Sana’a

Sana’a
By Dan Maraya Jos

Allaahu Mafiificin bayi
Shi yai sana’a yay yo aiki

Kadda mu daukaa har kullum
Aikinmu kawai shi ne aiki
Aikin wani ba aiki ne ba
Kada mu daukaa har kullum
Sana’anmu kawai ita cee sana’a
Sana’ar wasu ba san’aa ce ba

ldan muka dau wan nan hanyar
A kwana a tashi too wallahi
Na san sana’armu tana baya
Sannan aikinmu yana baya
Sannan ko qasarmu tana baya

In baa ku misali dan kima
Sannan ga wani dan yaro
Yai makaranta ya qare
Ya je shi Amerika zuwa London
Yazo gida nan ya zauna
Ga office ga littafi
Gaa masinja kofar office

Wanga wata ai yai aiki
An qi biya nai albashi
Yai haquri kuma ya qyale
Wanga wata ya danno ko
San nan yai musu dai aiki
An qi biya nai albashi
Yai haquri kuma ya qyale
Wanga wata in ya zo shi
Aka cee masa yaka taho aiki
Sai i ce musu ba ni iyawa don
Ko ba’a san darajar aikina ba

In ba ku misali kan sana’a
ldan kun lura da dan fenti
ldan kun lura da teloli
Mai faskare in kun gan shi
Haka dan amalanke da dan lodi
Duk wannan sana’a ce fa
A lokacin mota ta zo

Mai amalanke ka kirawo shi
Malam je ka kai man lodi
Yai lodi
Ya zo ya sauke
Ka qi biyanshi kudin lodi
Yai haquri kuma ya qyale
Gobe kace fa ije lodi
Ya je yay yo ma lodi
Yai haquri kuma ya qyale
Don ka qi biyansa kudin lodi
Jibi idan fa ka ce fa ije
Sai i ce ma ba ni zuwa domin
Ba ka san darajar sana’ata ba

Kadda mu dauka har kullum
Aikinmu kawai shine aiki
Kadda mu dauka har kullum
Sana’armu kawai ita ce sana’a
Sana’ar wani ba sana’a ce ba

Idan ka kalli dan taxi
In ka karbe shi a kan hanya
Baicin rana ta doke ka
Wait wait dan taxi
Yajja burki kau ya tsaya
Lambar gida fa ka bashi
Layi duk ka bashi
Ya kai ya sauke
Ka qi biyanshi kudin aiki
Yai haquri kuma ya qyale
An ko raba ku da kyar
A kwana a tashi ko wallahi
Rannan rana ta doke ka
Ga yunwa nan ta doke ka
Kak karbe shi a kan hanya
Wait wait da taxi
In ya leqa ya san kai ne
Sai ya ce ma ba na daukan ka
Domin baka san darajata ba
Ba ka san darajar sana’a ta ba

Bulaliya

Bulaliya
By Sani Yusuf Ayagi

Randa duk kwana ya qare
Ko a daki ko a zaure
Ka rufe kofa da kyaure
Za ta zo ran za a zare ba da kai mata ja inja ba

Ba a jinkirta ma kowa
Ba a gaggauta ma kowa
Ajami ko larabawa
In ta zo ko sai macewa ko sakan ba a dadawa

Kun ji dai ku yan uwana
Manya manya da kankana
Za ta zo musu ko a gona
Ko a daki ne na kwana in ta zo baza su kwan ba

Malamai ko jahilawa
Ma su kurdi talakawa
Masu mulki duk gamawa
Za ta zo musu ba rabewa ba ganin matsayi take ba

Dubi ayar qur’ani
Kullu nafsin tai bayani
Za’iqatul mautu aini
Ko a kauye ko a birni babu wanda ba zai mace ba

Duk mutum da sanadinshi
Wani yai cuta ta jashi
Wani ba ciwo ta kaishi
Wani ko hadari silarshi babu yadda ba zata zo ba

Wani na yawo a titi
Wani na ciniki a kanti
Wani ko na shafa fenti
Wani ko ya kama kati bai sani yau zai mace ba

Wani na fama da aiki
Wani na sukuwa da doki
Wani na wanka a tafki
Wani ko ya kama wanki zata zo bai karasa ba

Wani ko na cin abinci
Wani ko sai yayi barci
Wani na fama da kunci
Wani ko a cikin takaici zai mace bai ma sani ba

Wata na tukin tuwanta
Wata tazo haihuwarta
Wata ko na kan gadonta
Zata zo dan zare ranta bada ta farka anan ba

Mutuwa ita ba ruwanta
Inta zo ba mai hanata
Babu mai ikon tareta
Masu mulki ko wadata dai cikinsu bazai hana ba

Ba ruwan mutuwa da mulki
Ba ruwan mutuwa da mulki
Ko na mai rawanin ga sarki
In ta zo tilas ta dauki ransu mulkin bai hana ba

Dubi jariri kamar shi
Sai yana hannun uwarshi
Ta riga ta rungume shi
Sai ta rabo tsaf ta jashi ga uwar bata ko hana ba

Ko ta dauki uwar ta bar shi
Ba ruwanta da tausayin shi
Bata duban wai uwar shi
Zata dau nono ta bashi in ta zo ba za ya sha ba

Mutuwa bata kulawa
Saurayi ko ya budurwa
Yanzu ta maishe su gawa
Babu sauran shaqatawa bako zata jira biki ba

Mutuwa ba raya shaho
Ta buge yaro da tsoho
Ta kade kuturu makaho
Wani ma tun kan a haihu zai mace ko ba da wai ba

Mutuwa har in ta sauka
A gida wani zata dauka
Ba ruwanta da masu son ka
Yanzu kaji ana ta kuka wanda bai hana dauke ran ba

Yanzu aya zan karanta
Yan uwa kowa ya jita
Ko wani zaiga ma’anarta
Yadda kowa zai kowa fahimta ba tare da na barta a dunkule ba

Aina ma kuntum ku gane
Yadrukumul mautu kune
Ai walau kuntum mutane
Fi burujun can daban ne yan uwa ban qarasa ba

Ma’ana Allahu yace
Ko ina ne kun kasance
Zata zo muku karku mance
Mutuwa Allah sa mu dace kan ta zo mana duk mu tuba

Kun ji dai zance na aya
Gaskiya ce babu qarya
Ko ina ne kun ka buya
Zata zo muku sai ku shirya ba shirin shan magani ba

Ga misali mai kulawa
Mursalai haka annabawa
Ga sahabu da auliyawa
Sun wafati da dadewa mu suwa ba za muje ba

In kana ji ne da kanka
Da isa ko dukiyarka
Ko yawan mulki gare ka
Can a baya akwai gabanka ya wuce bai dakata ba

In yawan bauta gare ka
Rabbi yai wani kan ayi ka
Wanda in bautar yafi ka
Daukakar ya sha gabanka ya wuce bai ko tsaya ba

Kunji tarihi da qissa
Annabin allah da kansa
Wanda babu mutum kamarsa
Musdafa an zare ransa ya waninsa ba zai mace ba

Wanda zabi anka bashi
Shin a dau ran ko a bar shi
Daha dan jarumtakarshi
Sai ya zabi a zare ranshi bai bukaci ya dakata ba

Dan uwa bar shirya fati
Kyale cin naman faranti
Tunda Annabi yai wafati
Babu mai ikon sabati duniyan nan bai mace ba

Da uwa da uba gare ni
Sai uban ya mace ya bar ni
Tun ina karami ku gan ni
Sai uwata ta riqeni har na girma ba zan rufe ba

Sai na girma gaban uwata
Sai ta kyautata rayuwata
Har ta min aure da kanta
Gashi yau ni na rasata ban ko samu kamarta dai ba

Duniyar nan ba kamarta
Shi yasa in na tuno ta
Yadda tai mini tarbiyarta
Sai nace Allah jikanta . . .

Gashi yau na samu kaina
Ba uwata ba ubana
Sun bace wa ganin idona
To ashe wataran kwa raina zai bace ba ko da wai ba

Yan uwa in kun fahimta
Duniyar da muke cikinta
Dole kowa zaya bar ta
Babu mai ikon suturta wai yace ba za ya kau ba

Dan uwa bari yin dagawa
Dan ganin ka samu baiwa
Bar ganin ka zarce kowa
Mutuwa na keyawayawa babu inda bazata je ba

Randa duk aka zare ranka
Yan uwanka suna ta kuka
Wanda bai dawo da ranka
Ai su ce allah jikanka zai ji ba sui ta kururwa ba

Burinsu kawai a kaika
A saka ka a kabarinka
Sai su zo kan dukiyarka
Sui rabo ba mai tuno ka sai kace basu sanka da ba

Da kana mulkin gidanka
Yanzu bamai girmama ka
Babu sauran bada doka
Babu mata yaya da jika sai kace basu san ka dai ba

Alhajin allah kamarka
Mai isa da isa ya sanka
Gashi yau likkafaninka
Ba a sa shadda a dinka sai farin alawayyo duba

Kaga tarin dukiyarka
Bata amfani gare ka
Duk yawan motar gidanka
Ba a kai ka a marsidinka sai kace ba taka ce ba

Dan uwa kar dai ka mance
Duk kudin nan naka nace
An yima gata fitacce
Sai a dau motar itace a saka ba marsidin ba

Matuqar sun girmamaka
Sug gine kabarin ga naka
Daga nan sun sallameka
Ko ziyara in gayama sai su shekara ba su je ba

Dubi duk girman gidanka
Sai ya zam kan gorashinka
Wanda ba ya shiga da ranka
Sai ya aure sahibarka ya shige ba’a mai hani ba

Dan uwa in an saka ka
A cikin kabaringa naka
Ko ina an toshe iska
Babu mai sha’awar taya ka shi zaman nan ba da wai ba

Sai a tashi kawai a barka
Daga kai sai dai halinka
Sai Nankir Munkir su sauka
Sush shigo don tambayarka duk da ko baka san guda ba

Sai a dawo ma da ranka
Sai su hau bisa tambayar ka
In ka amsa sai su barka
Sai a yalawata kabarinka ba a barshi a takure ba

In ko har suka tambaye ka
Babu amsa zaka koka
Sai su hauka kawai da duka
Sai a matse tsababarinka har gabobi duk su saba

Sai a nuna ma makoma
Hawuya koko jahima
Inda nan za kai ta fama
Har zuwa tashin qiyama babu sassaucin azaba

Dan uwa zan sake jan ka
Kar ka ce na tsorata ka
Zan yi ma zancen gidanka
Inda farko za a kaika sanda ka mutu ba da wai ba

Kwanciyar kabari tuno ta
Ba katifa zaka yi ta
Ba filo haka zaka kwanta
Babu juyi dan ka huta kaji ba qarya nake ba

Babu haske babu iska
Babu A.C. babu fanka
Kai ka dai ba sahibarka
Sai abinda kawai ka aika zai fito maka ba da wai ba

Kwanciyar nan ko a barka
Babu zagi babu duka
Kaita bacci dai abinka
Wata ran ka so ka fark bada an maka izini ba

To bare kuma babu tashi
Ga gumi zafi ka san shi
Ba rigingina sam cikinshi
Ya ka shirya zaka yi shi baka sa Allah gaba ba

Ka ji dai yanayin cikin shi
Gashi ya zama babu fashi
Dole kowa zai shige shi
Ya kamata ka tanaje shi da yawan zikiri da tuba

In gaya muku yan uwana
Kun sakankance ganina
Sai yawan sabo da barna
Kun sani da wuta da jannah ya ba mu yi musu tanadi ba

Shugaba kake ko ko gwamna
Ofishin nan naka auna
Wanda kai ka shige ka zauna
Sai ka dau biro ka zana kai zaton fa ba’a sani ba

In tuna maka kar ka manta
Kar ka yarda ka shirya cuta
Ko kadan ce kar ka yi ta
In ko kai to an rubuta ba ko gogewa ake ba

Kar ka ce ba’a ganinka
Tunda ba’a shiga wajenka
Sai da yin izini a gan ka
To ji Allah na ganin ka ga Rakib da Atid ka lura

Duk abinda ka ke ka gane
Shin na kirki ko tsiya ne
Su suna hangen ka zaune
Sun rubuta ko kadan ne basu kyale ko guda ba

Dan uwa komai ka shuka
Zai fito kaji babu shakka
Zaka girba kai da kanka
Randa ka mutu kai da kanka zaka zana ba da wai ba

Sai ka ce can na yi sata
Can ko na bai wane kyauta
Can ko naci haqqin maqota
Kayi alheri da cuta baka biye ko guda ba

In ka dubi mu’amalarmu
Mun sakankance ganinmi..
Shin ku dubi mu’amalarmu
Mun sake sam ba ruwanmu
Bamu tanyon yan uwanmu
Dukiya daga mu diyanmu ba mu ba kowa kwabo ba

Kasuwarmu idan ka duba
Bamu ware haram halar ba
Bamu san zi da ribaa ba
Bamu bar yin algushu ba sai kace ba zamu kau ba

Yan uwa tuni ni na lura
Mun sakankance da naira
Burikanmu kawai mu tara
Ba tunanin zamu saura bamu dau mutuwa a kwam ba

Ga shigarta kwarai ganina
Gashi mun cika cin amana
Ga yawan sabo da barna
Sabuka manya kanana yi muke qarya da giba

Ni abinda ka bani haushi
Dan adam sam ba ruwanshi
Bai kula da abin gaban shi
Ko hisabin dukiyarshi dan uwana bai kula ba

Wanga waqe yan uwana
Nayi dan wa’azi akaina
Dan na lura na gyara kaina
In rage sab’o da kaina in tuno mutuwa na tuba

Dan ganin ni na shagalta
Mutuwa bana tuno ta
Ban tunanin ya kamarta
Nafi kyautata duniyata lahira ban ko kula ba

Shi ya sani na wallafa ta
Dan tunawa zuciyata
Shi ya sani na wallafa ta
Dan tunawa zuciyata
Da akwai mutuwa gabanta
Ko da yaushe za ta zo ta ba kwa sa rana take ba

Nafi so naga na wadata
Na sayo babur da mota
Marsidis honda tiyota
Ga gidana har da kwalta can a gefe ba gari ba

In yi dinkin kece raini
Riguna ko wanne launi
Shadda boyal na aini
Nayi dan nima a sanni mai kudi ne ba kadan ba

Nan da nan kaga nai abokai
Masu kurdi har sarakai
Masu mulki malamai sai
Sui ta danqa min muqamai duk da ban iya godiya ba

Sai a ce an ban sarauta
Shugaban duka masu kyauta
Ai ta famar gayyata ta
Gun a fil fan nai ta kyauta ba ‘yar kadan ba

Malamai ko su zo gidana
Sui ta nema na mu gana
Sai a ce musu na yi kwana
Sai su sami guri su zauna basu san ko zan fito ba

Sai su qirqiri yin karatu
Ko su kawo min rubutu
Wai na sha dan kar na zautu
Dukiya haka sai da hutu kai magauta suc ci riba

Gun biki sai an jira ni
Duk ana burin a ganni
In na zo fa a kewaye ni
Ga maroka na zugani in yi kyauta ba kadan ba

To a sannan na gama ni
Dole kowa zaya bi ni
Yaita famar girmama ni
Sai ace komai sai an jira ni ko abin ni ban sani ba

Dukiya ta ja sarauta
Na zamo malam akan ta
Ba a qaryata magana ta
Sai a so ni maza da mata duk da ko ban san alif ba

Ba a qaryata magana ta
Ko a yaya ni nayi ta
Ko nace na shuka fata
Ta fito kuma naga dan ta wani zai ce ba da wai ba

To ana haka sai na gane
Duniya wani gun zama ne
Burinka da nake haram ne
Mai nutsar da mutum a zaune wanda bai dace da ni ba

Mutuwa ni ba ni san ta
Ba ni san na ji ambatonta
Dan tana kada zuciya ta
Take sai kaga na dimauta kwarjinin fa ba zai gushe ba

Na sani ita gaskiya ce
Naji lallai na amince
Zata zo ba kauce-kauce
To fa Allah na dimauce dan kwa ban mata tanadi ba

Mai ya sani nake gudun ta
Yadda malam ya fade ta
Gashi yadda ya suffata ta
Naga babu gwani a gunta yaya ba zan fargaba ba

Ba macewar nag guda ba
Mutuwa ni ba da wai ba
Ba ina kyamar ta ne ba
Karta dau raina ku duba kwanciyar kabari na duba

Na yi sabo ba kadan ba
Ga shi ba sadaka nake ba
Ni ko ban wata nafila ba
Ban yi aiki ma su kyau ba ya ba zan mata fargaba ba

Ni mutum ne mai kasala
Mai buqatar tara daula
Gani ba na son wahala
Banda sallolin farilla gashi ban wani tanadi ba

Inka duba ayyukana
Wanda dai ni nai da kaina
Manya manyan laifukana
Nai nadama ni da kaina Rabbi ba zan sake yi ba

In na dubi abinda nay yi
Laifuka ne masu nauyi
Sai jikina yay yi sanyi
Sai kawai roqon buwayi gafara ba sake yi ba

Tunda yanzu idan ka gan ni
Duk gabobi sun yi rauni
Ya gwani Ar-rahamani
Nayi rokona da nuni kaj ji kan Ummi da Abba

Rabbi wanke mahaifiyata
Dagga dukan laifukanta
Jallah nai roqo ka sata
Can gidan rahama ta huta ba da an mata bincike ba

Rabbi kaine Arrahimu
Shafe dukkan laifukanmu
Duk abinda mu kai ka bar mu
A gidan nai’mu ba da ka kula laifukan ba

Rabbi babana ka bar shi
Kar a bincika ayyukanshi
Nay yi roko jalla sashi
Cancikin firdausi sashi rahama bai sha wuya ba

Duk haqqina ya biya ni
Ya gwada mini Qur’ani
Makaranta shi ya kaini
Yayi min horo da nuni bai gwadan san zuciya ba

Ya gwani Allah karimi
Zul-jalal wal’ikirami
Nayi roqo ya rahimi
Kaj jikan dukkan musulmi hada kanmu mu daina gaba

Na ga nan ne ya kamata
Yan uwana in taqaita
In batun mutuwa na huta
Allah sa dai mun fahimta ba mu bar ta mu shantake ba

Wanda duk ya tsaya ya ji ta
Ko ya dauka ya karanta
Inda yagga kure cikinta
Yai yi himma dan ya gyatta sani bai wuce yin kure ba

Ma su neman wa yayi ta
Koko neman baitukanta
Adadunsu su bar daqauta
Zan fada gun kammala ta can a qarshe ba a nan ba

Hausa Mai Ban Haushi

Hausa Mai Ban Haushi
By Alhaji Aqilu Aliyu

Saba da samo gaskiya duk nisa
Sarari da Boye kadan ka so bunqasa

Ga gargadi ya zuwa gare mu zumaina
Yayan Arewa da wanda duk ke Hausa

Ni nan da kai shi ke da su baki dai
Ku nan na kurkusa har na cana da nisa

Jama’a, mu karkade kunnuwanmu na zuci
Zancen da zanmana shi mu ji shi mu amsa

Na ce ma ja damara bajau qaqqarfa
Mui qoqarin tafiya garinmu da nisa

Qwazo ya kyautu da mu mu nuna kuzarin
Inganta harshen namu shi ne Hausa

Ku mu bar kasala, sai mu himmatu kun ji
Zazzage dantsen nuna kishin Hausa

Da yawan karambani kawai na kutso
Ba wai gwani ne ni ba kai nic cusa

Na ambata mana gaskiya daddata
Suka da harshe gansami kakkausa

Na gatsa hancin gaskiya mai ganci
Gafinsa na da yawa, ina mai lasa

Sukukun makaka kiki kaka,kaf kin kam
Tirkashi aiki ya yi kwancin kansa

Tsotso tsuku tsakiya tsare mafitsara
Allah tsare ni da ku karo da nahisa

Tsomo ka tsotse gwamatso ka yi guntsa,
In ka tsaya tsaf ka yi tswai, ka nisa.

Saurin musaya Hausa mai ban haushi
Sassake sauyi an sakar wa Hausa
x 2

Zarafin da mamaki gwanin ban haushi
Mugun barin sha’anin Bahaushen Hausa

Kowa da yare nasa bai kyama tai
Mu gamu mun tozarta harshen Hausa

Wai don gadarar mun jiyo Turanci
Har ba mu son magana da harshen Hausa

Tsuntsu kamata yai da shi ya yi kuka
Ya irin na kaka nasa can mai nisa

Ku sani Bature ba shi kin Turanci
In ya game da kininsa ko a makasa.

Faufau, ba ka ga, ba ka ji mai yare ba
Ya nuna Ri ga kininsa, sai mu Hausa.

In har akwai biyu masu jin Turanci,
Kuma ga na ukku cikarsu duk yan Hausa

In kai na ukkun ba ka jin Turanci
Biyu din na tare da kai sukan kiye Hausa

Tafiya fa tai tafiya, ma lura ma juyo
An ka da mu, mui koKarin shan fansa

Abu namu ne, mu rike shi kankan ya fi,
In man yi wasa dole zai mana nisa.

Mu riqe kaho ke nan a more tatsa,
Nonon a sha mu sai suda mu yi lasa

An bar mu gangambu, kago na jinka
Wasu can su sha inuwa Sagas lallausa

To kun ga aiki namu, ci na wadansu
An karkasa musu arha, sai su yi
Kwasa

Ba cas bare as, ba da kau da kara ba
Swadadas su sulle can su sha bunqasa.

Ta sa ni wannan na tuno wata hira
Wato karin maganar wajen yan Hausa

Wai na ji cewa Wane ya kasa gwaza,
Gefe waje daya mun ji ya kashe kasa.

Ban kasa kwashewar kashin gwazana
Domin ganin tarin kasassar kasa

Ba shirya waka ko karin zance ba
Jama’a, gudajin goro ya dara farsa

Bai zamto ci gaba, ban da cinye baya
In ka ki tinkaho da harshen Hausa

Kai ne da yas I see Halo Good morning
Wai ga Bature babu yayin Hausa

Ka debe alfarmark ka warwatsar
Ka bar wajen nasara, ka doshi nahisa

Tsini ka so don son gwanintar banza
Ka kasa kunda lokaci mai nisa

Bai san ba mako, sai ya ce wai Sati
Sai kun taba shi ya ce iyaye Hausa

Kaka uba yayyensa har dangogi
Ba sa da wayo ban da harshen Hausa

To mun ji ba yare gare su daban ba
Zaa tambaye ka da namu harshen Hausa

Amma ka ban amsa da zaran na yi
Domin in san kai ne Bahaushen Hausa

Ga tambayar nan, ba ni amsa kwaf dai
Miye kashereke da harshen Hausa

Wannan abin kunya ina tamka tai
Harshen wajen kakanka kai ka kasa

Ya zam abin a yi dariya a yi gwalo
A gare ka don ka fadi ba shan fansa

Ka zam marar ra’ayi kurum kyakykyawa
Don ba ka alfahari da harshen Hausa

Ka zamo shafi-mu-lera soko an nan
An ya da kai an bar ka baya da nisa

Ban nuna na dara ku tulin wayo ba
Sai dai ina kishi ga harshen Hausa

Tsuntsu yana bisa yai tsuhu tsororo
Tsiwa ta sa hali ya zam kakkausa

Gutsuro ka tsoma tsangwama ce tsantsa
Gatsa tsuko tsotso ba sa zama lasa
Ba wai habaici ne ba ko kyara ba
kyale ni kurkusa kar ka kai ni da nisa

Wannan gajeren gargadin da na kawo
Yan Hausa allai sa mu ji shi mu amsa

Mu bi gaskiya sak ba ciri ba coge
Da digirgire kar dai na kai mu da nisa

Ka zamo maje gaba kar a bar ka a baya
Maza gwamatso kusa kar ka yarda da nisa

Kowa ya shirya bazararsa don ya yi tsalle
Mu ga mu nan da bazar rawar mun kasa

Nuni nake mana don mu lura mu gano
In mun sake wasu za su sha bungasa

Ba na habaici ko na gugar zana
Don ratayar kaya na dan buga kusa

Mu tsaya da kwazo, kokari da kuzari
Tsaiwar daka mu tsaya mu kange Hausa

Bai kyautuwa mu sake mu zo mu ci baya
Har ma mu daddawo taba ka yi lasa

Ai ma kamata yai muna gaba an bi
Mil za mu dangwala dis wasunmu su lasa

Kai yan’uwa mu zubar da aikin banza
Ni na fada mana gaskiya yan Hausa

Ku mu daina yin sha’awa zuwa feleke
Ita kankara ku tuna fa ba to malasa

Mu zubar da kalen yare-yaren kowa
Mu kula da amfaninmu harshen Hausa

Ku mu kyautata ku mu kara inganta shi
Duk duniya bakinmu ba shi makusa.

Girma gare shi tuli akwai alfarma
Ba kankanen abu ne ba harshen Hausa

Da yawa yakan rika gwamatsa Larabci
In ban da Arabi ina misalin Hausa

Mui takama da abinmu, shi ne daidai
Shi ne abin faharinmu harshen Hausa

Ku ga dai su o’o da ban kira suna ba
An garzayo da gudu a kwashi rahusa

Amma fa ni ba zan yi ma rata ba
Mai tambayar suna taho ka ji amsa

Ni dai Akilu Aliyu nai wakena
Ba don a ce mini na fi kowa Hausa

Tafiya cikin sauri, a ce gaggawa
Sheqa gudu ke nan zubewa rusa

Kwara kwari kwararo kwaroron kura
Kore kare kurbatsi karyar karsa

Rago rago rogo ragowa raga
Rugugi rugurguza rungumar gargasa

Ban ce ba na dara wane ko kuma na fi
Sai dai nakan ciza na zo na yi busa

Allah nake Roko Gwani mai kome
Inganta bunkasar da harshen Hausa

Domin Muhammadu shugaban duka bayi
Allah ka fifitar da harshen Hausa

Albarkacin alayansa har sahabainai
Mata da yayayensa kome nisa

Zan dakata daga yanzu sai wata rana
Aikin da nai Allah hada shi da amsa

Domin Rasulullahi jigon bayi
Mai martaba in ya fada a amsa

Tsira ta karu gare shi ko wace rana
Kuma ba tuqewa ba iya adadinsa

Hada Kan Mu Africa Mu So Juna

Hada Kan Mu Africa Mu So Juna
By Abubakar Ladan

Yarda da abota soyayya
An shudu da juna ta sanayya
Gorin asali ko jayayya
Ba gaba an daina qiyayya
Ra’ayi ya zo daya an shirya

Turawan mulki sun tashi
Mun kakkabe hannu ba bashi
Sune Africa muke kishi
Hada kai ne yau mai kaushe shi
An samu hadadden harsashi

Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna

Saura a Mozambique da Angola
Da Guinea sun saura cikin wahala
Hada kai ne babban bulala
Wallahi da zaran mun tsala
Duka sauran za ka ga sun lula

Saura kuma me ya rage mallam
Hada kai a Africa wajen ni kam
Sai an so juna an yi na’am
Sai an hada kai ya tsaya mallam

Kan qauna ya tsayu ba kishi
Daga baya abota zai bi shi
Daga zaran ga abu ya tashi
An shawarta bisa karshe shi
Koko a tsaya kan samo shi
Hada kai ne babban harsashi

Hada kai ke nan ya wakkana
Domin ko abota ya zauna
Daga nan yanci zai amfana
A ji dadi sannan ai murna

Hada kai ba tarore ba kawai
Ba cacar baki ne ba kadai
Ko waye yai ta fadan son rai
Kan an watse taron dada sai
Ya mace kurmus domin ba rai

Hada kai ba wai hada baki ba
Ai zambo ko ai cuta ba
Da wulaqantar da mutane ba
Ko zalunci da fashin kai ba
Yanci bai yarda da wannan ba

Dukkan fitina daga jahilci
Take tushe kau nata lalaci
Shi ke jawo a yi zalunci
Da matsawa gun karbar hanci
Duka ba wannan a cikin yanci

Kyamar juna da yawan gori
A Afirca akwai su tsibi tari
Da kwafar zuci da yawan fahari
Da muke gasanmu da inkari
A ciki hada kai su ne sharri

Allah Shi ne ya ni’im’imta
Afirca kasarmu dukkaninta
Muka wofantar muka lalata
Da jibin goshi muka ya’yanta
Ya za mu yi yanzu mu more ta

Sai kam ba masu munafunci
Da wadanda suke nukurar yanci
Ra’ayinmu ya zo ba bambanci
Mu fahimta mu face wajen faci
Don more Afirca kasar yanci

Kwadayi ke ta da wulakanci
Shi ke cin karfin adalci
Da siyasannan na faqiranci
Ka shake cikinka da zalunci
Me za ka fada a cikin yanci

Mai wannan hali yau shi ne
Hadari a Afirca da mun gane
Komai ya fada mana karya ne
Don mun san logar zambo ne
Mai yin wannan la’ananne ne

Ba masu siyasar maula ba
Makiya yanci dillalai ba
Da idan ba su tuba da wannan ba
Hada kai ba zai wani karko ba
Yanci kuma bai dada komai ba.

Mulkin kai ba son kai ne ba
Ba miqe qafa a ci dadi ba
Ba alqawarorin qarya ba
Inda masu irin wannan a gaba
Yanci bai tsinana komai ba

Sai an manta da su zalunci
An zauna an kashe jahilci
An tumbuke tushen lalaci
Roqo da bara da tumasanci
Na rashin aiki da yawan barci
To sai ka ga an more yanci

Wallahi idan ba son juna
Hada kai da wuya ka ga ya zauna
Kullum ka gano sabon fitina
Jayayya ko neman magana
Sai an so juna an daina

Fitina barci take ba ta fita
Allah wadaran mai tado ta
Da wadanda suke dada jawo ta
Haka nan da wadanda ka kawo ta
Allah ka tsare mu da tashinta

Yaqi biyu yau aka lazumta
A Afirca na farko yayanta
Dauloli duk na qasashenta
Sannan hada kai na mutanenta
Kan an san wannan an huta

Yau ga wasu nan suke nukura
Don mun san yanci mun nasara
Wasu ma a cikin nasu sun fara
Hada gulma tsakani don a kara
Ko oho gama kuwa sun dara

Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna

Zaman mu da ku dai ya qare
Daimon da kuzanmu da zinare
Komai mun kwace mun tare
Ba sa son wai su ga mun more
Yau sun dage su ga mun dare

Kan ka ji fada yau ya tashi
Wasu baqi ne ke kawo shi
Don sun ga haqiqan sun tashi
Hada kanmu suke dada kishinshi
Komai kuwa sa yi su bashe shi

Da wadansu suke hada ma gwiwa
A Afirca akwai wasu yan yunwa
Da suke karbar kurdi da yawa
Rikici duka su ke jawowa
Ku mu tashi hana su da gaugawa

Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna

Da mun hada kanmu Afirca duka
Ba ka jin kyas wani ya yi haka
Sai mun so juna ba shakka
Sannan mu fice wannan halaka
Da rashin hada kanmu ya zo da haka

Afirca mutum ne yantacce
Hamshaki kuma ingantacce
Maikarfi ga shi amintacce
Da basira ilmi tatacce
Da fari da baki miji ko na mace

Harkar bawa ya zam kurra
Daga loton nan ne zai fara
Amfanin kansa yana shukura
Ya bido hakkinsa ya tattara
Ko jikoki nasa sa mora

Ya zamanto da ne mai himma
Bisa sabgar kyautata al’uma
Kan an haka ba sauran hamma
Talakawa ba wani mai rama
Ba sake zama a cikin tsumma

Duka da an so shi ya inganta
Kasa ta tarar da wadansunta
Za su yi sha’awa su ziyarce ta
Da kafarsu su zo su yi kallon ta
Komai ba mai iya kushe ta

Kan ko ka bar talakawanka
A cikin yunwa da zaman bukka
Ko yawon maula ko sadaka
Ka sani har yanzu suna sarka
Kowa ya gani zai zage ka

Lallai ne zurfafa hannunka
A cikin ramin aljihunka
Ka fitar da kudi kuma mai tsoka
Manqudai don aikin talaka
Kan kai wannan ba mai kin ka

Da fadawa zabura kai aiki
Nan ne aka san mutumin kirki
Ma’abucin adalcin mulki
Kuma ba mai ce maka cin kaski
Mai zalunci ya shiga daki

Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna

A kasa duka mai mulkin kanta
An so a tarar da mutanenta
Qosassu babu tsiraraita
Da rashin aiki da galabaita
Ko yawon banza ko sata

A kasa duka kam ba tarbiyya
Ba ci gaba sai ta tsaya baya
Sai girman kai kaya-kaya
Da kwafa da rashin tuna can baya
dan qauye ya shiga alkarya

Ga riga na dibar hakki
Ga kantar dauda ba wanki
Sai ya hango mai alkaki
Ya kira ya saya ya ci yai tanki
Gagon sai ya ji yana hakki

Ni Garba ina tausan kanmu
Ba ma fatawan neman samu
Sai zare ido a wajen damu
Muyi yaqi mu yi ta bidar ilmu
Shi ne manufar mulkin kanmu

Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna

Ilimi babban abu ne gun mu
Shi zai kakkange mutucinmu
A qasa shine akasin zulmu
Da yake bude kofar samu
Da wuya ka ji ga wasu sun fi mu

Ga mulkin kai an kakkarba
A Afirca kadan muka dan saba
Kowa da abin da ya zazzaba
Na wadansu abin har ya zoba
Da ya ja masu jar wahala da shuwa

Liberia ko ni na ganta
Su ne farko suka yayanta
Da ta dau nauyin rike yayanta
Ta san wahalar da ta fuskanta
Allah ya taya ta rikon kanta

Ethopia tun tuni sarki ne
Sarkin nan ko shahararre ne
Sha’anin mulki gogagge ne
Mai yin fara’a da mutane ne
A Afirca SelassieAboki ne

Mulkin da ya karba Sekou Toure
Da turawa sun tattare
Yanzun ba saura sun tsere
Sai daidai wanda ya tsattsare
Allah ya taya su zaman tare

Gold Coast ta samu sai murna
A qasar da ake cewa Ghana
Ku rike mulkinku ku amfana
Da aminci himma da lumana
Kan an haka yanci ya zauna

Sierra Leon sarqa sun yaye
A cikin himmar mister Magaye
Dukkan jama’a kuma ya yaye
Turawan mulki sun janye
Kuma ba fitina ba tawaye

Senegal qasa mai albarka
Su ma duka sun kwance sarka
Da Jalof da Walof yau sun farka
Daga barci yanzun ba shakka
Duka kowa na barka-barka

Cewar Mishar Mukhtar Dada
Mauritania yanzun ba abda
Yantattu ne ni na shaida
Sun dau mulkin kai ba zubda
Jini a qasarsu abin guda

Algeria yau da jibin goshi
Sun san rinjaye da faranshi
Turawan mulki sun tashi
Wuta duka ta mutu sai gaushi
Ben Bellah mu taru mu gaishe shi

Mu gusa mu ga Marshall Burjiba
Mai himma bai iya wargi ba
Ya san yanci tun ba yau ba
Tunis yaya ne sun ci gaba
Ga aiki daman sun saba

Mu gusa mu ga daular Libia
Horarru ne na Italiya
Sarki mai kyakkyawar niyya
Komai aka ce mashi za shi iya
Domin kuwa ba shi abin kunya

Mu yi biza mu ziyarci Masar
Ta Ra’isu Jamal Abdul Nasir
Ya dau mulkin kai babu na tir
Komai aka ce mar za shi idar
Da wuya ka ji an ce ya wahalar

Mu shige jirgi mu ga Sudani
Sun dau mulki fanni-fanni
Ibrahim mai aiki da sani
Mun sami abokai Ikhwani
Da aminci tun tsohon karni

Ta Sahara za mu bi sai Chadi
Sun dau yancinsu gwanin dadi
Ba garmi abokai na nishadi
Tamal ba ya nan bisa kan sirdi
Mutumin kirki bayya fadi

Mu biya ta Kano mu shige Niger
Sun dau mulkin kai ba wani ja
In ja don sun kawo hujja
Don Dori mutum ne mai daraja
Hamani aboki afuwaja

Daga nan mu ziyarci Upper Volta
Su ma can duk sun yayanta
Mursawa yau sun sabunta
Moris mai son sada zumunta
Ya mai gwado ba shi galabaita

A Wugadigu jirgi za mu shiga
Mu wuce fadar Abidjan ma ga
Ga Huhunye Banye yana yanga
Don ko bai yada abin tsarga
A qasarsa da ba wasu yan targa

Ku mu hau mota mu wuce Mali
Sun dau ‘yanci babu jidali
Yanzun sun tashi bidar jali
Ca a Modibbo Keita yana a Mali
Wani kyakkyawa mai kyan hali

Mu haye jirgin sama sai Cameroon
Su ma yaya ne a hararu
Mani’imta ne a cikin hanu
Kuma ga ihisani ba sharru

Daga nan jirginmu ya dirkako
Sai Center-Afirca mu sassabko
Mu ga mulkin nanna David Dako
A qasarsu da kansu suke iko
Ba ka jin wani da wani yai soko

Daga nan ne zan bi tsawon kogi
Mu yi ban kwana da mutan Bangi
Sai Brazzaville mu gano dangi
Sun takura sun balle kangi
Don Youlu ba shi abin zargi

Ku mu ketare kogi sai Belji
Na duba kasa sai jeji
Sun dau yanci kowa ya ji
Tuni Kongo suke yin karaji
Ba sa kaunar mulkin Belji

Aure Da Kudi

Aure Da Kudi
By Babangida Kakadawa

Yau na yi tagumi na rame ban iya cin komai
Allah koro, Allah koro da masoyiyata
Rashin ganinta na rame bana iya cin komai
Yau ga dan talakawa yana son yar mai kuddi
In na biya sadaki ni ba za ni yi lehe ba
Da na biya sadaki ni ba za ni yi lehe ba
Idan taje gidana ba zan bar ta a tsumma ba
Dada amman wata qil lallai babanta za zai so ba mamarta ba ta so ba
Matan garinga sun yi yawa kuma sun cika tunbulbul
Kuma ba su son aure sai sun bidi kuddi
Idan baka da kuddi bana ba zaka yi mata ba
Idan kana da kuddi, in sun ganka da mota har hotuna suke kaima
Darje bidi mai kwari
Tsoho da kudi yaro
Yaro in ba kuddi yau ya koma tsoho

Ana wata magana jama’a ga wata magana ta zo
Wani mai jaki ya ingiji mai goyo, babbar magana annan
Ji ana wata magana jama’a ga wata magana ta zo
Wani mai jaki ya ingiji mai goyo, babbar magana annan
Ji samari na son mata kuma sannan ba kuddi
Gayu na son mata bana gayu ba kuddi
Sai zama a kan hanya da takama da sa T-shirt
Sai zama a kan hanya da takama da sa 2-pac
In sunka ga mata wadansu na fadin chika, wasu na fadin chizga
Muna nan muna aikin ba zamu tsayawa ba
In ka ga tsayawata sai in mutuwa ta zo
Babangida Kakadawa mai kida kanen Sani
Na Dan Maraya wakar wa kayi sai mu
Dukan zare yana tsinkewa banda irin nau wa
Don nau zaren da yar murde ya zama karfen jirgi
Qirarsa sai maqeran asaili su yi ke horo nai, ga mu
Don da dan haye da dan gado ba zasu zame dai ba
Yaro bai son yaro ne ba
Yaro bai son yaro ne ba sai ya rasa baba nai ko ya rasa mama tai zai san yaro ne shi
Ku ji dai yana ganin duniyar nan tai masa talala har da fadin wai sune zasu yi ba mu ba
In banda rashin kunya, mai bidar nama mi kai shi zuwa gulbi wai har da yuqaqe nai
Mai bidar kifi mi ya kai shi zuwa kwata, mi ya kai shi zuwa zango kuma harda zugun taru
Tsohuwar kura mai bidar kashin bango, wancan na kan gina, in ta ga mai tsoka ba zata raga mai ba
Thohuwar kura sai dai ki ci kan ki, ni ba za ki ci na ba, yalum
Alhaji Babangida Kakadawa mai kida kanen Sani
Na Dan Maraya wakar wa kayi sai mu

Yau na yi tagumi na rame ban iya cin komai
Ga dan talakawa yana son yar mai kuddi
Da na biya sadaki ni ba za ni yi lehe ba
Idan taje gidana ba zan bar ta a tsumma ba

Da Ganinki

Da Ganinki
Umar M Shareef

Ehh da ganinki sai nakamo
Gashi kin zamo jinin jikina
Lokaci guda nakamo ooooh oohhh ooh

Aha aha aahaa
Aha aha aahaa aaaaah

Eh kallo daya bisa kallo ida nayi miki
Zuciyata sai ta kamo yan mata
Shi bari da ba’a yi mar ga damina
Zo a gareki sannu sannu yar gata
Banzo da matstsala ba
Ban zarce ka’ida ba
Ki yi min iso na zo gunki tunda kin ga ba koshi ba abin guduba

Na amsa sallamarka taho ga mazaun
Ka farta zantu kanka
Al’umma rahama ce
Har da kai ciki haka yaka ban gudunka
Manufarka bansaniba
Ban gani cikin ido ba
Ni dai fata nake komai zan ji ya zamo al khairi ina maraba

Baki gane me nake nufi ba
Soyayya ce nazo da ita
Da ita da ita
Kallo daya da nayi miki na na san macen da nakeso nayi gamo da ita
Da ita da ita
In jira bazan iyaba
Zantukan da na yi ki duba
Soyayya ce nake so ki bani inna samo zargi ba zan saki ba

Aha aha aahaa
Aha aha aahaa aaaaah

Uhm na yarda na yarda na amince
Yarda da kai taho mu kulla
Tsarinka lafazinka su suka sace
Zuciya tayi jimilla
Ba zan gujeka yiba
Nai caraf sonka na karba
Ni da kai kawai mu tsaro soyayya sabuwa
Karshenta na da riba

Nagode, nagode nayi murna mai zan biya tukuici
Ba komai ba komai tunda ka yaba
So ne shine tukuici
Lallai na zo da sa’a sai hamdala
Kin yi min karamci
Soyayya ce ta sanya
Komai ba zan gaza ba

Babbar Yarinya

Babbar Yarinya
By Adam A Zango

Ehhh babbar yarinya nai sa’a
Na zamo auta cikin maza

Eehhh haduwarmu da kai shine sa’a
Baya nai dace a yan mata

Aaaaah aaaaaah

Hankali ke sa ayo girma
Rasuwa mataki cikin girma
A gurinki dukkansu kin sama
Ko a cikin sunanki akwai girma
Babbar yarinya lakabinki
Ke na raba dan nayo girma

Duhu bai dusashe haske
Dukkam mai ido shi zaya fada
Idan akwai ka ba’a batuna
Ganinmu da kai ke karan girma
Manyan yara da sun gan ka
Su zo da sauri kai su karrama

So da kauna shi nake nema
In dai a gu nane tuni ka sama
Lallai gareki ina da alfarma
Ko wanne ka kawo ka sani zanyima
So ya kai so tsakaninmu
Ba na gajiya gunyi miki hidima
Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Baya nai dace a yan mata

Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Baya nai dace a yan mata
Eh nazari nayo a kanki
Da tabbacin banyin nadama
Kin yi min shimfida ta fuska
Zahiri ta zarce tabarma
Nai rawa a gabanki nataka
Zo kimin naki salon kema
Allah nunan masoyanmu
Ka tsaremu sharri na yan gulma
Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Baya nai dace a yan mata

Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Kayo nisa cikin raina
Ba’a hangenka barema a cimma
Gangancine ace za’a iske ka
Ko dan gajiyar tafiya a suma
Tunda na tsinke zaren birki
Yan samari sai kuyi ta himma

Eeehh babbar yarinya
Nai sa’a na zamo auta cikin maza

Ehh haduwarmu dakai shi nai sa’a

Auren Mu Ba Makawa

Aurenmu Ba Makawa
By Umar M Shareef

Ehhh ba zana barki ba
Auren mu ba makawa
Sai dai in rasa raina ni sai da ke zanyi zaman aure

Ba zana barka ba
Auren mu ba makawa
Sai dai in rasa raina ni sai da kai zanyi zaman aure

Uhmmmm sabo da juna
Ni da ke mun yi ba misali
Ace mun farake zai sakamu cikin wani hali

Wancin da zanyi yau yanayin sa bai da misali
Auren mu babu makawa in akwaishi sai dai in bani ba raina.

Ba zana barka ba
Auren mu ba makawa
Sai dai in rasa raina ni sai da ke zanyi zaman aure

Ni dakai mun faro gini kyakykyawa munyi nisa
Musa azuciya ke kawar ni na shiga cikinsa
Iyaye garemu sun yaushe za su rusa
Bazana so hakan ba aurena da ni dakai ba makawa.

Ba zana barki ba auren mu ba makawa
Sai dai inrasa raina insa da ki zanyi zaman aure

Ina zubar hawaye a idanu karsu kare
Na kasa yanda zanyi daina ko ko in jure.
Wutar da ke ta ruri acikin rai wa za ya hure
Sai dai a bani ke kin zamo ruwan kashe gobaran araina

Ba zana barka ba auren mu ba makawa
Sai dai in rasa raina insa dakai zanyi zaman aure

Ka zam rabin jikina sai da kai komai zanyi daidai
Zuci ta yo sukuni rayuwa ta zauna a daidai
Ace ba da kai ba dangara asara na bi yayi daidai
Kun ga babu rayuwa kenan agareni ni dai waiyo

Share hawaye masoyita ki daina kuka
Mu kara hakkuri ni da ke mu daina shakka
Karshe na taho watarana za ayi mana barka
Aurenmu babu makawa
Ni da ke zamu zamo ango da amarya

Ba zana barka ba
Auren mu ba makawa
Sai dai in rasa raina ni sai da kai zanyi zaman aure

Ba zana barki ba
Auren mu ba makawa
Sai dai in rasa raina ni sai da ke zanyi zaman aure

Burina

Burina
By Umar M Shareef

La lah lah lah lah
Buri na!
Buri na!

Buri na muyi aure da kai
Har abada muyi zama da kai

Zo ki kama hannu na ki rike masoyiyata
Ma’ana rikon amana soyayya ki adanata
In kin boye ta
In kin sirrinta
Na sani kin mini gata
Ki min rikon da nai miki
Da zuciya daya ya yar uwata
Kece burina
Hasken rayina
Dangina duk sun san dake
Wa zai banbanta?
Tsarin siffata
Nai kama da ni da ke
Da ni da ke

Duk wacce ta kalle ka
Da tabbacin sai ta kara
Dan kyawon idanunka
A kaina haka ya fara
Da zana bada sunanka
Sai dai ince da kai Nura
Kai wata ni ko Zahra
Nai karo da kaifin yaro
Haka rabbana ya tsara
Babu rabuwa yay ye
Babu rabuwa
Babu rabuwa
Da ni da kai
Haaaa
Da ni da kai

Fuskata sai labarin soyayyarki take nunawa
Duk jikina son ki ina ta nishadi ina darawa
Soyayya ta mantar dani labarin kunci bana tunawa
Wanda ya dace da soyayya diya da tarbiyya
Kai godewa
Allah ne mai shiryawa
Rashi da samawa bana mantawa
Tunda ya bani na samu na gode Allah

Dominka nai tattali na so
Kai nake yi wa adani
In mun yi aure da ni da kai
Na san zaka kula da ni
Komai kace in yi ma zanyi shi da hanzari ba guna-guni
Ka dinga yin alfahari da ni
Gare ni ka samu lamuni
Cutar dake son kwantar da ni
A yanzu na samu magani

Wasika

Wasika
By Umar M Shareef

Uhmmm hmmm haaaa hahahaha
Uhmmm haaaaa haaaa hahahaha

Wasika yau zan ambata ta
Sako ne ga masoyiyata.

Kin dade acikin zuciyata
Na rasa yanda zan yi har ki fahimta

Tun farko haduwar mu dake
Soyayya nak kamu dake
Nauyin baki shi ya hana ni in zo

Tunani kullum babu sake
Hawaye nayi ido ya jike
Kowani sayin sai kinyi mini gizo

Ya zam cuta gareni kin gani
Kece kadai kawai magani
Tallafa ki yo lamuni
Ki bani sonki in shigo gari

Ban jin dadin labari
In bana kiba ba tsari.
Aiko cikin taurari kinyi daban
Kin yi daban

Yardar nike yin buri.
Ki aminta dani ba sharri
Na zo da daban alkhairi sonki ki ban

Ni ina ta sanbatu har ance na zautu
Bana iya karatu

Kece
Kece
Kece
Kece
Kece kadai maganina

Hmhmm
Kyakykyawa mai kawata kallo kece.
Kece

In kira ki da dawisu ado haka ya dace
Ya dace
A dabiu ko da gani ke mai nutsuwace
Mai nutsuwa ce
In kin shiga taro ke tamkar fitalace

Tauraruwa ta bullo
Da kin fito sai kallo
Ko zaa yi mini gwalo
Ko an kira ni da dolo
Ni ke kadai nai kallo
Ko an buge ni da kwallo
Ban kauda kai ko zallo
Dan kyan ganinki da kallo

Ahahaha Ha hahahaa ha haha
x 3

Kece
Kece
Kece
Kece
Kece kadai magani na