Delu mai ganganchi

Mijin na Delu mai ganganchi

Tafarnuwa yar hoyi

Allah Sarki malam

Na gode muku ban raina ba

Da Habubakar Garba direban motana Alhaji Audu

Da Garba mai spare
Ali ya gode maka bai raina ba

Garba mai spare yar Bauchi

Za ni je na Mapole
In ga uban dakina
Saje Muhammadu Rabi’u

Muhammadu Rabi’u

Saje Muhammadu Rabi’u
Na Kabiru nawa
Dan day a bani fegi kyauta

Allah Sarki malam

Da rijiyar gwan gwan
Na gode maka ban raina ba

Gwanin Azumi yarinya
Ai kwarya ko ta tsage
Na tabbata da sauran zane

Toh ai anan muke samun su Babangida Dan Gwangola na
Babaye mutan Ana Gandu Na Muhammadu mai Ulu

Saje Muhammadu Rabi’u

Allah Sarki

Saje Muhammadu Rabi’u
Na gode maka ban raina ba

Na gwamna ma su maganin munafiki da barawo

Saida ku kasa ke doka
In babu ku fat a lalace
Ko ba haka ne ba?

Haka ne dan Zulai da malam Ya’u

Ma’arun Jalo

Mai unguwar Habuja

Ma’arun Jalo

Wanda ba shi da mata shi kuma yaro da kwana gwauro

Bawan Allah Ma’arun Jalo x 2

Da A’i yar mutanen London

Mutumen kirki Ma’arun Jalo
Na shiga ban dauka ba
Bat a fidda barawo rannan

Chali boyi yaro

Mai Kaba da ne malam

Na ga abun mamaki
Abun day a dame ni
Abun da yake ban tausai

Ni fa ban gane ba
Irin haka ban gane ba
A sai fura ba a sai nono ba
Sare sarin a chi gaya kenan

Allah Sarki malam dan malam
Alhaji Tsoho Abdullahi
Na Alhaji Bawa dan mutan Arugungun
Na Alhajiya Maimuna a chi gyada