Hada Kan Mu Africa Mu So Juna
By Abubakar Ladan
Yarda da abota soyayya
An shudu da juna ta sanayya
Gorin asali ko jayayya
Ba gaba an daina qiyayya
Ra’ayi ya zo daya an shirya
Turawan mulki sun tashi
Mun kakkabe hannu ba bashi
Sune Africa muke kishi
Hada kai ne yau mai kaushe shi
An samu hadadden harsashi
Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna
Saura a Mozambique da Angola
Da Guinea sun saura cikin wahala
Hada kai ne babban bulala
Wallahi da zaran mun tsala
Duka sauran za ka ga sun lula
Saura kuma me ya rage mallam
Hada kai a Africa wajen ni kam
Sai an so juna an yi na’am
Sai an hada kai ya tsaya mallam
Kan qauna ya tsayu ba kishi
Daga baya abota zai bi shi
Daga zaran ga abu ya tashi
An shawarta bisa karshe shi
Koko a tsaya kan samo shi
Hada kai ne babban harsashi
Hada kai ke nan ya wakkana
Domin ko abota ya zauna
Daga nan yanci zai amfana
A ji dadi sannan ai murna
Hada kai ba tarore ba kawai
Ba cacar baki ne ba kadai
Ko waye yai ta fadan son rai
Kan an watse taron dada sai
Ya mace kurmus domin ba rai
Hada kai ba wai hada baki ba
Ai zambo ko ai cuta ba
Da wulaqantar da mutane ba
Ko zalunci da fashin kai ba
Yanci bai yarda da wannan ba
Dukkan fitina daga jahilci
Take tushe kau nata lalaci
Shi ke jawo a yi zalunci
Da matsawa gun karbar hanci
Duka ba wannan a cikin yanci
Kyamar juna da yawan gori
A Afirca akwai su tsibi tari
Da kwafar zuci da yawan fahari
Da muke gasanmu da inkari
A ciki hada kai su ne sharri
Allah Shi ne ya ni’im’imta
Afirca kasarmu dukkaninta
Muka wofantar muka lalata
Da jibin goshi muka ya’yanta
Ya za mu yi yanzu mu more ta
Sai kam ba masu munafunci
Da wadanda suke nukurar yanci
Ra’ayinmu ya zo ba bambanci
Mu fahimta mu face wajen faci
Don more Afirca kasar yanci
Kwadayi ke ta da wulakanci
Shi ke cin karfin adalci
Da siyasannan na faqiranci
Ka shake cikinka da zalunci
Me za ka fada a cikin yanci
Mai wannan hali yau shi ne
Hadari a Afirca da mun gane
Komai ya fada mana karya ne
Don mun san logar zambo ne
Mai yin wannan la’ananne ne
Ba masu siyasar maula ba
Makiya yanci dillalai ba
Da idan ba su tuba da wannan ba
Hada kai ba zai wani karko ba
Yanci kuma bai dada komai ba.
Mulkin kai ba son kai ne ba
Ba miqe qafa a ci dadi ba
Ba alqawarorin qarya ba
Inda masu irin wannan a gaba
Yanci bai tsinana komai ba
Sai an manta da su zalunci
An zauna an kashe jahilci
An tumbuke tushen lalaci
Roqo da bara da tumasanci
Na rashin aiki da yawan barci
To sai ka ga an more yanci
Wallahi idan ba son juna
Hada kai da wuya ka ga ya zauna
Kullum ka gano sabon fitina
Jayayya ko neman magana
Sai an so juna an daina
Fitina barci take ba ta fita
Allah wadaran mai tado ta
Da wadanda suke dada jawo ta
Haka nan da wadanda ka kawo ta
Allah ka tsare mu da tashinta
Yaqi biyu yau aka lazumta
A Afirca na farko yayanta
Dauloli duk na qasashenta
Sannan hada kai na mutanenta
Kan an san wannan an huta
Yau ga wasu nan suke nukura
Don mun san yanci mun nasara
Wasu ma a cikin nasu sun fara
Hada gulma tsakani don a kara
Ko oho gama kuwa sun dara
Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna
Zaman mu da ku dai ya qare
Daimon da kuzanmu da zinare
Komai mun kwace mun tare
Ba sa son wai su ga mun more
Yau sun dage su ga mun dare
Kan ka ji fada yau ya tashi
Wasu baqi ne ke kawo shi
Don sun ga haqiqan sun tashi
Hada kanmu suke dada kishinshi
Komai kuwa sa yi su bashe shi
Da wadansu suke hada ma gwiwa
A Afirca akwai wasu yan yunwa
Da suke karbar kurdi da yawa
Rikici duka su ke jawowa
Ku mu tashi hana su da gaugawa
Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna
Da mun hada kanmu Afirca duka
Ba ka jin kyas wani ya yi haka
Sai mun so juna ba shakka
Sannan mu fice wannan halaka
Da rashin hada kanmu ya zo da haka
Afirca mutum ne yantacce
Hamshaki kuma ingantacce
Maikarfi ga shi amintacce
Da basira ilmi tatacce
Da fari da baki miji ko na mace
Harkar bawa ya zam kurra
Daga loton nan ne zai fara
Amfanin kansa yana shukura
Ya bido hakkinsa ya tattara
Ko jikoki nasa sa mora
Ya zamanto da ne mai himma
Bisa sabgar kyautata al’uma
Kan an haka ba sauran hamma
Talakawa ba wani mai rama
Ba sake zama a cikin tsumma
Duka da an so shi ya inganta
Kasa ta tarar da wadansunta
Za su yi sha’awa su ziyarce ta
Da kafarsu su zo su yi kallon ta
Komai ba mai iya kushe ta
Kan ko ka bar talakawanka
A cikin yunwa da zaman bukka
Ko yawon maula ko sadaka
Ka sani har yanzu suna sarka
Kowa ya gani zai zage ka
Lallai ne zurfafa hannunka
A cikin ramin aljihunka
Ka fitar da kudi kuma mai tsoka
Manqudai don aikin talaka
Kan kai wannan ba mai kin ka
Da fadawa zabura kai aiki
Nan ne aka san mutumin kirki
Ma’abucin adalcin mulki
Kuma ba mai ce maka cin kaski
Mai zalunci ya shiga daki
Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna
A kasa duka mai mulkin kanta
An so a tarar da mutanenta
Qosassu babu tsiraraita
Da rashin aiki da galabaita
Ko yawon banza ko sata
A kasa duka kam ba tarbiyya
Ba ci gaba sai ta tsaya baya
Sai girman kai kaya-kaya
Da kwafa da rashin tuna can baya
dan qauye ya shiga alkarya
Ga riga na dibar hakki
Ga kantar dauda ba wanki
Sai ya hango mai alkaki
Ya kira ya saya ya ci yai tanki
Gagon sai ya ji yana hakki
Ni Garba ina tausan kanmu
Ba ma fatawan neman samu
Sai zare ido a wajen damu
Muyi yaqi mu yi ta bidar ilmu
Shi ne manufar mulkin kanmu
Allah ya Allah ya Allah
Hada kanmu Africa mu so juna
Ilimi babban abu ne gun mu
Shi zai kakkange mutucinmu
A qasa shine akasin zulmu
Da yake bude kofar samu
Da wuya ka ji ga wasu sun fi mu
Ga mulkin kai an kakkarba
A Afirca kadan muka dan saba
Kowa da abin da ya zazzaba
Na wadansu abin har ya zoba
Da ya ja masu jar wahala da shuwa
Liberia ko ni na ganta
Su ne farko suka yayanta
Da ta dau nauyin rike yayanta
Ta san wahalar da ta fuskanta
Allah ya taya ta rikon kanta
Ethopia tun tuni sarki ne
Sarkin nan ko shahararre ne
Sha’anin mulki gogagge ne
Mai yin fara’a da mutane ne
A Afirca SelassieAboki ne
Mulkin da ya karba Sekou Toure
Da turawa sun tattare
Yanzun ba saura sun tsere
Sai daidai wanda ya tsattsare
Allah ya taya su zaman tare
Gold Coast ta samu sai murna
A qasar da ake cewa Ghana
Ku rike mulkinku ku amfana
Da aminci himma da lumana
Kan an haka yanci ya zauna
Sierra Leon sarqa sun yaye
A cikin himmar mister Magaye
Dukkan jama’a kuma ya yaye
Turawan mulki sun janye
Kuma ba fitina ba tawaye
Senegal qasa mai albarka
Su ma duka sun kwance sarka
Da Jalof da Walof yau sun farka
Daga barci yanzun ba shakka
Duka kowa na barka-barka
Cewar Mishar Mukhtar Dada
Mauritania yanzun ba abda
Yantattu ne ni na shaida
Sun dau mulkin kai ba zubda
Jini a qasarsu abin guda
Algeria yau da jibin goshi
Sun san rinjaye da faranshi
Turawan mulki sun tashi
Wuta duka ta mutu sai gaushi
Ben Bellah mu taru mu gaishe shi
Mu gusa mu ga Marshall Burjiba
Mai himma bai iya wargi ba
Ya san yanci tun ba yau ba
Tunis yaya ne sun ci gaba
Ga aiki daman sun saba
Mu gusa mu ga daular Libia
Horarru ne na Italiya
Sarki mai kyakkyawar niyya
Komai aka ce mashi za shi iya
Domin kuwa ba shi abin kunya
Mu yi biza mu ziyarci Masar
Ta Ra’isu Jamal Abdul Nasir
Ya dau mulkin kai babu na tir
Komai aka ce mar za shi idar
Da wuya ka ji an ce ya wahalar
Mu shige jirgi mu ga Sudani
Sun dau mulki fanni-fanni
Ibrahim mai aiki da sani
Mun sami abokai Ikhwani
Da aminci tun tsohon karni
Ta Sahara za mu bi sai Chadi
Sun dau yancinsu gwanin dadi
Ba garmi abokai na nishadi
Tamal ba ya nan bisa kan sirdi
Mutumin kirki bayya fadi
Mu biya ta Kano mu shige Niger
Sun dau mulkin kai ba wani ja
In ja don sun kawo hujja
Don Dori mutum ne mai daraja
Hamani aboki afuwaja
Daga nan mu ziyarci Upper Volta
Su ma can duk sun yayanta
Mursawa yau sun sabunta
Moris mai son sada zumunta
Ya mai gwado ba shi galabaita
A Wugadigu jirgi za mu shiga
Mu wuce fadar Abidjan ma ga
Ga Huhunye Banye yana yanga
Don ko bai yada abin tsarga
A qasarsa da ba wasu yan targa
Ku mu hau mota mu wuce Mali
Sun dau ‘yanci babu jidali
Yanzun sun tashi bidar jali
Ca a Modibbo Keita yana a Mali
Wani kyakkyawa mai kyan hali
Mu haye jirgin sama sai Cameroon
Su ma yaya ne a hararu
Mani’imta ne a cikin hanu
Kuma ga ihisani ba sharru
Daga nan jirginmu ya dirkako
Sai Center-Afirca mu sassabko
Mu ga mulkin nanna David Dako
A qasarsu da kansu suke iko
Ba ka jin wani da wani yai soko
Daga nan ne zan bi tsawon kogi
Mu yi ban kwana da mutan Bangi
Sai Brazzaville mu gano dangi
Sun takura sun balle kangi
Don Youlu ba shi abin zargi
Ku mu ketare kogi sai Belji
Na duba kasa sai jeji
Sun dau yanci kowa ya ji
Tuni Kongo suke yin karaji
Ba sa kaunar mulkin Belji