Uban Gida na

Uban Gida na
By Aminu Ala

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

In ban da bautar zuciya da bata tsirarwa
Ya za na tara abincin da ba ni cinyewa
Ya za na gina gida wanda ba shi dorewa
Ya za na tara tufafin da ba ni sanyawa
Ya za na dassa hasashen da ba shi dorewa
Ya za na shinfida daula da ba ta dorewa
Ya za na daura majanyin da ba za ya suncewa
Uban gida na da zaka dauki zance na
Da ka yi gyara kafin a gincire kwana

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Yey in banda bautar zuciya da ke halakkarwa
Abin hawa na ya zarce na hawan kowa
Rigar sakawa ta zarce ta jikin kowa
Gami da takalma sun fi kafar kowa
Dangi agogo na ya fice ta gun kowa
Daidai da zobe na ya fi hasashen kowa
Hatta da biro na alqalam na zannawa
Uban gida na da zaka dauki zance na
Wallahi da an gyara da tsakkiyar rana

Uhmm gida dubu na gina tanadin wajen kwana
Ciki da falo dubbai daban daban dana
Don tanadi na talauci da ke tsumin rana
Sannan in kauce wa idanduna da ke bina
In badda sawaye na ga masu bi kona
An dauke duniya mai tabbata gidan kwana
Gida ga mai burin rayuwa gidan gona
Uban gida na da zaka dauki zance na
Wallahi Allah da ka cikan muradi na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Yey mun zam bayi na ciki da ba shi turewa
Muna haqaya na mai rijiya da babu ruwa
Muna nutsewa qasa zuciya ta na qawa
Muna ta bautar gangar cikin mu ba qiwa
Muna biyewa al’aura muna tsiyacewa
Giya ta rai ta sa muna qara rudewa
Ina tunani da sani da ke a kwakwalwa
Uwar gida na da kin fahimci zance na
Wallahi Allah da an rufe tunani na

Ni zuciya ta kuma ta hana ni yin barci
Dare da rana kuma ba ragi na sassauci
Tana ta kakabi ko abinci ba ta ci
Cikin ta mamaki ya game ta ga qunci
Sannan tunani yai tarnaqi gadon barci
Ina ta mamaki kan hali na zalunci
Baqin maciji da ake kira da kumurci
Uban gida na bisa qarqashin tunani na
Yafe mu jin qan tsare nasa a tunani na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Duk inda ka ga qasa kan ture a kan ilmi na
Toh arziki da Buwayi ya basu dangi na
Ya zarce dukka buqatu na su da an tona
Sai dai idan jagoran su ya zamo bauna
Sai babu adalci gun su shugabanni na
Idan da adalci babu mai shiga rana
Kowan su ya zarce wa jibin sa dangi na
Ya shugaba na in an nazar a zance na
Wallahi Allah ya tseratar da mu quna

Hannun ka mai sanda yau na ke iyaye na
Nuni da nishadi nake wa baba na
Yau gyara kayanka ba shi maida mu rana
Ya shugaba na in har ka dauki zance na
Abin da ka tara ka aje gidan kwana
Da wanda ka yi bushasha kake tsumin qauna
Toh wanda ka bayar za shi yayi ma rana
Uban gida na in yanzu ka ga laifi na
Ai za ka gane ran tsaida mu cikin rana

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Ku taimaka mini gun dakatar da kuka na
Don kar na qarar da ruwan cikin idanu na
Suna da rana a gaba zubar hawaye na
Wai shin kwa ruhi da jiki da hankali da na
Sun yarda ranar tsayuwa tana tsumin kwana
Wai shin kwa labari na wuta da aljannah
Anya bani Adam ya aminta ko ni da na
Ya shugaba na da ka amince zance na
Mai za ya rude ka da handama tsakar rana

Uban giji na afuwar ka ni nake nemaaaaaaaaaa
Uban giji na gafarar ka ni nake nema
Uban giji na afuwar ka mu muke nema
Uban giji na sauqin ka ne abin nema
Uban giji na rahamar ka mu muke nema
Uban giji na gafarar ka mu muke nema
Uban giji na ceton ka mu muke nema

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na

Uban gida na da zaka dauki zance na
Aradu Allah da ka haye hasashe na