Jarumar Mata

Jarumar Mata
By Hamisu Breaker

Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciya ta ba
Komai ruwa da iska akan ki ba za na daina kewa ba
Idan na samu zarrar samun ki ba zani tanka kowa ba
Ni ban ga mai harara ba
Bare na waiwaya fa

In dai a kan ki ne za na jure wahalar zuwa garin nisa
Da an taba ki a jira ni don kau tilas na dau fansa
Jumirin jiranki nai don ki zo na kalle ki gimbiyar Hausa
Sirri na rayuwa ta kece kawai da kin kira da na amsa
Zuma a baki dadi gare ta kin bani taki na lasa
In dai a kan ki ne na yi nisa don ba kiran da zan amsa
Tilas ganin mu tilas barin mu qaunar ki tunda nai nisa
Sam ba batun na fasa ko za’a ce mani in bada rai fansa

Zarin zubin ki daidai ne
Ya kama zuciya ta ne
Ina jin kamar mafarki ne
Ina san ki so mataki ne

Ni banda damuwa in har zan bude yan idanu na
Kalle ki ga ki dab da ni toh me za ya damu qalbi na
Yau za na yo amo tunda na gane kina da tausai na
Don yanzu na zamo ya mafatauci mai bidar qurin kwana
Na kwallashe ladas sarar da iya maki ya kalamai na
Daga zuciya nake kwatanta ina zaiyano jawabai na
Idan babu ke ina ne zan saka zuciya ta bar yawan quna
Kowa da nasa amma ni kece cikar muradai na
Yau ga ni an ruwa kusa da kada zo ki ceci qarko na
Komai da maffita karda ki saba da furta bankwana
Ina ji ina gani yadda nake son ki ya fi qarfi na
Ina son a duniya da wanda ya ke janye duk tunani na
Soyayya rawuya wani sa’in sai ta zam wutar gona
Duk wanda ke cikin ta shine jurau amma fa a gurina
So na faranta rai da ruhi ya sa ka zam kamar sarki
Kuma rayuwa da so misali zai na kama da a mafarki
Samari muyi hakuri don har mun samu so mu sa sauqi
Yan mata muyi hakuri idan har mun samu so mu sa sauqi
Masoyi yana da rana ne
Masoyi yana da rana ne