Angara

Angara
By Aminu Ala

Na dauki angaraaaaaaaaaaaaaa
Angara zan bankwana
Na yi guziri da ruwan salka
Kyawon tafiya mai dawowa
Ga ni zani bako mai ba
Zan roqo du’a’i gun kowa
Sai da mai rabo zan ganawa
Ranar rabuwa wa mai motsawa
Mai motsaawa
Mai motsaa zuciyar mai bankwana
Yau ina mai bankwana
Yau ina yin bankwanaaaaaaaaaaaaaaaa
Bankwana
Nai maku bankwana

[Chorus] x 2:
Na dauki angara
Na sagala
Za ni zani b azan dawoba
Na yi guziri da rowan salka
Zani zani b azan waigo ba

Wanda yai rashin taguwarsa in har ya hangi tandu zai duba
Na yi lalube sammai kassai ban yi katari da agwandu ba
Na gama bulayi na dawo
Na sani gaba dan na so ba
Ban yi katari ba ina kukan zuciya tana duba duba

Chorus

Wai garin masoyi ba nisa
Haka na ji wai ba karya ba
Na yi yunkuri har na qosa
Duk gulaguce na ban kai ba
Zuciya kamar ta faso ta fito
Don batai gamo da abun so ba
Na zubda hawaye har ya zam
Yanzu ma hawayen basu zuwa

Chorus

Raqumi da akal ko gafiya zata ja shi ba zai tsauri ba
Ya zamo kamar talalabo namijinga ba zai karfi ba
Jijiyar jikina harda qashi jinin jikin jiki ruwa ban dauke wa
Sun zamo kamar na jikin tsoho
Sakwa sakwa ba zai kwari ba

Chorus

I na ji na gani
na maida gani da jin kamar ba ayi ba aguna ba
na zamo kamar sabon hauka
jinnu jinnu ba ma wawa ba
na ji na sani inda muryata
zata kai jiki ba zai kai ba
raquri batu da abun son zuciya ba zai mun sauqi ba

Chorus

Angaraaaaaaaaaaaaaaaaaaa
Bankwanaaaa
Inai maku bankwana
Angaraaaaaaaaaaaaaaaaaa
Bankwanaaaa
Inai maku bankwana

Ya rage ni kukan zuciya
Mai sanya zazzabi ba qarya ba
Zuciya kamar dan kukuki
Don baqi ba zan maku qarya ba
Ta dushe gani na ga rauni da ya sa ka ba zan yi katabus ba
Zahirin jikina da badini ji nake kamar ba nine ba

Chorus

Rabbu kai ka san abincin zuciya dab a zan bude wa
Rabbu sa na samu rabo na ganawa da ni da abun duba
Eh na riga ni na san na yi gamo da katar na so da abun duba
Ya rage ni kyakykyawan karshe
In cika da imani Rabba

Chorus

Ga ni na zamo mai raunin bauta da ayyukan alkhairi ba
Ni Aminu mai yalwar sabo
Rabbu ka sani ba karya ba
Rabbana gafurun Ar-Rahaman Rahimi na sarki na rabba
Sa ni na zamo daga tsarin masu rabo a ranan nan babba

Chorus
Na dauki angaraaaaaaaaaaaaaaaaa
Angara zan bankwana
Na dauki angara
Angara zan bankwana
Na yi guziri da ruwan salka
Kyawon tafiya mai dawowa
Ga ni zani bako mai ba
Zan roqi du’a’I gun kowa
Sai da mai rabo zan ganawa
Gani mai rago wa mai motsawa
Mai motsawa
Mai motsa zuciyar mai bankwana
Yau ina mai bankwana
Yau ina yin bankwanaaaaaaaaaaaaaaaa

Chorus x 3