Uban Makam Uban Gardaye

Uban Makama Uban Gardaye
By Mai Dai Sabon Birni

[Chorus]:
Uban Makama Uban Gardaye
Bawa sannu dakwanan yaki

Chorus

Alhaji Dandango jikan Geda
Ya wadata gari dan Mamman

Chorus

Alhaji Dandango jikan Geda
Ya wadata gari dan Mamman

Chorus

Baban shamaki sarki
Alhaji baban Jekadiya dan Mamman

Chorus

Dogo na Salihu jikan Gunda
Uban Hassan na Barayan zaki

Chorus

Dogo na Salihu jikan Gunda
Uban Hassan na Barayan zaki

Chorus

To zamanin na Habu dan Inna
Gobir ba a da sauran yunwa
To kuma ba a da sauran ragga
Kowa yay yi bida ya dace

Chorus

To zamanin na Habu dan Inna
Gobir ba a da sauran yunwa
To kuma ba a da sauran ragga
Kowa yay yi bida ya dace

Chorus

Ina mazan suke Sarkin Gobir
Ina mazan suke duk sun kare

Chorus

Ina mazan suke Sarkin Gobir
Ina mazan suke duk sun kare

Chorus

Yan sarki kowa yay gona
Tarmamen na Habu ya dace
Kos san bai iya banka tai ba

Chorus

Bawa uban Buli ikon Allah
In ka dauki mutum ya dace
In kau ka ki mutum ya tcine
Ban san mai iya kwasa tai ba

Chorus

Darzaje makiya dan Inna
Kowac ce ka ce shi yac ce
Sarki bai yi ma kowa sheri
To kumabai ci abin kowa ba

Chorus

Zamanin na Habu da Inna
Gobir ba a da sauran yunwa
To kuma ba a da sauran ragga
Kowa yay yi bida ya dace

Chorus

Na gode maka Sarkin Gobir
Alhaji Makada ya gode

Chorus

Na gode maka Sarkin Gobir
Alhaji Makada ya gode
Ga wata riga Sarki ya ba ni
Ta zuba kasa ta kai oba
Alhaji ya bi gari ya share
Ga dan Tasala da sarki yab ba ni
Na nad’a shi kamar dan daki
Har ya sa mini doron tilas

Chorus

Alkyabbag ga da sarki yab ban
Ta kara muna hasken hwada

Chorus

Ga hwan talatin sarki ya ba ni
In yi jajibiri ran sallah

Chorus

Ai kuddin sun wuce kwasan nama
Rago za mu saye ko dan sa

Uban Salau ya zo rangadi,
Amma Alhaji ni ban zo ba,
Sai ran da yaz zaka niz zo gai sai,
Dami dari da biyar yab ba ni.

Chorus

Kyautar na Iro uban Gardaye
Kyautar ta hi gaban na gode,
Sai dai ay ladabi ko shukura.

Chorus

In da na gaji sarauta birni
Da ko ba ni da kuddi an ban.

Chorus

Da in ba ka ba ni gari Hidi ba,
To ka nad’a muna ko Janzani.

Chorus

Amma Janzani ta ‘yan sarki ta
Da sarautar makada nik koma

Chorus

Amma Janzani ta ‘yan sarki ta
Da sarautar makada nik koma

Chorus

To kwamma ka ba ni gari Hidi
Ko da nig gab a su da kanhwab ba ni

Chorus

Dubi sa’ad da bida tak kama
Kullum niz zaka sai sun ba ni

Chorus

Dubi sa’ad da bida tak kama
Kullum niz zaka sai sun ba ni

Chorus

Na gode ma gari Hidi,
Hatta matansu da ‘yan matansu.

Chorus

Alhaji Bakawai ya shirya masallaci
Ya yo mana shi don Allah
Bai yi saboda bidar kuddi ba.

Chorus

Masallacin ga da kay yi na juma’a
Jika bubu da dari sun kare
Amma bag aria shiryat tai ba

Masallacin ga da kay yi na juma’a
Jika bubu da dari sun kare
Amma bag aria shiryat tai ba

Chorus

Ga latirin ga kuddin hwanho,
To kuria ba a gama tagogi ba.

Chorus

Alhaji Dandango jikan Geda
Ya wadata gari dan Mamman

Chorus

Alhaji Dandango jikan Geda
Ya wadata gari dan Mamman