Bulaliya

Bulaliya
By Sani Yusuf Ayagi

Randa duk kwana ya qare
Ko a daki ko a zaure
Ka rufe kofa da kyaure
Za ta zo ran za a zare ba da kai mata ja inja ba

Ba a jinkirta ma kowa
Ba a gaggauta ma kowa
Ajami ko larabawa
In ta zo ko sai macewa ko sakan ba a dadawa

Kun ji dai ku yan uwana
Manya manya da kankana
Za ta zo musu ko a gona
Ko a daki ne na kwana in ta zo baza su kwan ba

Malamai ko jahilawa
Ma su kurdi talakawa
Masu mulki duk gamawa
Za ta zo musu ba rabewa ba ganin matsayi take ba

Dubi ayar qur’ani
Kullu nafsin tai bayani
Za’iqatul mautu aini
Ko a kauye ko a birni babu wanda ba zai mace ba

Duk mutum da sanadinshi
Wani yai cuta ta jashi
Wani ba ciwo ta kaishi
Wani ko hadari silarshi babu yadda ba zata zo ba

Wani na yawo a titi
Wani na ciniki a kanti
Wani ko na shafa fenti
Wani ko ya kama kati bai sani yau zai mace ba

Wani na fama da aiki
Wani na sukuwa da doki
Wani na wanka a tafki
Wani ko ya kama wanki zata zo bai karasa ba

Wani ko na cin abinci
Wani ko sai yayi barci
Wani na fama da kunci
Wani ko a cikin takaici zai mace bai ma sani ba

Wata na tukin tuwanta
Wata tazo haihuwarta
Wata ko na kan gadonta
Zata zo dan zare ranta bada ta farka anan ba

Mutuwa ita ba ruwanta
Inta zo ba mai hanata
Babu mai ikon tareta
Masu mulki ko wadata dai cikinsu bazai hana ba

Ba ruwan mutuwa da mulki
Ba ruwan mutuwa da mulki
Ko na mai rawanin ga sarki
In ta zo tilas ta dauki ransu mulkin bai hana ba

Dubi jariri kamar shi
Sai yana hannun uwarshi
Ta riga ta rungume shi
Sai ta rabo tsaf ta jashi ga uwar bata ko hana ba

Ko ta dauki uwar ta bar shi
Ba ruwanta da tausayin shi
Bata duban wai uwar shi
Zata dau nono ta bashi in ta zo ba za ya sha ba

Mutuwa bata kulawa
Saurayi ko ya budurwa
Yanzu ta maishe su gawa
Babu sauran shaqatawa bako zata jira biki ba

Mutuwa ba raya shaho
Ta buge yaro da tsoho
Ta kade kuturu makaho
Wani ma tun kan a haihu zai mace ko ba da wai ba

Mutuwa har in ta sauka
A gida wani zata dauka
Ba ruwanta da masu son ka
Yanzu kaji ana ta kuka wanda bai hana dauke ran ba

Yanzu aya zan karanta
Yan uwa kowa ya jita
Ko wani zaiga ma’anarta
Yadda kowa zai kowa fahimta ba tare da na barta a dunkule ba

Aina ma kuntum ku gane
Yadrukumul mautu kune
Ai walau kuntum mutane
Fi burujun can daban ne yan uwa ban qarasa ba

Ma’ana Allahu yace
Ko ina ne kun kasance
Zata zo muku karku mance
Mutuwa Allah sa mu dace kan ta zo mana duk mu tuba

Kun ji dai zance na aya
Gaskiya ce babu qarya
Ko ina ne kun ka buya
Zata zo muku sai ku shirya ba shirin shan magani ba

Ga misali mai kulawa
Mursalai haka annabawa
Ga sahabu da auliyawa
Sun wafati da dadewa mu suwa ba za muje ba

In kana ji ne da kanka
Da isa ko dukiyarka
Ko yawan mulki gare ka
Can a baya akwai gabanka ya wuce bai dakata ba

In yawan bauta gare ka
Rabbi yai wani kan ayi ka
Wanda in bautar yafi ka
Daukakar ya sha gabanka ya wuce bai ko tsaya ba

Kunji tarihi da qissa
Annabin allah da kansa
Wanda babu mutum kamarsa
Musdafa an zare ransa ya waninsa ba zai mace ba

Wanda zabi anka bashi
Shin a dau ran ko a bar shi
Daha dan jarumtakarshi
Sai ya zabi a zare ranshi bai bukaci ya dakata ba

Dan uwa bar shirya fati
Kyale cin naman faranti
Tunda Annabi yai wafati
Babu mai ikon sabati duniyan nan bai mace ba

Da uwa da uba gare ni
Sai uban ya mace ya bar ni
Tun ina karami ku gan ni
Sai uwata ta riqeni har na girma ba zan rufe ba

Sai na girma gaban uwata
Sai ta kyautata rayuwata
Har ta min aure da kanta
Gashi yau ni na rasata ban ko samu kamarta dai ba

Duniyar nan ba kamarta
Shi yasa in na tuno ta
Yadda tai mini tarbiyarta
Sai nace Allah jikanta . . .

Gashi yau na samu kaina
Ba uwata ba ubana
Sun bace wa ganin idona
To ashe wataran kwa raina zai bace ba ko da wai ba

Yan uwa in kun fahimta
Duniyar da muke cikinta
Dole kowa zaya bar ta
Babu mai ikon suturta wai yace ba za ya kau ba

Dan uwa bari yin dagawa
Dan ganin ka samu baiwa
Bar ganin ka zarce kowa
Mutuwa na keyawayawa babu inda bazata je ba

Randa duk aka zare ranka
Yan uwanka suna ta kuka
Wanda bai dawo da ranka
Ai su ce allah jikanka zai ji ba sui ta kururwa ba

Burinsu kawai a kaika
A saka ka a kabarinka
Sai su zo kan dukiyarka
Sui rabo ba mai tuno ka sai kace basu sanka da ba

Da kana mulkin gidanka
Yanzu bamai girmama ka
Babu sauran bada doka
Babu mata yaya da jika sai kace basu san ka dai ba

Alhajin allah kamarka
Mai isa da isa ya sanka
Gashi yau likkafaninka
Ba a sa shadda a dinka sai farin alawayyo duba

Kaga tarin dukiyarka
Bata amfani gare ka
Duk yawan motar gidanka
Ba a kai ka a marsidinka sai kace ba taka ce ba

Dan uwa kar dai ka mance
Duk kudin nan naka nace
An yima gata fitacce
Sai a dau motar itace a saka ba marsidin ba

Matuqar sun girmamaka
Sug gine kabarin ga naka
Daga nan sun sallameka
Ko ziyara in gayama sai su shekara ba su je ba

Dubi duk girman gidanka
Sai ya zam kan gorashinka
Wanda ba ya shiga da ranka
Sai ya aure sahibarka ya shige ba’a mai hani ba

Dan uwa in an saka ka
A cikin kabaringa naka
Ko ina an toshe iska
Babu mai sha’awar taya ka shi zaman nan ba da wai ba

Sai a tashi kawai a barka
Daga kai sai dai halinka
Sai Nankir Munkir su sauka
Sush shigo don tambayarka duk da ko baka san guda ba

Sai a dawo ma da ranka
Sai su hau bisa tambayar ka
In ka amsa sai su barka
Sai a yalawata kabarinka ba a barshi a takure ba

In ko har suka tambaye ka
Babu amsa zaka koka
Sai su hauka kawai da duka
Sai a matse tsababarinka har gabobi duk su saba

Sai a nuna ma makoma
Hawuya koko jahima
Inda nan za kai ta fama
Har zuwa tashin qiyama babu sassaucin azaba

Dan uwa zan sake jan ka
Kar ka ce na tsorata ka
Zan yi ma zancen gidanka
Inda farko za a kaika sanda ka mutu ba da wai ba

Kwanciyar kabari tuno ta
Ba katifa zaka yi ta
Ba filo haka zaka kwanta
Babu juyi dan ka huta kaji ba qarya nake ba

Babu haske babu iska
Babu A.C. babu fanka
Kai ka dai ba sahibarka
Sai abinda kawai ka aika zai fito maka ba da wai ba

Kwanciyar nan ko a barka
Babu zagi babu duka
Kaita bacci dai abinka
Wata ran ka so ka fark bada an maka izini ba

To bare kuma babu tashi
Ga gumi zafi ka san shi
Ba rigingina sam cikinshi
Ya ka shirya zaka yi shi baka sa Allah gaba ba

Ka ji dai yanayin cikin shi
Gashi ya zama babu fashi
Dole kowa zai shige shi
Ya kamata ka tanaje shi da yawan zikiri da tuba

In gaya muku yan uwana
Kun sakankance ganina
Sai yawan sabo da barna
Kun sani da wuta da jannah ya ba mu yi musu tanadi ba

Shugaba kake ko ko gwamna
Ofishin nan naka auna
Wanda kai ka shige ka zauna
Sai ka dau biro ka zana kai zaton fa ba’a sani ba

In tuna maka kar ka manta
Kar ka yarda ka shirya cuta
Ko kadan ce kar ka yi ta
In ko kai to an rubuta ba ko gogewa ake ba

Kar ka ce ba’a ganinka
Tunda ba’a shiga wajenka
Sai da yin izini a gan ka
To ji Allah na ganin ka ga Rakib da Atid ka lura

Duk abinda ka ke ka gane
Shin na kirki ko tsiya ne
Su suna hangen ka zaune
Sun rubuta ko kadan ne basu kyale ko guda ba

Dan uwa komai ka shuka
Zai fito kaji babu shakka
Zaka girba kai da kanka
Randa ka mutu kai da kanka zaka zana ba da wai ba

Sai ka ce can na yi sata
Can ko na bai wane kyauta
Can ko naci haqqin maqota
Kayi alheri da cuta baka biye ko guda ba

In ka dubi mu’amalarmu
Mun sakankance ganinmi..
Shin ku dubi mu’amalarmu
Mun sake sam ba ruwanmu
Bamu tanyon yan uwanmu
Dukiya daga mu diyanmu ba mu ba kowa kwabo ba

Kasuwarmu idan ka duba
Bamu ware haram halar ba
Bamu san zi da ribaa ba
Bamu bar yin algushu ba sai kace ba zamu kau ba

Yan uwa tuni ni na lura
Mun sakankance da naira
Burikanmu kawai mu tara
Ba tunanin zamu saura bamu dau mutuwa a kwam ba

Ga shigarta kwarai ganina
Gashi mun cika cin amana
Ga yawan sabo da barna
Sabuka manya kanana yi muke qarya da giba

Ni abinda ka bani haushi
Dan adam sam ba ruwanshi
Bai kula da abin gaban shi
Ko hisabin dukiyarshi dan uwana bai kula ba

Wanga waqe yan uwana
Nayi dan wa’azi akaina
Dan na lura na gyara kaina
In rage sab’o da kaina in tuno mutuwa na tuba

Dan ganin ni na shagalta
Mutuwa bana tuno ta
Ban tunanin ya kamarta
Nafi kyautata duniyata lahira ban ko kula ba

Shi ya sani na wallafa ta
Dan tunawa zuciyata
Shi ya sani na wallafa ta
Dan tunawa zuciyata
Da akwai mutuwa gabanta
Ko da yaushe za ta zo ta ba kwa sa rana take ba

Nafi so naga na wadata
Na sayo babur da mota
Marsidis honda tiyota
Ga gidana har da kwalta can a gefe ba gari ba

In yi dinkin kece raini
Riguna ko wanne launi
Shadda boyal na aini
Nayi dan nima a sanni mai kudi ne ba kadan ba

Nan da nan kaga nai abokai
Masu kurdi har sarakai
Masu mulki malamai sai
Sui ta danqa min muqamai duk da ban iya godiya ba

Sai a ce an ban sarauta
Shugaban duka masu kyauta
Ai ta famar gayyata ta
Gun a fil fan nai ta kyauta ba ‘yar kadan ba

Malamai ko su zo gidana
Sui ta nema na mu gana
Sai a ce musu na yi kwana
Sai su sami guri su zauna basu san ko zan fito ba

Sai su qirqiri yin karatu
Ko su kawo min rubutu
Wai na sha dan kar na zautu
Dukiya haka sai da hutu kai magauta suc ci riba

Gun biki sai an jira ni
Duk ana burin a ganni
In na zo fa a kewaye ni
Ga maroka na zugani in yi kyauta ba kadan ba

To a sannan na gama ni
Dole kowa zaya bi ni
Yaita famar girmama ni
Sai ace komai sai an jira ni ko abin ni ban sani ba

Dukiya ta ja sarauta
Na zamo malam akan ta
Ba a qaryata magana ta
Sai a so ni maza da mata duk da ko ban san alif ba

Ba a qaryata magana ta
Ko a yaya ni nayi ta
Ko nace na shuka fata
Ta fito kuma naga dan ta wani zai ce ba da wai ba

To ana haka sai na gane
Duniya wani gun zama ne
Burinka da nake haram ne
Mai nutsar da mutum a zaune wanda bai dace da ni ba

Mutuwa ni ba ni san ta
Ba ni san na ji ambatonta
Dan tana kada zuciya ta
Take sai kaga na dimauta kwarjinin fa ba zai gushe ba

Na sani ita gaskiya ce
Naji lallai na amince
Zata zo ba kauce-kauce
To fa Allah na dimauce dan kwa ban mata tanadi ba

Mai ya sani nake gudun ta
Yadda malam ya fade ta
Gashi yadda ya suffata ta
Naga babu gwani a gunta yaya ba zan fargaba ba

Ba macewar nag guda ba
Mutuwa ni ba da wai ba
Ba ina kyamar ta ne ba
Karta dau raina ku duba kwanciyar kabari na duba

Na yi sabo ba kadan ba
Ga shi ba sadaka nake ba
Ni ko ban wata nafila ba
Ban yi aiki ma su kyau ba ya ba zan mata fargaba ba

Ni mutum ne mai kasala
Mai buqatar tara daula
Gani ba na son wahala
Banda sallolin farilla gashi ban wani tanadi ba

Inka duba ayyukana
Wanda dai ni nai da kaina
Manya manyan laifukana
Nai nadama ni da kaina Rabbi ba zan sake yi ba

In na dubi abinda nay yi
Laifuka ne masu nauyi
Sai jikina yay yi sanyi
Sai kawai roqon buwayi gafara ba sake yi ba

Tunda yanzu idan ka gan ni
Duk gabobi sun yi rauni
Ya gwani Ar-rahamani
Nayi rokona da nuni kaj ji kan Ummi da Abba

Rabbi wanke mahaifiyata
Dagga dukan laifukanta
Jallah nai roqo ka sata
Can gidan rahama ta huta ba da an mata bincike ba

Rabbi kaine Arrahimu
Shafe dukkan laifukanmu
Duk abinda mu kai ka bar mu
A gidan nai’mu ba da ka kula laifukan ba

Rabbi babana ka bar shi
Kar a bincika ayyukanshi
Nay yi roko jalla sashi
Cancikin firdausi sashi rahama bai sha wuya ba

Duk haqqina ya biya ni
Ya gwada mini Qur’ani
Makaranta shi ya kaini
Yayi min horo da nuni bai gwadan san zuciya ba

Ya gwani Allah karimi
Zul-jalal wal’ikirami
Nayi roqo ya rahimi
Kaj jikan dukkan musulmi hada kanmu mu daina gaba

Na ga nan ne ya kamata
Yan uwana in taqaita
In batun mutuwa na huta
Allah sa dai mun fahimta ba mu bar ta mu shantake ba

Wanda duk ya tsaya ya ji ta
Ko ya dauka ya karanta
Inda yagga kure cikinta
Yai yi himma dan ya gyatta sani bai wuce yin kure ba

Ma su neman wa yayi ta
Koko neman baitukanta
Adadunsu su bar daqauta
Zan fada gun kammala ta can a qarshe ba a nan ba