Wazobiya

Wazobiya
By Adam A Zango

Wazobiya…
Rayuwa sai da naira
In babu naira
Toh ko ka zam kwalele

Eyyyy yeh yeh yeeeh
Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Jama’armu ku saurara cikin kidanmu ba ma yaudara (wazobiya)
Kidan na bahaushe ne waqar ta Hausa ce kuma ba dabo (wazobiya)
Kalangu dan Hausa da ba’a yi mai jan kunnuwa (wazobiya)
Idan baku gane ba ina nufin Bature nai nufi (wazobiya)
Don ko da ya ji zai jinjina wa Hausa da al’uma

Ehhhhhhh
Yar yar yar lale lale kalangu shine kida

Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Mata nayi kira gaba dayanku sai ku yi tarbiya (wazobiya)
Duk kyawon mace in bada kyan halin kyawon kawai (wazobiya)
Mata kuyi aure ku dena zagayawan bariki (wazobiya)
Toh ga wata tai kwantai saboda kun ga bata da tarbiyya (wazobiya)
Yawan tarnaqiya yana ba mazaje sha’awa
Lai lai lale lale kalangu shine kida

A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)
Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Samari nayi kira a duniya ku bar yin yaudara (wazobiya)
Idan kunje tadi ku daina latsa yan’mata haka (wazobiya)
In ko kun qi ji toh in kuka haihu sai an maku (wazobiya)
Toh samari muyi sana’a mu daina dauke-dauke ga al’ummah
Toh duk nairar gaye idan da dan-hali nairar kawai (wazobiya)
Toh samari kuyi aure nai kira ku daina ruwan ido
Lai lai lale lale kalangu shine kida (eh.. ah.. ah.. toh..)

Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Kai ka ji kidan naira da ko mahaukaci na rausaya (wazobiya)
Duk tsufan tsoho idan ya ganta sai yai rausaya (wazobiya)
Toh kogi ya kawo ku zo mu sanya gora muyi hito (wazobiya)
In dai naira ce da ka biye ta yanzu ka bata (wazobiya)
Naira mai sa fada da uwa da uba kai duniya (wazobiya)
In dai kana da naira gidanku kai ne alhaji (wazobiya)
Ko da kai laifi gidanku babu mai yi ma fada
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Lai lai lale lale kalangu shine kida
Ehh Allah bani kudi in sai gida in je aikin Hajji (wazobiya)
Yaran zamani kuje ku yo karatu ya fi kyau (wazobiya)
Kai duk gayun gaye in babu ilimi hoto kawai (wazobiya)
Iliminmu na addini da boko ya zama garkuwa (wazobiya)
Toh mata kuyi ilimi domin ku bai wa ya’ya tarbiya (wazobiya)
Yarinya kyakykyawa ku zo ku ganta amma ba aji (wazobiya)
Ba Arabi ba boko cikin gidansu ta zama akuya meh (wazobiya)
Idan za’ai aure a dunga bincike kar ai tumun dare
Lai lai lale lale kalangu shine kida (ahah!)

Akwai wasu na magana da ni da Zango ba yan Hausa ba (wazobiya)
Kuce wacece ce kuce mai kar ce ta rage wa baqin ciki (wazobiya)
Idan kuma caca ta ci ta samu kurciya don suyi ciro (wazobiya)
Idan baka gane ba ka zo da Hausa zan ma tambaya (wazobiya)
Idan ka ban amsa in tarbatar bahaushe ne kake (wazobiya)
In dai a Hausa ne gidanmu babu baubawan bara (wazobiya)
Toh barewa ta yi burus cikin birgimarta a bariya (wazobiya)
Bar barna bara na Kare wa ke bin mutum ba tarbiyya (wazobiya)
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Eyyyy yeh yeh yeeeh
Ey a hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya
A hayye sama ruwa qasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

A hayye sama ado kasa kudi yan’matan duniya

Yan’matan duniya
Samarin duniya (wazobiya) x 5

Dinya
Samarin duniya (wazobiya) x 3