Mata Ku Dau Turame

Mata Ku Dau Turame
Nazir M Ahmad

[Chorus]

Mata ku dau turame ya yi
Kuma ku ce nadi dai anyi
Sarki Kano Sanusi na II
Duniya tai dadi
Kuma ku ce Kano Dan Lamido
Uban matasa yayi

Wannan kidi kidin mata ne
In namiji ya taka yawa ne
Dada mu bar su suyi sha’aninsu
Mu dai muce Kano Dan Lamido
Uban matasa yayi

Mu dai mu ce Kano…
Kano…
Kano Dan Lamido

Chorus

A’a nace ku ce Kano…
Kano..
Kano Dan Lamido

Chorus

Kai farin ciki mutane rairai

Eyy mu bayyana mu jero daidai
Mu tara tara taro dai-dai
Mai takura da takon Lamido
Sanusi babban sarki

Kai ana daka ana Dan Lamido

Eyy ashe zuma tana nan zai-zai
Suma mabi bin ta zai-zai zai-zai
Ga shi muna kidan Dan Lamido

Kai mu kada kai muna Dan Lamido

Eyy Kano Dan Lamido
Na ce ku kada kai ana Dan La
Sarkin Kano Dan Lamido
Ga shi ana ta za.. Kano.. Kano
Ga shi Muna ta murna da sanusi
Sanusi mai Kano Dan Lamido

Chorus

Toh mazan kwarai suna bisa aiki
Matan kwarai kau kullun aiki
Wannan kida kidan mata ne
Yawan kidan na mai gata ne
Talaka mai kudi dai-dai ne
Ku doka tamburan Allah raini
Sarkin Kano matarar yaqi
Kun ga tsakin tama Dan Audu
Mai ilimi kuce insanu
Da ya fito a kwana da nunin
Qasan saninsa kullum yafun
Ba aljani bare ifritu
Maza jiran maza Dan Audu
Ko ma su qin ka sai sun so ka
Tunda Rabbi ya baka
A ko a kwance kai barcinka
Ja mu je zuwa sarkinmu
Babanmu mai tsare kukanmu
Taho mu je zuwa dan baiwa

Chorus

Ku dai mu ce Kano…
Kano..
Kano Dan Lamido

Chorus

Da na ji gangunan sun tashi
Sai in kira Yarima in gama
Da na ji dunyar ta dauke
Sai in kira Yarima in gama
Ruwan dollar yane man dai-dai
Wannan sakin ya ne Dan Lamido

Chorus

Toh ku zo mu je ga Sardaunan Dutse
Ehh Sardaunan Dutse
Nace da Sardaunan Dutse
Jallah mai kwana sallah
Jarman Wudil yana nan shima
Kuma ya na ta jin Dan Lamido
Sanusi babban sarki

Chorus

Dada e kai mu tafa hannuwa sai Lamido
Ehh Kano Dan Lamido
Kai mu bashi hannuwa Dan Lamido
Sarkin Kano Dan Lamido
Kai mu kada kai muna Dan Lamido
Ehh Kano Dan Lamido
Nace kai ku kada kai ana Dan Lamido
Sarkin Kano Dan Lamido
Kun ga muce Kano Dan Lamido
Uban matasa ya yi
Allah shi taya ka riqo (amin)

Wazobiya

Wazobiya
By Adam A Zango

Wazobiya…
Rayuwa sai da naira
In babu naira
Toh ko ka zam kwalele

Eyyyy yeh yeh yeeeh
Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Jama’armu ku saurara cikin kidanmu ba ma yaudara (wazobiya)
Kidan na bahaushe ne waqar ta Hausa ce kuma ba dabo (wazobiya)
Kalangu dan Hausa da ba’a yi mai jan kunnuwa (wazobiya)
Idan baku gane ba ina nufin Bature nai nufi (wazobiya)
Don ko da ya ji zai jinjina wa Hausa da al’uma

Ehhhhhhh
Yar yar yar lale lale kalangu shine kida

Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Mata nayi kira gaba dayanku sai ku yi tarbiya (wazobiya)
Duk kyawon mace in bada kyan halin kyawon kawai (wazobiya)
Mata kuyi aure ku dena zagayawan bariki (wazobiya)
Toh ga wata tai kwantai saboda kun ga bata da tarbiyya (wazobiya)
Yawan tarnaqiya yana ba mazaje sha’awa
Lai lai lale lale kalangu shine kida

A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)
Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Samari nayi kira a duniya ku bar yin yaudara (wazobiya)
Idan kunje tadi ku daina latsa yan’mata haka (wazobiya)
In ko kun qi ji toh in kuka haihu sai an maku (wazobiya)
Toh samari muyi sana’a mu daina dauke-dauke ga al’ummah
Toh duk nairar gaye idan da dan-hali nairar kawai (wazobiya)
Toh samari kuyi aure nai kira ku daina ruwan ido
Lai lai lale lale kalangu shine kida (eh.. ah.. ah.. toh..)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Kai ka ji kidan naira da ko mahaukaci na rausaya (wazobiya)
Duk tsufan tsoho idan ya ganta sai yai rausaya (wazobiya)
Toh kogi ya kawo ku zo mu sanya gora muyi hito (wazobiya)
In dai naira ce da ka biye ta yanzu ka bata (wazobiya)
Naira mai sa fada da uwa da uba kai duniya (wazobiya)
In dai kana da naira gidanku kai ne alhaji (wazobiya)
Ko da kai laifi gidanku babu mai yi ma fada
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Lai lai lale lale kalangu shine kida
Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Yaran zamani kuje ku yo karatu ya fi kyau (wazobiya)
Kai duk gayun gaye in babu ilimi hoto kawai (wazobiya)
Iliminmu na addini da boko ya zama garkuwa (wazobiya)
Toh mata kuyi ilimi domin ku bai wa ya’ya tarbiya (wazobiya)
Yarinya kyakykyawa ku zo ku ganta amma ba aji (wazobiya)
Ba Arabi ba boko cikin gidansu ta zama akuya meh (wazobiya)
Idan za’ai aure a dunga bincike kar ai tumun dare
Lai lai lale lale kalangu shine kida (ahah!)

Akwai wasu na magana da ni da Zango ba yan Hausa ba (wazobiya)
Kuce wacece ce kuce mai kar ce ta rage wa baqin ciki (wazobiya)
Idan kuma caca ta ci ta samu kurciya don suyi ciro (wazobiya)
Idan baka gane ba ka zo da Hausa zan ma tambaya (wazobiya)
Idan ka ban amsa in tarbatar bahaushe ne kake (wazobiya)
In dai a Hausa ne gidanmu babu baubawan bara (wazobiya)
Toh barewa ta yi burus cikin birgimarta a bariya (wazobiya)
Bar barna bara na Kare wa ke bin mutum ba tarbiyya (wazobiya)
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Eyyyy yeh yeh yeeeh
Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

A hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

A hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Yan’matan duniya
Samarin duniya (wazobiya) x 5

Dinya
Samarin duniya (wazobiya) x 3

Sai da Dan Koya

Sai da Dan Koya
By Ashiru Nagoma

Uhmmm
Sai da dan koya akan yi gwani in ji Dan Auta
In har kana koya wata ran za ka zam gwani babba

[Chorus]
Uhmmm
Sai da dan koyo akan yi gwani in ji Dan Auta
In har kana koya wata ran za ka zam gwani babba

Uhmmm
Sai da dan koya akan yo gwani in ji Dan Auta
In har kana koya wata ran za ka zam gwani babba

Ina masoyana ga saqo na gaisuwa kyauta (uhmm Dan Auta)

Wannan masoyinku ne Nagoma Ashiru Dan Auta (uhmm Nagoma)

Wayanda ba sa so na ina so su zo mu sasanta (uhmm Dan Auta)

Da sannu sannu idan ka nay wata ran zaka zam babba

Chorus

Uhmmm
Idan ka ji ance wannan shi ya iya sosai (uhmm Dan Auta)

A can a baya sai da ya koya ya yi zama sosai (uhmm Nagoma)

Kafin ya samu abun da yake so ya ci wuya sosai (uhmm Dan Auta)

Yanzu ku dan lura ku fahimta shine gwani babba

Chorus

Ina mawakan Kaduna na zo ku zo ku shafan kai (uhmm Dan Auta)
Ina mawakan Kano ta Dabo ku zo ku shafan kai (uhmm Nagoma)
Ina mawakan Katsinawan Dikko ku zo ku shafan kai (uhmm Dan Auta)

Mawakan Zamfara ke bin na Sokoto ku zo ga Dan Auta

Chorus

Uhmmm
Sai da dan koya akan yi gwani in ji Dan Auta
In har kana koya wata ran za ka zam gwani babba

Chorus

Uhmmm
Sai da dan koya akan yi gwani in ji dan auta
In har kana koya wata ran zaka zam gwani babba

Chorus

Uhmmm
Ina matasa ina kiranku ku daina sa’insa (uhmm Dan Auta)

Baiwa ta Allahu ce ku gane mu daina yin gasa (uhmm Nagoma)

In Rabbi ya yarda lamuranka ba wanda zai amsa (uhmm Dan Auta)

Wannan misali ne a kaina baiwa ta Dan Auta

Chorus

Nigeria ha kasa ce ta gado mu daina tababa (uhmm Dan Auta)

Yawan fada shi ne ke kawo ana zaman gaba (uhmm Nagoma)

Sannan ya kan kawo tabarbarewa na arziki babba (uhmm Dan Auta)

Mu na kiran al’umma mu gane ku bar zaman gaba

Chorus

Zama na qarshe da magaifiyata tai min addu’a sosai (Allah ya amsa)
Zama na qarshe da Abba gare ni yay mani addua sosai (Allah ya karba)
Nima a yanzu garesu sai dai na yi addu’a sosai (Allah ya amsa)
Domin nay ladabi da biyayya Allah ka dafa min

Chorus

Auren Dole

Auren Dole
By Dan Ladi Kima

Ni ba na soooo
Ni ba na sooo

O’o jama’a ku taya ta

Ni bana son shi babana
Auren ga na dole ba na so
Ku mun adalci inna ta
Ni auran dole ba na so

Ina da masoyi dan lalle
Mai addini ta tarbiya
Ki gafarce ni innata
Ina roqon ka babana
Iyayena ku qyale ni
Ina qaunarsa mamana
Ku bar ni na auri mai so na
Iyayena ku wa Allah da manzo mai tsarki
A kan auren da bana so
Ina neman sauqi
Iyayena ku bar mani auren dole
Yana kawo ya sanya diyarku ta walle
Ku gane yau a ko ta ina an waye
Iyayena ku wa Allah da manzo mai tsarki
A kan auren da bana so
Ina neman sauqi

Ina da masoyi dan lalle
Mai addini ta tarbiya
Ki gafarce ni mamana
Ina roqon ka babana
Dan-Ladin Kima yayana
Mu je ka raka ni dangina
Mu je in fada wa kakana
Auren ga na dole ba na so

Qarshen tika-tikin kima
Na ce qarshen tika-tikin tik (aha!)
Qarshen tika-tikin tik
Allahna yana bayani (ashe!)
Qarshen tika-tikin tik
Annabi ma ya na bayani (gaske!)
Qarshen tika-tikin tik
Bi iyayenki kar ki kore (gaske!)
Qarshen tika-tikin tik
Zan so ki zugun ki gane (aha!)
Qarshen tika tikin ooo
Qarshen tika-tikin tik
Qarshen tika-tikin tik
Auren dole babu kyawo (ehe!)
Qarshen tika-tikin tik
Shi ke sa diyanmu yawo (haka!)
Qarshen tika-tikin tik
Bijirewarsu babu kyawo (aha!)
Qarshen tika-tikin tik
Ku bar mata zabi ya fi kyawo (gaske!)
Qarshen tika-tikin ooo
Qarshen tika-tikin tik
Qarshen tika-tikin ooo
Qarshen tika-tikin tik

Ni bana son shi babana
Auren ga na dole ba na so
Ku mun adalci innata
Ni auran dole ba na so

Ina da masoyi dan lalle
Mai addini ta tarbiya
Ki gafarce ni innata
Ina roqon ka babana
Iyayena ku qyale ni
Auren ga na dole ba na so
Ina qaunarsa mamana
Ku bar ni na auri mai so na

Ina da masoyi dan lalle
Mai addini ta tarbiya
Ki gafarce ni innata
Ina roqon ka babana
Iyayena ku qyale ni
Auren ga na dole ba na so
Ina qaunarsa mamana
Ku bar ni na auri mai so na

Inna ki dakata
Baba ka dakata ni naku ne
Wanga diyar ga ta baya taku ce
Yaya amana Ilahu ya ba ku (I mana!)
Ya ce a lura ake ta kula da mu (aha!)
Fannin karatunmu da tarbiya (aha!)
Kwanci da tashinsu idanku duk
Yana a kansu dare ko safiya
Amma diya mace rauni nata ne (I mana!)
Ko ya alamar sai ke nata ne (haka!)
Yawan sakin-sake auren dole ne
A bata zabi cikin uku dau guda
Idan na yo kura kar kuy tir da ni (I mana!)
Koko a ce za ay wadarai da ni (aha!)
Kuy mun du’ai zaya tarar da ni
Inna ki dakata
Baba ka dakata ni naku ne
Inna ki dakata
Baba ka dakata ni naku ne (Ba shakka!)

Mai Makka Sayyadi
Mai Makka Sayyadi
Mai Makka har da Madina Muhammadi
Na tuba na bi Ilahu gaba daya
Ya Mahmudu gare ka na zo niya
Aure na dole ake so ay mani
Ni kuma ko kusa sam-sam bani so

Makka Sayyadi
Mai Makka Sayyadi
Mai Makka har da Madina Muhammadi

…babana
Auren ga na dole ba na so
Ku mun adalci innata
Ni auran dole ba na so

Ina da masoyi dan lalle
Mai addini ta tarbiya
Ki gafarce ni innata
Ina roqon ka babana
Iyayena ku qyale ni
Auren ga na dole ba na so
Ina qaunarsa mamana
Ku bar ni na auri mai so na
Ina qaunarsa mamana
Ku bar ni na auri mai so na
Ina qaunarsa mamana
Ku bar ni na auri mai so na

Mata Ku Yi Aure


Mata Ku Yi Aure
By Mamman Shata

Don Sallah da Salatil Fatih
Don darajar kakan Tijjani

[Chorus]
Don Sallah da Salatil Fatih
Don Allah mata kuyi aure

Don Sallah da Salatil Fatih
Don Allah mata kuyi aure

Chorus

Don Sallah da Salatil Fatih
Don darajar kakan Tijjani
Kun ji kidan da nayi wa mata
Kado ya so ya wulaqantani

Chorus

Alhaii bai taba yin zambo ba
Ni kuma bana zagin kowa
Kun ga dugunzuma ya sa nayi
Allah ya isa Kadon Bauchi

Chorus

Wai don na ce mata suyi aure
Shi ko ya ce masu kar suyi aure
Mun sabani a Jos
Mun daidaita rannan a bikin Babangida
Sai a Kaduna ta koma danya
Ya zagi su Lalo gidan Mai-koko

Chorus

Amma fa uwata in za’a yi mani aure
Goggo idan za’a yi man aure
Inna idan za’a yi mani aure
Baba idan za’a yi man aure
KAwu idan za’a yi man aure
A bar ni in zabi fari kyakykyawa
Kar da a bani baqi mummuna
Auren tilas ba aure ne ba
Shi kesa wasu yawon banza

Chorus

Don na taba jin a wurin babana
Shima ji yayi a wurin kakana

Chorus