Yanar Gizo

Yanar Gizo
By Aminu Ala

Ya mai tafi da kukan bayi
Kai mini agaji

Hehhh yanar gizo gizo
Yanar gizo gizo
Ta sa a danne haqqoqi na
Yanar gizo gizo

[Chorus]:
Yanar gizo gizo
Yanar gizo gizo
Ta sa a danne haqqoqi na
Yanar gizo gizo

Yanar gizo gizo
Yanar gizo gizo
Hanyar nishaduwar ruhi na
Yanar gizo gizo

Allah abun nufi da buqata
Na zo a firgice
Roqo na zo da shi sarki na
Sura a birkice
Qara na zo a kan ango na
Ya bar ni yakice
Yanar gizo gizon da ya aura
Zai sa na haukace
Ya kasa bibiya ka haqqi na
Ya bar ni dimace
Ya mai tafi da kukan bayi
Kai mnin agaji

Ki haquri fa mai daki na
Kar nayyi bincike
Na baki sutura da abici
Ya zaki firgice
Yanar giza gizai da na aura
Aikace aikace
Zan zaga duniya a taqi ne
Kafin a fargace
Hanya ta walwala da nishadi
Domin na yo fice

Ya mai tafi da kukan bayi
Kai mnin agaji

Chorus x 2

Na zo da durquso ango na
Ba ni da walwala
Ka qaurace muhallin bacci
Ka bar ni santala
Riqon ka na saka ni nishadi
Na sani walwala
Haqqin zamantakewar aure
Shi ke da falala
Yanar gizo gizo ango na
Ta zo ta fadala
Ya mai tafi da kukan bayi
Kai mini agaji

Hanya ta ilmantawa ce
Yanar giza gizai
Kafa ta saduwa da nishadi
Yanar giza gizai
Zango na debe kewar bayi
Yanar giza gizai
Saqo na saduwa da zumunta
Yanar giza gizai
Ba za ni bar kafar sadarwa
Yanar giza gizai
Ya mai tafi da kukan bayi
Kai mnin agaji

Chorus x 2

Yanar gizo gizo
Yanar gizo gizo
Hanyar nishaduwar ruhi na
Yanar gizo gizo
(x 2)

Chorus