Badossa
By Sa’adu Bori
Intro:
Hey jama’a
Gado sai dan gado
Ko wab bar gida gida ta bar shi
Dawakin Dosa kama suka tara
Mace mai wuya ta ba dosa
Kun san Makurdu ba ta fa dosa
Mai tufar kwarai ta fa dosa
Kun san talaka ba ta fa dosa
Aljani kuke wa tsahi
Aljanin kwarai sai gado
Ina Yanaye ina Fadaka
Ina Dan-Uje ina Chirido
Ko me kake dama tsatsama
An ba uwar makaho kashi
Don ba gani yake ga chido
Balle shi je shi ramo kashi
Bori ta kuna ba dosa
Dan talaka bashi ba dosa
Me ag gare shi balle shi bata
Aljanin kwarai sai gado
Ina Yanaye ina Fadaka
Ina Dan-Uje ina Chirido
Ohhhhh yah!
Ware Yanaje
Ai wayar Fadaka
Hai wayar Dan-Uje
Hai wayar Chirido
(Language)
Ku kwakkwkwafe mu yi wasa
Ina samarin bori
Ku maida kanku mutane
Ku gilgiza ku yi wasa
Ku rairaya ku yi wasa
Ku kwakwkwafe ku yi bori
Bori abun sha’awa ne
Bori abun murna ne
Wayyo samarin bori
(Language)
Ku kwakkwkwafe mu yi wasa
Ina magadan bori
Ku maida kanku mutane
Ku gilgiza ku yi wasa
Ku rairaya ku yi wasa
Ku kwakwkwahe ku yi bori
Bori abun sha’awa ne
Bori abun murna ne
Wayyo magadan bori
(Language)
Bori abun murna ne
Bori abun whara’a ce
(Language)
Ina mutanen bori
Bori abun sha’awa….
(fades away)