Rayuwa a Duniya

Rayuwa a Duniya
By Aminu Ala

Al ajjamiyya mai ban tsoro
Ahhhhhhhhhhh ahhhhahahaa
Hahhhhh ahaaaaaaaa ahhhhhhhh

[Chorus]:
Rayuwa a duniya tana ban tsoro
Lamarin duniya rawar yan mata
Rayuwa a duniya tana ban tsoro
Lamarin duniya rawar yan mata

Ga dan baba take yi wa horo
ya zama baba mai yin horo
alajabi mai ban tsoro

rayuwa a duniya mai tsoro
rayuwar mu yau akwai ban tsoro
tsoro Lamarin duniya rawar yan mata

Da farko ka tashi ne kana dan yaro
Duk wani motsinka zaka yi sa ne bisa horo
Sai ayi maka tarbiya cikakken horo
Ka ga ka akwai duk dake da kyau da na tsoro
Ka tashi na garkun kuruciya kana dan yaro
Ba aikin fari bare ka wahalta

Chorus

Larurarka gaba daya ake daukarta
A baka abinci da sutura ka tufata
A dora ka a turbar sani makaranta
In ba ka da lafia a kai ka ga likita
Muhallin kwancika ya zamo mai tsafta
A baka kulawa madi nagartar tsafta

Chorus

Watan wata rana a tashi baka ijewa
An samu waninka yanzu shi ake duba
Ba a mamarinka yanzu said dan baba
Ga ka madadin hawa uba dan baba
Ka zama mai yunkurin zamowa baba
Sha’anin duniya rawar yan mata

Chorus

Da ka data munzali na isa aure
A dan ququta da yan uwanka a daure
A sama maka yar budurwarka ta aure
Shi aure sha’aninsa sai fa an daddaure
Sai an jure riqe amanar aure
An bar ka day au da gobe dan tatata

Corus

Ahhhhhhhhhhh ahhhhahahaa
Hahhhhh ahaaaaaaaa ahhhhhhhh

Daga nan sai tsufa dake shiga ba ciwo
Abun da kake yi a da a yau ba shi yau
Ba ka tafia ta nesa balle yawo
Da kai tafiya yar kadan jiki sai ciwo
Babu ka katabus a gunka ka zamo wowo
Ka zamo sai dai ka ci abinka fa ka kwanta

Chorus

Fuskarka buzu buzu da gashin girma
A na nan sai furfura ta bayyana itama
Da ko tsayuwa ka wo jiki na kyarma
Zama kwanci tsayyuwarka duk ba dama
Tufata ta jikinka ta saki gyarawa
Raunin bargon jikinka ya nakasa ta

Chorus

A na nan yau lafia ta gobe da dama
A yau ciwo a a gunka gobe da dama
Ganin nesa a gunka yau ba dama
Zan ce in an yi sai an maimaitama
Abinci cikin hikima ka dan lalama
Sanna ka hadiye ka dan kikkifta

Chorus

A sannu zuwa hankali komai sai an ma
Abun da ake wa jinjiri a yanzu shi ake ma
Ya zam ko kasha kayi sai an wanke ma
Jimbintar lammarinka har su da zama
Wai karfe da quriciya ya koma
Rarrauna mar rashi labo na buqata

Ahhhhhhhhhhh ahhhhahahaa
Hahhhhh ahaaaaaaaa ahhhhhhhh
Ahhhhhhhhhhhhhhh

Chorus