Sarakuna
By Naziru M Ahmad
Ba’a chinye toron giwa
Kai giwa da ranta toh sai dai kallo
Sarkin Kanonmu mai alfarma
Sarkin Zaria na nan shima
Sarkin Musulmi mai dumbin daraja
Sarakuna iyayen kowa ne
Ba’a chinye toron giwa
Kai giwa da ranta toh sai dai kallo
Sarkin Kanonmu mai alfarma
Sarkin Zaria na nan shima (gaishe ku)
Sarkin musulmi mai dumbin daraja (a’a)
Sarakuna iyayen kowa ne
Kare da kai bakwai sai kallo
Ita qarya fure take ba y’ay’a
Kamar mutum tana nan daidai
Ku yi shiga yana nan d’aid’ai
Kare da kai nakwai ko dad’a ne
Da ka gane shi ka san aljan ne
Zaki cikin awakai sarki
Kai kura da akuya sai dai kallo
Ruburbusa take ban taushi
Mai akuyar yana jin haushi
Ya labe da adda nan gefe
Yana jiranta ta kai ya kar ta
A gafara nace ga kyarkechi
Toh wannan batun yana chan baya
Girmansa ne kawai dan banza
Ga kwarjini kamar wata gabza
Ko akuya tana yi mai waigi
Da ta biyo shi sai dai yats tsere
Bara in waiwaya baya
In duba rayuwar baya
In binchiko hirar wata gawa
Sarki tura fa ta kai bango (iye)
Ka saka mu a loko
Zanche kake kamar wani soko
Hirar dabba muke yi ko waqa
Hirar Kanon kuke so ko Zazzau
A’a ka kyale baba ba kwa dan Zazzau
Na baya rauma komai sai doya
Idan ya ji ku kun san zai rama
Eh ko da ya jimu ba zai che shine ba
Ba shi a che mai dan Zazzau
Kuna nufin yana kalan dangi
Eh idan ya ji ko da ya haura (iye)
In yay yi Niger
Anka che Kano ne ko Zazzau
Sai yace Kanon nan ta fi su (gaske)
Ko manyansu don ba su so a gane sunansu (ku che da su)
Toh mu mun san su
Ya ake ana gane su
Toh mallam shigarsu mai ban tsoro che (ashe)
In sarki ne in ya taho kamar wani gwanki ne (gaske)
Sarkin Zazzau in ya shigo kamar wani giwa ne (gaishe ku)
A fagen mulki al’amuransa tamkar rana ne (haka ne uhm)
In ta haska duk duniyar ga kowa ya gane (iye)
Al’adunsu kamar ache mutanen farko ne (a’a)
Sarkin Zazzau ga tambura yau mun doka (hmm)
Naziru ne sarkin waqa (gaishe ku)
Ya shigo a Zaria gaisheka (uhn hm)
Lafia zaki ko wat taba ka yau sai ya koka
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
In gaida Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Eh gaisuwa ga babban dutse qaryarsu fa su kawo ma raini
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Eh gaisuwa ga babban jeji ko wab bache ciki sai dai ihu
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Eh gaisuwa ga babban sarki wanda in ya tashi kowa zai miqe
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Eh gaisuwa ga sahun giwa taken su wa na mai tsoron aiki
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Eh gaisuwa ga babbar fada baban sarakuna ‘ya’yan kirki
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Sarkin Musulmi Nazir sarkin waqa ne yake yi ma baiti
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaqi
Su dawisu masu ado
Sarkin garinmu mai kyan zamani
A Kanon dabo
Mu dai garinmu akwai ban mamaki
Lafia iska
Kowa ya kewaya zai sameka
Lafia tarko
Ko wash shigo ka zai sha mamaki
Ka ga dutsen murhu
Sai an aje ka ne za’ai dori
Sasarin alqali
Duk kan mazan gari na tsoron ka
Mai ado mai tsari
Dawisu yan gari na qaunar ka
Sarkin dabo
Mai martaba da alfarma
Mai wa diyansa ne hidima
Mu dai sarakuna yau mun samu
Sarakuna iyayen kowa
Mu daki tamburan sarki nazbi
Sarkin waqar da duk duniya duk an san shi
Mai kayan yaqin da duk duniya ke tsoron shi
Mai girma nazbi jama’arka na nan damanka
Shiga da kanka mai komai naira
Sarkin waqa a duk duniya na gaishe ka
Mu daki tamburan sarki nazbi
An baku mota yara
Sarkin waqar da duk duniya duk an san shi (uh hm)
Mai kayan yaqin da duk duniya ke tsoron shi (gaishe ku)
Mai girma nazbi jama’arka na nan damanka
Shiga da kanka mai komai naira (ga miliyan biyu ku sha mai)
Sarkin waqa a duk duniya na gaishe ka
Ga sarkin waqa (wane)
Baban Islama (gaske)
Mai haqora na azurfa maqogaronsa tamkar zinari (gaskia ne)
Fannin waqa (hmm)
Kun ga shi ya gawurta
In kana jin muryarsa sai kace kana susar kunne (sarki yana ji)
Don dadinta (ashe)
Shi ya gawurta (sarki)
Al’amuransa sai ikon Allah (ashe kaima sarki taka zata)
Lafia na hazbi
Sannu baban Islama (an hada maku da dawakai)
Buhun qaya sam ba’a chiko
In an chika ka kuma ba’a danne (gaskia ne)
In an danna mutum ya soke hannunsa (gaskia ne)
Ba wanda ya tsaya ma sai Allah balle mutum yace sai ya kar ka (sarki ya gode)
Babu mai ma sai Allah balle mutum yache yau ya daina (gaskia ne)
Allah ka kyautata karshenmu
Ameeeeen