Rayuwa
By Fati Musa
[Chorus x 2]:
Rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba’a yi ba
Rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba’a yi ba
Da fari zan sanya Khaliqina mamallakin duniya
Ya qagi balbelu da yawa nasu ya yi su da kala daya
Ya bani haske in raira waqa ya qarfafan zuciya
In yi ta tun yau don wata ran babu ni cikin duniya
In yi tat un yau don wata ran babu ni cikin duniya
Zan zamo kamar ba’a yi ba
Chorus
Ina salati ina salami ga shugaban duniya
Wanda ya shirayar da kafirawa ya basu kalma daya
Ya shugabantar da manya manya sukai riqon gaskiya
Su kai hukunci da gaskiya kuma suka riqi Allah daya
Su su kai hukunci da gaskiya kuma suka riqi Allah daya
Gasu yau kamar ba’a yi ba
Chorus
Bara in kawo misali don dai ku karkade kunnuwa
Idan gyara kui mani don shine cikar yan uwa
In ya ji laifi na dan uwansa bas hi bari yai yawa
Duk ma su qaunar Manzon Allah ni sun zaman yan uwa
Ni fa kun ga in ba kwa gyara mani aikin bai tsaruwa
Gara ma ace ban yi ba
Chorus
Ka duba farkon zuwan ka duniya kamar abun tausayi
Ka zo kana rusa ihu ba ka son zama kai daya
Jikin ka sam babu ‘quality’ ko riqon ka sai an iya
In ba barchi kake tabawa ba ba zaman lafiya
Ga shi ga nonon mahaifiyar ka abubuwan duniya
Ga shi yau kamar ba’a yi ba
Chorus
Ka fara girma a kan hakan sai ka fara bin yan gida
Suyi maka wayo da yar alewa a kai ka kofar gida
in wata ran ka fito da kan ka ka kasa gane gida
Sai ka bace don babu sani sai ka je ka mace gida
Ai ta cigiyarka day an gidanku har a gidan rediyo
Ga shi yau kamar ba a yi ba
Chorus
Ya dan uwa na tsaya ka duba irin halin rayuwa
Idan kana yi qiriniya an hana ka ka qi hanuwa
A yau da gobe a kwana a tashi me ye yake faruwa
A yanzu kai ke hani a daina sauyi cikin rayuwa
Duk masu hanaka na da sun qare wasu bas a rayuwa
Sun fice kamar ba’a yi ba
Chorus
Ko makarantarku in ka duba da wasu ne malamai
Suna zuwa ba su kauta rana ba latti jarumai
A yanzu Allah ya chanza daliban da duk malamai
Duk daliban na da yanzu ka ga duk sun zamo malamai
Toh ana hakan dai wata ran suma zaka ga duk sun wuce
Sun zamo kamar ba’a yi ba
Chorus
Toh haka famin rashi da samu abin yake faruwa
wata ran saboda karfin babu ka gan ka babu natsuwa
Ka dunga neman ka sabi Allah kullum kana tsarguwa
kana gani kai kadai Ya ware samun ka bai qaruwa
In kofar samu ta bude maka kuma sai kai yo dariya
Damuwa kamar ba’a yi ba
Chorus
Toh hakan in ka samu sukuni jikinka sai yai fari
Saboda tsabar jin dadi kai gida ka sake guri
Ka manca kowa ka mance komai gidanka ka sa katari
Ba ka tsoron yawan buqatu domin kau ka yi guzuri
Ai ta shirya tsari na duniya rayuwa tana ta tafiya
Sai ka wuce kamar baka yi ba
Chorus
Toh haka shima gado na mulki ake hawa mun gani
Wadansu gada suke wadansu saya suke mun sani
Ko ma ta yaya ka hau shi wata ran komai tsawon zamani
Dole a sauke ka ko ka sauka a sake baiwa wani
Toh in ma bah aka ba mutuwa ba ta kyale wani don wani
Sai ka wuce kamar baka yi ba
Chorus
Idan rashin lafiya ta zo maka duk sai ka kasa natsuwa
ka je ga ‘doctor’ ka je ga malam kullum ana ta adu’a
Ka shafa wannan ka kurbi wancan domin ka zam warkuwa
wata ran ka ganka ka warke ka sabe kana rayuwa
sai ka ganka malam ka warke ko ina kana kewaya
Cutuka kamar baka yi ba
Chorus
In ajali ya zo maka malam dole ka je lahira
Idan da ciwo ko babu ciwo zaka mace ba jira
Ko da ana baka dan turare ana jiqon sabara
Ko za ka je asibiti ka kwanta don kar ka je lahira
Karshe a zare ran ka ana kallonka a dole za’a hakura
Sai ka mace kamar ba a yi ba
Chorus
Allah ka zabe mu tun a duniya ka bamu kyawon hali
Ka sa mu dace da kwaikwayon Annabinmu mai kyaun hali
gaba dayan mu da duk musulmi Ilahu ya Adali
Muna tawassali da Annabi mai cika ta kyau da fasali
dukkan laifukan mu dam un ka yi Rabbana ka shafe mana
duk su zam kamar ba mu yi ba
Chorus
BArin na shaida Fati Musa a nan nake son in tsaya
Yar makarantar Nuruddini wajen kiran tarbiya
Ni dai kira nag a duk musulmi mu kyautato tarbiya
Domin da hakan ne ake wucewa a shallake lafiya
A dunga dai tunawa ya dan uwana komai tsawon zamani
Za ka zam kamar ba a yi ba
Chorus x 3