Auren Soyayya

Auren Soyayya
By Aminu Rinji Bagwai

Auren soyayya da dadi yake Allahu ya bani
Alkwarin qauna ki riqe ni amana don Allah yar’uwata

Chrous:

Auren soyayya da dadi yake Allah ya cishshe mu (wayyo Allah)
Ku rungumi junanku
Riqo na amana don Allah yan’uwa

Assalamu alaikum ya masoyi hasken alkhairi (wayyo Allah)
Annurin raina farar inuwa da zaman sirri (wayyo Allah)
A sansanin qauna da masoya da kai nake fahari (wayyo Allah)
Sonka nake nachi masoyi kai ne ka ceto rayuwata

Chorus

Na je ni ziyara gun qawaya wadda ta sha kurumi (wayyo Allah)
Na tarar da angonta a dakin sai suka koro ni (wayyo Allah)
Ga shi garin ya dau hadari ai kau ruwa ya doke ni (wayyo Allah)
Kafin gida na jiqe sharaf yau dole na bayyana damuwata

Chorus

Yau ga shi nima na kasance ni da abun raina (wayyo Allah)
An mani aure na yi bankwana da qawayena (wayyo Allah)
Fata nike Allah ya bar mu a tare da mai so na (wayyo Allah)
Allahu ya baka masoyi ka riqe ni aman dan’uwana

Chorus

A cikin lamari na zama na aure share hawayenki (wayyo Allah)
Abun da kike nema na soyayya yau na baki (wayyo Allah)
Yana deban kewa duk randa na kalli idanunki (wayyo Allah)
Ga ki da kyan sura abun da kike so kin samu yar’uwata

Chorus

Yawan kallonki yana zamewa annashuwan raina (wayyo Allah)
Kece mabodin sirrikan qauna da suke raina (wayyo Allah)
Ina fatan Allah ya hada mu a tare a Aljannah (wayyo Allah)
Tunani ya qare ya tattare sonki da qaunarki yar’uwata

Chorus

Ehh ki tashi ki bani ruwa ki kashe inji ki rage fitila (wayyo Allah)
Mu je mu ga jan barchi duhu na maraice ya tsala (wayyo Allah)
Mu gode wa Allah gwani da ya yo mu cikin daula (wayyo Allah)
Ga shi muna sallah muna azumi mu hade kanmu yar’uwata

Chorus

Abun da kake nema inai maka shi komai wahala (wayyo Allah)
Ba ni da kowa ban da komai sai kai sai Allah (wayyo Allah)
Inai maka albishiri zama na mutunci mun qulla (wayyo Allah)
Na kunno fitila kuma na kashe inji zo mu wuce dan’uwana

Chorus

Ina dimaucewa idan na ga kyawun surarki (wayyo Allah)
Bare in dago kaina in kalli fararen idanunki (wayyo Allah)
In gan ki fara santal tsarin surarki na mamaki (wayyo Allah)
Kuma ga ki da kyan gashi yana walwali da adon ribbon na mata

Chorus

Badariyya

Badariyya
By Aminu Ringim Bagwai

Hmmmmmmmmm Hmmmmmmm
Bankwanaaaaaaaa
Soyayya mai sanya zumudi
Soyayya mai sanya zumudi
Wayyo Badariyya
Soyayya mai sanya zumudi
Wayyo Allah Badariya

[Chorus x 3]:
Soyayya mai sanya zumudi
Bankwana mai sa ai kuka
Godiya ga mutan Jama’are
Jam’are garin Badariyya

Allah mai qulla zumuncin qauna da ba’a yi zato ba
Waya ta zamo sanadiyyar soyayya rabuwa bamu so ba
Wata rana ne da daddare ina kwance barchi bai zo ba
Sai na ji waya a gabana tai ringing na daga sai na duba
So..
Sai muryar badariyya

Chorus

Yeehhh zuciya ta amsa kalamun qauna tun ido bai gani ba
Network ya bayyana saqon soyayya bamu gane gari ba
Said a soyayya tai nisa bamu chimma duka uzuri ba
Ido da ido na neman ganawa bamu samu gamo ba
So…
Rannan sai ga Badariyya

Chorus

Yeehhh da dai dai ta shigo garin Kano sai ta kira ni kamar a mafarki
Lokacin ina Dan’ladi Nasidi gurin Alba zan gaida aboki
Sai tace ka taho kayi tarba a Yan kaba nas samu masauki
Tace ka taho da kalaman soyayya muyi zama na tsanaki
Haba sai na kama hanya

Chorus

Na je Yan Kaba Masallaci a kofar yamma na zauna
Nai waya nace ga ni na zo na kwatant gurin da na zauna
Sai na chanza gurin da na zauna don in ga wacece zata zo nan
Sai naga fara kyakyawar yarinya ta taho ta gaba na
So…
Ashe itace Badariyya

Chorus

Ta zo ta tsaya a gurin ta bugo tace na zo babu kowa
Ina labe sai nacce mata nai nisa na gaji da tsayuwa
Da dai na ga tayi relax na fito ta gabanta ina warwasawa
Shine ta qure ni da kallon soyayyar nan na nuna yabawa
So..
Sai tace ni ce Badariyya

Chorus

Yehh muka gaisa ta ce Aminllah a yau sai mu gode Allah
Gwani day a wo sanadiyyar ganawa hart a san a yi kwalla
Tace gayyatar ka nake Jama’are bayan babbar sallah
Ina gayyatar ka bikin wata kanwata Allah sa zaku bulla
So..
Sai nace an gama Badariyya

Chorus

Yeehhh zan wuce ta qure ni da kallon soyayya mai ratsa masoya
Ta ce ka riqon uzuri na don Allah kar ka bar ni a baya
Ta ce ki sani zuciya ta in ta bug eke ce sanadiyya
Na ce na karbi amanar soyayya ban barinki a baya
So..
Sai mu kai sallama ta masoya

Chorus

Uhmmm randa zamu garin Jama’are buki tun karfe bakwai na safe
Na tashi naje na ziyarci abokaina Mukhtar da Nazifi
Na kira ta glass Audu D.J. shi da Jamilu ya zauna a gefe
Motar Ado dan Makwarwa yayana it ace muka dafe
So…
Mu kai ta gudu bias hanya

Chorus

Yeehhh muna tafiyarmu muna hira direba bay a kula kowa
Ka san hirar mu samari kullum ba ta wuce ta budurwa
Har Nazifi Usha ya yi barchi da Mukhtaru muke chakusawa
Muna ta gudu bias hanya ga yunwa ta hade da qishirwa
So..
Sai ga mobobi a hanya

Chorus

Muka tsaya suka nemi takardu ko lasi ko ranmu ya bachi
Direba idan Magana ta kudi za ai ga shi bas hi da asi
Sai n ace masu motata ce ni ma arzukinta na chi
Aminu Bagwai nake mai ta’aziyyar nan sai suka bamu karamchi
So..
Suka ce ku wuce babu sanya

Chorus

Hmmmmmmmmm Hmmmmmmm
Soyayya mai sanya zumudi
Soyayya mai sanya zumudi
Soyayya mai sanya zumudi

Chorus x 2

Yeehh da wajan karfe ukku daidai sai muka sa motarmu a titi
Na bude jakarmu na dauko cassette dina na warware sauti
Zuwa karfe hudu daidai muka je Jama’are masauki
Jama’are garin yan mata Jama’are garin alfarma
Jaa’are garin nono da fura garin girma da karama
Garin Ilmin addini kuma garin ilmmin zamani
So..
Dole in gaisuwa ga masoya

Chorus

Yeehhh gaisuwa ta faru da farko gun Shu’aibu yan Badariyya
Da Aliyu yaron Turai Yar’adua ban barinka a baya
Ina gaisuwa ga Dan-Liti Jama’are garin Badariyya
Ina gaisuwar yabo a gurin Sadiya kawar Badariyya
So…
Duk ba ni barin ku a baya

Chorus

Shu’aibu sai ya tare mu da mota ta kamfaninsu ya kaimu masauki
Aka bamu abinchi da namomin kaji har mu kai aswaki
Dagan an gimbiya Badariyya sai ta zo tai she mu a daki
Tace barka da zuwa angona yau fa ka chika aiki
So…
Ni kau sai ta bani kunya

Chorus

Zuwa bayan sallar Isha’ aka sa kayanmu a mota
Muma muka hau muka wurin party tun a nan nag a mata
Muna waqa suna rawa liqin kudi kau yana ta ratata
Zuwa qarfe goma na dare sai muka tafi gida muka kwanta
So…
Safiyar Juma’a muka juya

Chorus

Eehhh muka je gidansu amarya chan gurin da aka daura aure
Mu kai ta hadin rugugin kayan sauti har muka raba dare
Ga yan’mata suna rawa har ba ka banbanche na aure
Mata na makwauta na ta zuwa kallo har suna karya kyaure
So…
Nan na san ina da masoya

Chorus

Jama’a suka dunga zubar da kudi mu muna shirya su a kwali
Mata da maza na rawa a chuchchude hart a kece misali
Kullum in gari ya waye abinchi har ba misali

So…
A bikin qanwar Badariyya

Chorus

Toh ina gaishe da masoya na duniya masu saurarena
Gaisuwar fatan alkhairi da fatan haduwar mu da juna
Ina gaishe da Amina baby ta garin Gezawa
Da Ummi Nasarawa
Da Umma yar Dutsanma
Surayya Zaria na gaishe ki
Da Hauwa’u fara ta Okene
Da Basira Birnin Gwari
Da Bilkisu yar hotoro
Da Binta yar Hotoro
Bilki Jos na yi gaisuwa ta
Da gaisuwar Firdausi Kaduna
Da Hajiya Fati ta Hadeja
Da Hauwa’u yar Fanshekara tawa fara kyakyawar budurwa
Da Naja’atu yar Katsinawa
Yan’kara na gaishe ki kema
Da Lubabatu mai waqarmu
Da Awwal D.J. makadina
A ina ka ga Nafi’u Rabson
Mai recording gaisheka kaima
Gaisuwar SadiyaAli Baba
Ga ta yau ta tabbata ita ma
Gaisuwar Maryam ta garin Jos
Maryam fara doguwa kyakykyawa
Da gaisuwar wata Maryam din ta Kano
A chan kofar Nasarawa
Da gaisuwar Maryam ta kaduna
Fauziyya maman Baby
Aminu yana gaida ke
Dahiru Zaria na gaishe ka
Surayya Zaria gaishe ki kema
Soyayya mai sanya zumudi
Da qauna ta sa ni zumudi
Rabuwa ta haddasa kuka
Mutuwar Safiya ta Abuja
Gata nan ta bayyana itama
Soyayya ta sa ni nishadi
Karshe ta rabu da kuka
So..
Wayyo Badariyya
Wayyo Allah Badariyya

Chorus

Hmmmmmmmmm Hmmmmmmm
Bankwanaaaaaaaa
Soyayya mai sanya zumudi
Bankwana da ganin Badariyya
Soyayya mai sanya zumudi
Soyayya mai sanya zumudi
Wayyo Badariyya
Wayyo Allah Badariyya

Chorus x 3