Labbaika Rasulullah
By Ramlatu Hafiz
Intro:
Assalatu wassalamu alaika ya Mahmuda
Za ku saurari qasida ne daga bakin Ramlatu Hafiz Kofar-Mazugal
Daga Halarat ta Imamul Ahbabu
Ra’isul Ahbabu Rasulallahi
As-Sayyadi Sharif Sani
Shehu Kudo Radiyal lahu ta’ala anhu
Karkashin jagoranchin Umar Abdul’aziz Baba fadar bege
A yi saurare lafiya
Labbaika Rasulallah x 2
Sarki na gwanin kyauta
Allah kai nake roqo
Don girman rasulallah
Gun ka na zo da dan koko
Amsa mun buqata ta
In samu in kai saqo
Duk mai son rasulallah
Yai ta kiran rasulallah
Labbaika rasulallah
Qara isa ka qara duk
Gun masani uban gaske
Mai matsayin da baya fado
Limami na yan aike
Al-arabiyyu al-mahadi
In aka ce ka ce take
Tauraron halitta ne
Babu irinsa sallallah
Labbaika rasulallah
Amma sai ince qara
Yau adadin mu waqar ka
In ko na salati ne
Gun zatin haqiqar ka
Nai suna da sunan ka
Nai motsi da humar ka
Ya Allah Muhammadu ne
Alqiblar ibadullah
Labbaika rasulullah
Allah sa da alaye
Al-ashabu tsarkaka
Dattija na madallah
Duk a saka su na roqa
Qauna ce zan kama
Nai murna da samu ka
Baba mu je Sharif Sani
Kai mu ga Daha sallallah
Labbaika rasulallah
Qarka da rasulallah
Son ka nake rasullah
Komai na bari na yar
Son ka nake inatallah
Yanzu a ganni ina murna
Kan a jima ina barna
Sai in ga ga ka na ganka
Kuma sai ka bace rasulallah
Labbaika rasulullah
Ga ka mutum kamar kowa
Ba shi yiwo a gane ka
Sai a taho ana bin ka
In aka zo a gaida ka
Mai face ganin maqiya
Ko fa ya kunu gaida ka
Mai masa hassada ya sani
Shine dai habibullah
Labbaika rasulallah
Yaushe so ya dauko ka
Ko kauna ta nuna ka
Ka wuce duk halitta fa
Tai furuchi ta furta ka
Allah ne ya zabe ka
Shi ya chike yana ce ka
Mai neman ya san Allah
Yai ta kiran rasulallah
Labbaika rasulullah
Mai neman haqiqar ka
A ce ya bari ya kyale ka
Ko mai fada zai fada
Ya tauye a haqqin ka
Mai cewa da kai zan ce
Ina ya gano ya gane ka
Komai ga shi hasken ka ne
Ina kake ne rasulallah
Labbaika rasulallah
Shi surarsa ta zarce
Mai kalla ya gane ka
Mai kallo yana kalla
Sai Allah ya canza ka
Shi Mahmudu sirri ne
Ina ka sani ka siffanta
Ni Mahmudu sonka nake
Ina kake ne rasulallah
Labbaika rasulullah
Zauna lau rasulallah
Dole a zo a gaida ka
Allah ne ya zabe ka
Yake gadin halittarka
In an zo a cuce ka
Sai Allah ya kare ka
Wa Allah yake wa haka
Tashi ka ce rasulallah
Labbaika rasulullah
Zababan halittu ne
Sun ce ni son ka ya abku
Na na riqe ciki da waje
Ni da yabon ka mun shaqu
Sirrin zuciya na ne
Na riqi son ka ya dauku
Lillahil abil Mahmud
Banda irin ka sallallah
Labbaika rasulallah
Allah kai kadai ya sani
Kai ya riqe abun auna
Ga ni a nan rasulallah
Shayyabar muradi na
Buri na guda daya ne
A bar ni da sonka abba na
Ko an nuna duk nasu
To su fade ka rasulallah
Labbaika rasulallah
Mai kyauta gwanin baiwa
Zul miqdaru ka gautu
Ni dai Daha ka yi mun
Ga ni a son ka na zautu
Ya Mahmudu dauke ni
In ka riqe ni na yantu
Na zama ya yantarta
Ga ni gaban ka sallallah
Labbaika rasulallah
Yan khairul zukata na
Sun aiko in gaida ka
Hanyoyiin jini da ruwa
Suna murna da samun ka
Mai kuka yana kuka
Yaushe zai ga fuskar ka
Ni goya ni ya Muhmud
Ya gaza jin ka sallallah
Labbaika rasulallah
Mai saita ni ya tsere
Na rasa inda zan nema
Mai ganar da ni ni ne
Ya kyale ni can dama
Na rasa gane yanzu da da
Ga ni a son ka na tsoma
Daharar son ka ga ni ciki
Ina hanya rasulallah
Labbaika rasulallah
Daha ka tausaya gu na
Ga rana tana garji
Wa na nan galabaice
Babu ido ga ran baci
Nisa da kai kusa ne
Jira ni rasulu ko na ci
Madallah da mai magana
Salamu alaika sallallah
Labbaika rasulallah
Labbaika rasulallah
Ya mausulu zal wajahi
Ahlan bika ya rasulallah
Kai amsa wa mai nema
Salatu alaika sallallah
Wal huwa sulu zatullah
Imamul ambiya’ullah
Ajidda kamalu ainaika
Ahlan bika ya rasulallah
Labbaika rasulallah
Mun ga balarabe ka kai
Ina mai so ya kyale ka
Gode wa maqagin ka
Da yai mana baige son ka
Sai kuma lamuni na biyu
Mu tashi da kai a tutarka
Ya Mahmudu don Allah
Yarda da ni rasulallah
Labbaika rasulallah
Bani guri in gaida shi
Haiqawa uban gayya
Ai har lafiya sarki
Sai da ka zo a ke koya
Annabi malamin kowa
Duk mai son ka ko yaya
Ya kawo haqqin Allah
Tunda ya so rasulallah
Labbaika rasulallah
Je ka abinka sha lele
Allah ne ya shirya ka
Daha irinka an qare
Ba za ai ba ko qaqa
Kai Allah yake qauna
Ko a ina ya nuna ka
Tashin qiyama ma
Kai ne sanadi rasulallah
Labbaika rasulallah
In kyawun halittu ne
Kai da ganinsa ya tsaru
Mai yalwar idanu ne
Ga gashin sa ya jeru
Allah ya halitta mu
Ya daura shi ya doru
Idan aka ce da kai taku
Ka tashi kace rasulallah
Labbaika rasulallah
Je ka da kyau uban kyawu
Daha irin ka ya koru
Ni dai Daha ka yi mun
Duk mai son ka ya gyaru
Kyakykyawa uban kyawu
Daha irin ka ya tsaru
Ya Mahmudu son ka nake
Ka mun uzuri rasulallah
Labbaika rasulallah
In kawa gurin Allah
Mai kayar da mai gaba
In an ja da kai a mutu
Don haduwar ba tai kyau ba
Je ka da kyau uban bayi
Son ka rasulu na karba
Duk rumtsi a bar ni da kai
Sayyidina rasulallah
Labbaika rasulallah
Ja mu ka kai mu jagora
Ya Mahmudu dan lele
Bar mu da son ka don Allah
Duk mu ji kai ka bar balle
Ya Mukhtaru ya Nuru
Daha isar ka sai gobe
Ga mu gare ka ya baba
Ya Mukhtar rasulallah
Labbaika rasulallah
Ni wallahi mun dace
Annabi ne wakilinmu
Sha kundun ku ban kowa
Duk mai son ka ya samu
Takawa da kyau asalu
Son ka a zuciya ka ku
Ba ranar da zai warke
Sai mun sadu sallallah
Labbaika rasulallah
Dole in tashi nai murna
Wane ne kamar nawa
Kai Allah yake duba
Shi ya nade ya damqa wa
Sai an zo da shi aka zo
Taska ce ta hutawa
Karshe shawara ta ni
Ku tashi mu so rasulallah
Labbaika rasulallah
Mai bege ku ce Ramla
Mai qauna ga annabi ce
Maulana ku ce Fada
Shi ya saka ni dimauce
In begen rasulallah
Kai wallahi mun dace
Qara mai cikar matsayi
Yai ta fadar rasulallah
Labbaika rasulallah