Soyayya Dadi

Soyayya Dadi
By Adam A Zango

Eyy soyayya dadi idan har da ke zana yi
In ba ke wa zani kalla a bayan rai

Soyayya dadi idan har da kai zana yi
In ba kai wa zani kalla a bayan rai

Bayan rai sai mutuwa ajali dole
Riga ce babu guda wanda zai tube

Mai so na daure ki juyo na kalle ki
Don murna zan cika raina da mamaki
Kin yarje na kama gefen mayafinki
Dacena kin ban wuri ranki na zauna

Bayan rai sai mutuwa ajali dole
Riga ce babu guda wanda zai tube

Doka tambarin qauna taurarona mai haska samaniya
Zo ka cika burina ka yarda da ni hannunka na dan riqe

Iye zo ki cika burina ki yarda da ni hannunki na dan riqe

Ba ku ji bayani ba taurari ne ado na samaniya
Bisa sama in sun ka so haske nasu sai ya kewaye duniya

Iye cikin ido sahiba kin yi kwarjini
Tun haduwarmu na yo farin gani
Babu nadama ko da na sani
Daga haka mun ka hadu qauna ta dadu sai so ba fariya

Bisa sama in sun ka so haske nasu sai ya kewaye duniya

Na ji dadi ne gari da can haka an sa min mari
Murmushin alkawari zan yi miki babu saraurari

Na ji dadi ne gari da wuyar so gara shiga haure
Murmushin alkawari zai sam abun alfahari

Zan tsaya tare da kai zan baka kula ba sake (Bayan rai)
Kayanka na cancana in babu sai in sha rake (Bayan rai)
Alfarmata da kai inuwar ka ka barni ina fake (Bayan rai)
Bayan rai babu ni laifi in na yi ka haquri

Na ji dadi ne gari da wuyar so gara shiga mari
Murmushin alkawari zai zamabin alfahari

Eyy soyayya dadi idan har da ke zana yi
In ba ke wa zani kalla a bayan rai

Soyayya dadi idan har da kai zana yi
In ba kai wa zani kalla a bayan rai

Bayan rai sai mutuwa ajali dole
Riga ce babu guda wanda zai tube

Wazobiya

Wazobiya
By Adam A Zango

Wazobiya…
Rayuwa sai da naira
In babu naira
Toh ko ka zam kwalele

Eyyyy yeh yeh yeeeh
Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Jama’armu ku saurara cikin kidanmu ba ma yaudara (wazobiya)
Kidan na bahaushe ne waqar ta Hausa ce kuma ba dabo (wazobiya)
Kalangu dan Hausa da ba’a yi mai jan kunnuwa (wazobiya)
Idan baku gane ba ina nufin Bature nai nufi (wazobiya)
Don ko da ya ji zai jinjina wa Hausa da al’uma

Ehhhhhhh
Yar yar yar lale lale kalangu shine kida

Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Mata nayi kira gaba dayanku sai ku yi tarbiya (wazobiya)
Duk kyawon mace in bada kyan halin kyawon kawai (wazobiya)
Mata kuyi aure ku dena zagayawan bariki (wazobiya)
Toh ga wata tai kwantai saboda kun ga bata da tarbiyya (wazobiya)
Yawan tarnaqiya yana ba mazaje sha’awa
Lai lai lale lale kalangu shine kida

A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)
Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Samari nayi kira a duniya ku bar yin yaudara (wazobiya)
Idan kunje tadi ku daina latsa yan’mata haka (wazobiya)
In ko kun qi ji toh in kuka haihu sai an maku (wazobiya)
Toh samari muyi sana’a mu daina dauke-dauke ga al’ummah
Toh duk nairar gaye idan da dan-hali nairar kawai (wazobiya)
Toh samari kuyi aure nai kira ku daina ruwan ido
Lai lai lale lale kalangu shine kida (eh.. ah.. ah.. toh..)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Kai ka ji kidan naira da ko mahaukaci na rausaya (wazobiya)
Duk tsufan tsoho idan ya ganta sai yai rausaya (wazobiya)
Toh kogi ya kawo ku zo mu sanya gora muyi hito (wazobiya)
In dai naira ce da ka biye ta yanzu ka bata (wazobiya)
Naira mai sa fada da uwa da uba kai duniya (wazobiya)
In dai kana da naira gidanku kai ne alhaji (wazobiya)
Ko da kai laifi gidanku babu mai yi ma fada
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Lai lai lale lale kalangu shine kida
Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Yaran zamani kuje ku yo karatu ya fi kyau (wazobiya)
Kai duk gayun gaye in babu ilimi hoto kawai (wazobiya)
Iliminmu na addini da boko ya zama garkuwa (wazobiya)
Toh mata kuyi ilimi domin ku bai wa ya’ya tarbiya (wazobiya)
Yarinya kyakykyawa ku zo ku ganta amma ba aji (wazobiya)
Ba Arabi ba boko cikin gidansu ta zama akuya meh (wazobiya)
Idan za’ai aure a dunga bincike kar ai tumun dare
Lai lai lale lale kalangu shine kida (ahah!)

Akwai wasu na magana da ni da Zango ba yan Hausa ba (wazobiya)
Kuce wacece ce kuce mai kar ce ta rage wa baqin ciki (wazobiya)
Idan kuma caca ta ci ta samu kurciya don suyi ciro (wazobiya)
Idan baka gane ba ka zo da Hausa zan ma tambaya (wazobiya)
Idan ka ban amsa in tarbatar bahaushe ne kake (wazobiya)
In dai a Hausa ne gidanmu babu baubawan bara (wazobiya)
Toh barewa ta yi burus cikin birgimarta a bariya (wazobiya)
Bar barna bara na Kare wa ke bin mutum ba tarbiyya (wazobiya)
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Eyyyy yeh yeh yeeeh
Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

A hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

A hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Yan’matan duniya
Samarin duniya (wazobiya) x 5

Dinya
Samarin duniya (wazobiya) x 3

Babbar Yarinya

Babbar Yarinya
By Adam A Zango

Ehhh babbar yarinya nai sa’a
Na zamo auta cikin maza

Eehhh haduwarmu da kai shine sa’a
Baya nai dace a yan mata

Aaaaah aaaaaah

Hankali ke sa ayo girma
Rasuwa mataki cikin girma
A gurinki dukkansu kin sama
Ko a cikin sunanki akwai girma
Babbar yarinya lakabinki
Ke na raba dan nayo girma

Duhu bai dusashe haske
Dukkam mai ido shi zaya fada
Idan akwai ka ba’a batuna
Ganinmu da kai ke karan girma
Manyan yara da sun gan ka
Su zo da sauri kai su karrama

So da kauna shi nake nema
In dai a gu nane tuni ka sama
Lallai gareki ina da alfarma
Ko wanne ka kawo ka sani zanyima
So ya kai so tsakaninmu
Ba na gajiya gunyi miki hidima
Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Baya nai dace a yan mata

Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Baya nai dace a yan mata
Eh nazari nayo a kanki
Da tabbacin banyin nadama
Kin yi min shimfida ta fuska
Zahiri ta zarce tabarma
Nai rawa a gabanki nataka
Zo kimin naki salon kema
Allah nunan masoyanmu
Ka tsaremu sharri na yan gulma
Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Baya nai dace a yan mata

Haduwarmu da kai shi ne sa’a
Kayo nisa cikin raina
Ba’a hangenka barema a cimma
Gangancine ace za’a iske ka
Ko dan gajiyar tafiya a suma
Tunda na tsinke zaren birki
Yan samari sai kuyi ta himma

Eeehh babbar yarinya
Nai sa’a na zamo auta cikin maza

Ehh haduwarmu dakai shi nai sa’a