Dan Kwali

Dan Kwali
By Sogha Niger

Dan kwaliiii
Ga wakar dan kwali

Dan kwaliiii
Ga wakar dan kwali

Iye nanaye ayye iye iye nanaye
Ayye iye iye nanaye dan kwali

Wai ni mareni, wai ni mareni, wai ni mareni
Wai ni mareni na ban tausai
Ba ta da inna ba ta da abba
Ba ta da sarmayin da ka sai mata dan kwali

Iye nanaye ayye iye iye nanaye
Ayye iye iye nanaye dan kwali

Dan kwali iri da iri ne

Babu wanda ban darma ba
Sai wancan na hanyar kwanni mai rabasha

Iye nanaye ayye iye iye nanaye
Ayye iye iye nanaye dan kwali

Ina tahiya ta
Sai tarar da malam zamne
Sai ya tokare ni da allo
Sai na hwadi bayan darni
Sai na haihi dana Bube
Amman bani ce mashi Bube
Sai dan malami da karatu da turanci

Iye nanaye ayye iye iye nanaye
Ayye iye iye nanaye dan kwali

A can da dauri
Anka ce yau wasa
Yan mata su sanyo kwalli
Sauran sai su sa jan-baki
Sai a hadu hilin wasa
Samari sai suna wilgawa
Ka ga wadda ranka yake so
Hittila ce kake matsawa
Rawa da waka rannan sai sahe

Iye nanaye ayye iye iye nanaye
Ayye iye iye nanaye dan kwali

Dan kwaliiii
Ga wakar dan kwali

Dan kwaliiii
Ga wakar dan kwali

A can da dauri
Anka ce yau wasa
Yan mata su sanyo kwalli
Sauran sai su sa jan-baki
Sai a hadu hilin wasa
Samari sai suna wilgawa
Ka ga wadda ranka yake so
Hittila ce kake matsawa
Rawa da waka rannan sai sahe

Iye nanaye ayye iye iye nanaye
Ayye iye iye nanaye dan kwali

Dan kwaliiii
Ga wakar dan kwali

Dan kwaliiii
Ga wakar dan kwali

Samarin Shaho

Samarin Shaho
By Sogha Niger

Soooyayyaaaaaa…
Allah ya bar soyayya
Soyayyaaaaa…

Soyayya kala kala ce
Soyayya iri iri ce
Soyayyan maso wani cuta
Kai kowa ya son mai so nai

Samarin shaho hankali da samarin shaho yan’mata

Yan’mata ku duba sosai
Ku sa hankali ku gane samari
Ku gane samarin kirki
A nan cikin masoyan naku
Ma su son ku da niyyar kirki
Don yan yaudara suna da dama
Sune samarin shaho

Samarin shaho hankali da samarin shaho yan’mata

Yan yaudara samarin shaho
Ganin kitse a ke wa rogo
In kin ganine su tsab sun shirya (lab lab lab)
Ga su wajen ki
Wannan magana mai dadi
Iya jan hankali yan’mata (toh)
Hattara yarinya
In bakki da dogon dubi
Da nazari da yin lissahi
Zai shirya gadar zare ram
Da kin hau ta kin hwada rami

Samarin shaho hankali da samarin shaho yan’mata

Soyayyan maso wani cuta
Kowa ya son mai so nai
Mai son ka baya sa lubutar ka
In dadi in wuya ga ku tare
Nema yake duk sahe
Allah ya kai ku hwagen aure (samarin kirki)
Allah ya kai ku hwagen aure (samarin kirki)
Eh Allah ya kai ku hwagen aure (samarin kirki)

Eh samarin shaho
Ku dibi idanun nashi
Ku dibi kahwahun nashi
In ka gane shi tsab ya shirya
Lab lab lab ga shi wajen ki
Wannan magana mai dadi
Iya jan hankalin yan’mata
Toh hattara yarinya

Ko kaine samarin shaho
Ku dibi idanun nashi
Ku dibi kahwahun nashi
Ko kaine samarin shaho
Ko kaine samarin shaho
Ehhhh (can dai)

Yan yaudara samarin shaho
Ya buge ki ki hwadi ya tsere
Ya bar ki nan kina wayyoh Allah
Ya cuce ni ya cuce ni

Ya cuce ni ya tahi ya bar ni
Ya cuce ya tahi ya tahi

Soyayyan maso wani cuta
Kowa ya son mai so nai
Mai son ka baya sa lubutar ka
In dadi in wuya ga ku tare
Nema yake duk sahe
Allah ya kai ku hwagen aure (samarin kirki)
Allah ya kai ku hwagen aure (samarin kirki)
Eh Allah ya kai ku hwagen aure (samarin kirki)

Uban Gida na

Uban Gida na
By Aminu Ala

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

In ban da bautar zuciya da bata tsirarwa
Ya za na tara abincin da ba ni cinyewa
Ya za na gina gida wanda ba shi dorewa
Ya za na tara tufafin da ba ni sanyawa
Ya za na dassa hasashen da ba shi dorewa
Ya za na shinfida daula da ba ta dorewa
Ya za na daura majanyin da ba za ya suncewa
Uban gida na da zaka dauki zance na
Da ka yi gyara kafin a gincire kwana

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Yey in banda bautar zuciya da ke halakkarwa
Abin hawa na ya zarce na hawan kowa
Rigar sakawa ta zarce ta jikin kowa
Gami da takalma sun fi kafar kowa
Dangi agogo na ya fice ta gun kowa
Daidai da zobe na ya fi hasashen kowa
Hatta da biro na alqalam na zannawa
Uban gida na da zaka dauki zance na
Wallahi da an gyara da tsakkiyar rana

Uhmm gida dubu na gina tanadin wajen kwana
Ciki da falo dubbai daban daban dana
Don tanadi na talauci da ke tsumin rana
Sannan in kauce wa idanduna da ke bina
In badda sawaye na ga masu bi kona
An dauke duniya mai tabbata gidan kwana
Gida ga mai burin rayuwa gidan gona
Uban gida na da zaka dauki zance na
Wallahi Allah da ka cikan muradi na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Yey mun zam bayi na ciki da ba shi turewa
Muna haqaya na mai rijiya da babu ruwa
Muna nutsewa qasa zuciya ta na qawa
Muna ta bautar gangar cikin mu ba qiwa
Muna biyewa al’aura muna tsiyacewa
Giya ta rai ta sa muna qara rudewa
Ina tunani da sani da ke a kwakwalwa
Uwar gida na da kin fahimci zance na
Wallahi Allah da an rufe tunani na

Ni zuciya ta kuma ta hana ni yin barci
Dare da rana kuma ba ragi na sassauci
Tana ta kakabi ko abinci ba ta ci
Cikin ta mamaki ya game ta ga qunci
Sannan tunani yai tarnaqi gadon barci
Ina ta mamaki kan hali na zalunci
Baqin maciji da ake kira da kumurci
Uban gida na bisa qarqashin tunani na
Yafe mu jin qan tsare nasa a tunani na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Duk inda ka ga qasa kan ture a kan ilmi na
Toh arziki da Buwayi ya basu dangi na
Ya zarce dukka buqatu na su da an tona
Sai dai idan jagoran su ya zamo bauna
Sai babu adalci gun su shugabanni na
Idan da adalci babu mai shiga rana
Kowan su ya zarce wa jibin sa dangi na
Ya shugaba na in an nazar a zance na
Wallahi Allah ya tseratar da mu quna

Hannun ka mai sanda yau na ke iyaye na
Nuni da nishadi nake wa baba na
Yau gyara kayanka ba shi maida mu rana
Ya shugaba na in har ka dauki zance na
Abin da ka tara ka aje gidan kwana
Da wanda ka yi bushasha kake tsumin qauna
Toh wanda ka bayar za shi yayi ma rana
Uban gida na in yanzu ka ga laifi na
Ai za ka gane ran tsaida mu cikin rana

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Ku taimaka mini gun dakatar da kuka na
Don kar na qarar da ruwan cikin idanu na
Suna da rana a gaba zubar hawaye na
Wai shin kwa ruhi da jiki da hankali da na
Sun yarda ranar tsayuwa tana tsumin kwana
Wai shin kwa labari na wuta da aljannah
Anya bani Adam ya aminta ko ni da na
Ya shugaba na da ka amince zance na
Mai za ya rude ka da handama tsakar rana

Uban giji na afuwar ka ni nake nemaaaaaaaaaa
Uban giji na gafarar ka ni nake nema
Uban giji na afuwar ka mu muke nema
Uban giji na sauqin ka ne abin nema
Uban giji na rahamar ka mu muke nema
Uban giji na gafarar ka mu muke nema
Uban giji na ceton ka mu muke nema

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Ciwon Idanu na

Ciwon Idanu na
By Umar M Shareef

Ciwon idanu na
Ki yi mani magani
Ine maki godiya
Kin ji masoyiya ta

Ciwon idanu na
Kayi mani magani
Ine maka godiya
Ka ji masoyi na

Amshe kiran da nai miki kiyi mani lamuni
Na makance idanu na ba sa gani
Na bi yi zafi na bi sanyi ke nake son gani
Kin ji sautin ki kawai shi zai warkar da ni
A rashin lafia na niyo kwanciya
Maganar gaskia ke ce magani na

Ciwon idanu na
Kayi mani magani
Ine maka godiya
Ka ji masoyi na

Ga ni da batutuwa don ke na tanada
Ba ni da gurin zuwa in ba kya gida
Ke zan kawo wa komai kika yo bida
Ba na mantuwa zance in kin fada
Kine mani kwarjini in da nake gani
A so son bayani ko ga abokai na

Ban jin zagar qawaye a soyayya kai na dauka
Ka share mani hawaye ka sa na daina kuka
In dai ina a raye sam ba na barin ka
Allahu ya kiyyaye ba ni son wanin ka
Kai ne dai daya a cikin zuciya
Mai saka ni dariya sannu masoyi na

Ciwon idanu na
Ki yi mani magani
Ine maki godiya
Kin ji masoyiya ta

Za ni zamo uwa cikin zuriyar ka
Za ni zamo surrika gun mahaifiyar ka
Ba ni barin damuwa ta isso gare ka
Babu jira dariya nai shirin ba ka
Ba ni so kai fushi na dau alwashi
Barin ka da qishi in ka shigo gida na

Ba ni so a mini zance in ba na ki ba

Ba ni so a mini kyauta in ba naka ba

Za ni rassa rai idan aure ba’a bani ba

Ban shirin zama da kowa in ba kai ne ba

Maganar gaskia a cikin zuciya
Ke ce ke daya ni na addana

Haaaaa Haaaaa