Fati Yar Adamawa

Fati Yar Adamawa
By Naziru Gwauro

Fatimaaaaaah

Fatimaaaaaah

Fatiiii

Fatiiii

[Chosus x 2]:
Fatiii
Yar asalin mahaifan la
Fatii
Yar adamawa tudun Yola
Fatii
Yau Salisu yana cigiyar
Fatii
Zo taho garin Kano

Ran da na fara ganinki Fatimah
Ran asabar ne da kin ci kwalliya
Da yammaci sannan ga damina
Ta busa sanyi tamkar da safiya
Yeh ooooh
Tamkar da safia
Wajen biyar da rabi nake nufi
Hotoro tai shiru ba hayaniya
Wayyo Fati ba hayaniya
Ga ni’imar Allah a ko ina
Ciyawa tai kore gabadaya
Sai ga baiwa nan daga Allah
Fati kin danno karo daya

Chorus

Nai mata kallon Shari’ah guda daya
Sai nag a fuskarta kamar tana fushi
Fati kamar kina fushi
Aminina Aminu na gefe na
Shi kuma sai na ga yana ta murmushi
Ko Aminu yana ta murmushi
Koh da ta kallai sai ta yi dariya
Sai naga kun gaisa gaba daya
Sannan ta zarce gidansu tai tsaye
Aminu ya kallen yayi murmushi
Sannan na san lallai Salisu
Tarkona ya kama kurciya

Chorus

Aminu yai man iso ga Fatima
Mun ka fahimci juna da gaskia
Ashe kanwa ce gun matar wan su
Ka ji abun dadi da dariya
Don a gidan su Aminun ni dana
Ta ko ina sam babu wariya

Chorus

Cikin shekara mun yi da Fatimah
Soyayyar mu ta zaga ko ina
Hatta ma Abba ga Fatimah
Ya san muna son juna da gaskia
Yai alkwarar zai je Adamawa
Don ya sanar da Ummi ga Fatimah
Sai ga mutuwa tai gaggawa
Ta dauke Abba ga Fatimah

Chorus

Yau Fati ta koma Adamawa
(Started crying but stopped)
Bani da ikon ganin ta ko daya
Ganinki ko daya
Allah shi zai bani Fatimah
Ba ni da wayo ko guda daya
Sunan kaka ta Fatimah
Fatimah
Sunan babbar yar mu Fatimah
Fatimah
Sunan yar autar mu Fatimah
Fati
Ya Allahu ka ba ni Fatimah

Fatimaaaaah

Fatimaaaah

Fatiiii

Fatiiii

Chorus x 3

Fati
Zo taho garin Kano
Fati
Zo taho garin Kano
Fati
Zo taho garin Kano