Auren Dole

Auren Dole
By Dan Maraya Jos

Uwa da uba ga gargadi
Uwa da uba ga gargadi
Shi auren tilas babu kyau
Shi yakan saka yara gantali

Uwa da uba ga gargadi
Kun ga aure tilas babu kyau
Shi yakan saka yara gantali

Domin Allah ba ya so
Annabin Allah ma ba ya so
Domin yai hani a yi

Malam wannan yar ka ce
Malam wannan yar ka ce
Ga wanda take so tun tuni
Tun suna yan yara kankana
Domin ta saba da shi
Shima ya saba da ita
Mutumin kau da ka saba da shi
Ai yana da wuya a raba kuwa

Sai ka ce mata ba ka bata shi
Sai wanda kake so za ka ba
In kai auren ka jiya
Kai mata auren dole wai
Sai ka ji lalle ta chale
Baba ya mini auren dole ne
Tunda an min auren dole ni
To zama a gidan ba dole ai

Sai ka ga ‘ya kuma ta fita
Ta je gantali
Kan a jima ta je Kano
Sai ka ji ta kai Samuru
Sai ka ji ta je har Gusau
Kan a jima in ka tuna
Sai ka ga ta kai har Kuta
Ko da kudin mato ta je
Ko babu kudin mato ta je

Uwa da uba in kun tuna
Wannan abu ku kuka haddasa

Idan da kudin moto ta je
In babu kudin ma to ta je
To uwa da uba in kun tuna
Wannan abu ku kuka haddasa
Kun san wannan laifin ku ne

Uwa da uba in kun tuna
Ni dai rokon ku nake ta yi
A bar auren tilas dada
Tunda da dai Allah ba ya so
Kuma Annabi yayi hani a yi