Hausa Mai Ban Haushi

Hausa Mai Ban Haushi
By Alhaji Aqilu Aliyu

Saba da samo gaskiya duk nisa
Sarari da Boye kadan ka so bunqasa

Ga gargadi ya zuwa gare mu zumaina
Yayan Arewa da wanda duk ke Hausa

Ni nan da kai shi ke da su baki dai
Ku nan na kurkusa har na cana da nisa

Jama’a, mu karkade kunnuwanmu na zuci
Zancen da zanmana shi mu ji shi mu amsa

Na ce ma ja damara bajau qaqqarfa
Mui qoqarin tafiya garinmu da nisa

Qwazo ya kyautu da mu mu nuna kuzarin
Inganta harshen namu shi ne Hausa

Ku mu bar kasala, sai mu himmatu kun ji
Zazzage dantsen nuna kishin Hausa

Da yawan karambani kawai na kutso
Ba wai gwani ne ni ba kai nic cusa

Na ambata mana gaskiya daddata
Suka da harshe gansami kakkausa

Na gatsa hancin gaskiya mai ganci
Gafinsa na da yawa, ina mai lasa

Sukukun makaka kiki kaka,kaf kin kam
Tirkashi aiki ya yi kwancin kansa

Tsotso tsuku tsakiya tsare mafitsara
Allah tsare ni da ku karo da nahisa

Tsomo ka tsotse gwamatso ka yi guntsa,
In ka tsaya tsaf ka yi tswai, ka nisa.

Saurin musaya Hausa mai ban haushi
Sassake sauyi an sakar wa Hausa
x 2

Zarafin da mamaki gwanin ban haushi
Mugun barin sha’anin Bahaushen Hausa

Kowa da yare nasa bai kyama tai
Mu gamu mun tozarta harshen Hausa

Wai don gadarar mun jiyo Turanci
Har ba mu son magana da harshen Hausa

Tsuntsu kamata yai da shi ya yi kuka
Ya irin na kaka nasa can mai nisa

Ku sani Bature ba shi kin Turanci
In ya game da kininsa ko a makasa.

Faufau, ba ka ga, ba ka ji mai yare ba
Ya nuna Ri ga kininsa, sai mu Hausa.

In har akwai biyu masu jin Turanci,
Kuma ga na ukku cikarsu duk yan Hausa

In kai na ukkun ba ka jin Turanci
Biyu din na tare da kai sukan kiye Hausa

Tafiya fa tai tafiya, ma lura ma juyo
An ka da mu, mui koKarin shan fansa

Abu namu ne, mu rike shi kankan ya fi,
In man yi wasa dole zai mana nisa.

Mu riqe kaho ke nan a more tatsa,
Nonon a sha mu sai suda mu yi lasa

An bar mu gangambu, kago na jinka
Wasu can su sha inuwa Sagas lallausa

To kun ga aiki namu, ci na wadansu
An karkasa musu arha, sai su yi
Kwasa

Ba cas bare as, ba da kau da kara ba
Swadadas su sulle can su sha bunqasa.

Ta sa ni wannan na tuno wata hira
Wato karin maganar wajen yan Hausa

Wai na ji cewa Wane ya kasa gwaza,
Gefe waje daya mun ji ya kashe kasa.

Ban kasa kwashewar kashin gwazana
Domin ganin tarin kasassar kasa

Ba shirya waka ko karin zance ba
Jama’a, gudajin goro ya dara farsa

Bai zamto ci gaba, ban da cinye baya
In ka ki tinkaho da harshen Hausa

Kai ne da yas I see Halo Good morning
Wai ga Bature babu yayin Hausa

Ka debe alfarmark ka warwatsar
Ka bar wajen nasara, ka doshi nahisa

Tsini ka so don son gwanintar banza
Ka kasa kunda lokaci mai nisa

Bai san ba mako, sai ya ce wai Sati
Sai kun taba shi ya ce iyaye Hausa

Kaka uba yayyensa har dangogi
Ba sa da wayo ban da harshen Hausa

To mun ji ba yare gare su daban ba
Zaa tambaye ka da namu harshen Hausa

Amma ka ban amsa da zaran na yi
Domin in san kai ne Bahaushen Hausa

Ga tambayar nan, ba ni amsa kwaf dai
Miye kashereke da harshen Hausa

Wannan abin kunya ina tamka tai
Harshen wajen kakanka kai ka kasa

Ya zam abin a yi dariya a yi gwalo
A gare ka don ka fadi ba shan fansa

Ka zam marar ra’ayi kurum kyakykyawa
Don ba ka alfahari da harshen Hausa

Ka zamo shafi-mu-lera soko an nan
An ya da kai an bar ka baya da nisa

Ban nuna na dara ku tulin wayo ba
Sai dai ina kishi ga harshen Hausa

Tsuntsu yana bisa yai tsuhu tsororo
Tsiwa ta sa hali ya zam kakkausa

Gutsuro ka tsoma tsangwama ce tsantsa
Gatsa tsuko tsotso ba sa zama lasa
Ba wai habaici ne ba ko kyara ba
kyale ni kurkusa kar ka kai ni da nisa

Wannan gajeren gargadin da na kawo
Yan Hausa allai sa mu ji shi mu amsa

Mu bi gaskiya sak ba ciri ba coge
Da digirgire kar dai na kai mu da nisa

Ka zamo maje gaba kar a bar ka a baya
Maza gwamatso kusa kar ka yarda da nisa

Kowa ya shirya bazararsa don ya yi tsalle
Mu ga mu nan da bazar rawar mun kasa

Nuni nake mana don mu lura mu gano
In mun sake wasu za su sha bungasa

Ba na habaici ko na gugar zana
Don ratayar kaya na dan buga kusa

Mu tsaya da kwazo, kokari da kuzari
Tsaiwar daka mu tsaya mu kange Hausa

Bai kyautuwa mu sake mu zo mu ci baya
Har ma mu daddawo taba ka yi lasa

Ai ma kamata yai muna gaba an bi
Mil za mu dangwala dis wasunmu su lasa

Kai yan’uwa mu zubar da aikin banza
Ni na fada mana gaskiya yan Hausa

Ku mu daina yin sha’awa zuwa feleke
Ita kankara ku tuna fa ba to malasa

Mu zubar da kalen yare-yaren kowa
Mu kula da amfaninmu harshen Hausa

Ku mu kyautata ku mu kara inganta shi
Duk duniya bakinmu ba shi makusa.

Girma gare shi tuli akwai alfarma
Ba kankanen abu ne ba harshen Hausa

Da yawa yakan rika gwamatsa Larabci
In ban da Arabi ina misalin Hausa

Mui takama da abinmu, shi ne daidai
Shi ne abin faharinmu harshen Hausa

Ku ga dai su o’o da ban kira suna ba
An garzayo da gudu a kwashi rahusa

Amma fa ni ba zan yi ma rata ba
Mai tambayar suna taho ka ji amsa

Ni dai Akilu Aliyu nai wakena
Ba don a ce mini na fi kowa Hausa

Tafiya cikin sauri, a ce gaggawa
Sheqa gudu ke nan zubewa rusa

Kwara kwari kwararo kwaroron kura
Kore kare kurbatsi karyar karsa

Rago rago rogo ragowa raga
Rugugi rugurguza rungumar gargasa

Ban ce ba na dara wane ko kuma na fi
Sai dai nakan ciza na zo na yi busa

Allah nake Roko Gwani mai kome
Inganta bunkasar da harshen Hausa

Domin Muhammadu shugaban duka bayi
Allah ka fifitar da harshen Hausa

Albarkacin alayansa har sahabainai
Mata da yayayensa kome nisa

Zan dakata daga yanzu sai wata rana
Aikin da nai Allah hada shi da amsa

Domin Rasulullahi jigon bayi
Mai martaba in ya fada a amsa

Tsira ta karu gare shi ko wace rana
Kuma ba tuqewa ba iya adadinsa