Ina So In Yi Aure

Ina So In Yi Aure
By Babangida Kakadawa

Mai madi ka tallar zaqi
A’a toh shi kam mai zuma gida ya ke zaune ne
Ku fa malamai ku dauko littafanku tunda dai kune ne manya
Ku karanta ku fassara mana aya
A yanzu dai shine dai dai

Musulunci akwai nasiha a cikinsa
Wanda kuma Allah ya so
Manzon Allah yayi
Amma yanzu mun tsiro da al’adunmu
Masu son lalata mu
Don yau ba a baka aure ba kuddi
Wai su sun fi so su bai wa mai taqama da adda a cikin gida
Yana datse hannu
Suna samun kudi
Sannan za su bashi mata kyakykyawa

Ga ni ni kuma Babangida
Ina so in yi aure
Ina son auren diyan kabawa Babangida
Ni kuma ga ni bani yin minti dai ruwa

Ina son in yi aure
Ina son auren badakkara ni Babangida
Ni kuma ga ni ban da walki gindina

Ina son in yi aure
Ina son auren basakwkwata ni Babangida
Sannan nig a nib a batoranki ne ba

Ina son in yi aure
Ina son auren Fulani Babangida
Ni kuma ga ni ban da shanu ba rugga

Ina son in yi aure
Ina son auren Bagobira yar Gobir
Amma ni ba ni son ace bawa ne ni

Ina son in yi aure
Ina son auren Bazazzaga ni Babangida
Ni kuma ba ni cin faten doya kullum

Ina son in yi aure
Ina son auren Babarbara ni Babangida
Sissan nan na gwal ke sa ni ina sauna

Ina son in yi aure
Ina son auren Bakambara ni Babangida
Ni kuma ga ni bani son daukar kaya

Ina son in yi aure
Ina son auren diyan Kanawa Babangida
Ni kuma ga ni ban da tsagen baki
Sannan ni ga ni ba gajere ne ni ba

Ina son in yi aure
Ina son auren Bakatsina ni Babangida
Katsinawa na dikko dakin kara
Kunya garesu ba dai tsoro ba
Ina son auren Bakatsina ni Babangida
Ni kuma ga ni bani son yaqi ko kusa

Ina son in yi aure
Ina son auren Bazamfara ni Babangida
Ita tana qaunata ni ina ra’ayinta
Ubanta sai yacce a’a

Ita tana qaunata ni ina ra’ayinta
Ubanta sai yacce um um

Wani da bata qauna wai das hi za’ayi aure
Toh don Allah a daina auren dole
Saboda auren tilas kasa diya yawon banza

Ba wulaqantarce a yanzu sai marar ilmi
Ko wai ilmi ku gane ya kece raini
Ba wani mai yi mai

Da sana’a
Da fahimta
Kowa da wadda Allah nayyo mai

In sahiya ta waye
Wadansu na aikin gona
Wadansu suna office
Wadansu karatu
Wadansu ko waqa sun kai
Hakanan Allah yas so

Tsuntsu asalin gidansu kan icce ne
Kifi asalin gidansu bai wuce rafi ba

A’a ni dai Babangida
Duniya ko tai man kida b azan taka ba
Duk wanda ya taka ya ga kwan

Cin hakin sama sai raqumi
Awaki ku ci kyasuwa
Ku ko ku yi hankuri
Inda Allah bai kai mutum ba qaqa zai kai can

Akuya ba ta layya in ga rago
Duk na Annabi na san ba zai lalace ba