Gari Ya Waye

Gari Ya Waye
By Unknown Artist

Gari ya waye dukkan duhu na yaye wa x 4

Bayani na taho in baki kan soyayyata
Cikin natsuwa tsab a waye ba na yin wauta
Mutanen kirki da gaskiya suka shirya ta
Tunani na ai da ni da ke ba sabawa
Uhum ka ji maigida a bar dai tonawa

Kin ce ba kya son zama da kowa na yarda
An ce kishin shi ki ya baci kowa ya shaida
Amma ni lafayar zama da ke shi na yarda
Shi ya sa duk tanke tanke ba na dubawa
Ka ma duba in ka rabu da ni wa za kaiwa

A a don Allah ki daina zance yan yara
Domin ni dai kin san qauna da so shi na aura
Amma yanzu da ni da ke a yau ni na lura
Kina ta wahalshe ni ni kau ban iya ramawa
In ka rama ni da kai fa wa taka kwabewa

Gari ya waye dukkan duhu na yayewa x 2

Gida na duk ga abinci nan ba yankewa
Ruwa an shaida drum drum naka tarawa
Tufafi dukkan wata guda naka dinkawa
In kawo miki don gudun zugar mai batawa
Toh ni wa ma zai zuga ni in zam kamawa

Ni dai ai baki ji ni na fada ba dan huce
Tsiren nan kin san in baki ci ba zai lalace
Kudin in na baki sai ki je fa ki taskance
Abincin ci na sai kin so kika girkawa
Ni na qoshi kuma kudin gida naka aikawa

Kalamai na yau gatse gatse kika amsa mun
Yau na gane nufin ki so kike fa ki saba mun
Toh shikenan duk abun da zan yi ki ce amin
Yau zan mutu lallai ga rabbi zan zam komawa
Kama mutum man in ka tafi miji zan sake wa

Don Allah taso wai maigida baka san wasa
Kamar ni ya za’a ce da kai naka sa’insa
Abun da kai mun da safe rannan shi yassa
Amma komai ya wuce a bar ma hangawa
Haba na gwada ki ne kawai don ramawa

Amma ka sammaci zuciya ta ta zautu
Toh shikenan zo mu je mu zauna mui hutu
Toh ba komai ai a yau fa lallai ya kyautu
In dan ci abinci da dan ruwa don walawa

Gari ya waye dukkan duhu na yayewa