Buje

Buje
By Sa’adu Bori

[Chorus 1]:
Haba yarinyar nan
Don Allah juya
Idan ba ki juya ba
Kin chi amana ta
Mai abun dadi kawo
Marar abun dadi koma

[Chorus 2]:
Rabbana Allah gyara ya jalla
Rabbana Allah gyara ya jalla

Chi gaba mu shika na maku talla
Shi yai angon Husaina malam
Yai yan tagwaye na kanbo malam
Ku bani in yi kidina
Kidi abun da na gada yaro
Gadon da ban raina ba dan malam
Duk dan da Allah ke so
Ba za ya jin kunya ba yarinya
Allah ka bar mani Kifti yarinya
Kibi amanar Almu dan yaro
Allah ka bar mani Balu
Halima amanal Manu dan yaro
Allah ka bar mani Dudu dan yaro
Maryama amanar Dudu dan yaro
Malam daga rumbuna ka ga gero tsaba
Malam daga taga ka ga hasken daki
Malam daga buje ka ga dan matsatsa
Malam daga buje ka ga yankan Allah
Wasu lunguna-lunguna sai tshoyun mata
Wata wawuyar runguma sai manyan mata
Jawara da gashin baki aurenta sai wanzammai dan yaro

Chorus 1

Rikita har juyawa ka ga kwaddo da machiji dan yaro
Wannan kidin nono ne wadda bata da nono ta ji haushi malam
Gindi abun juyawa tun ba na yarinya bad an malam
Gindi abun juyawa tun ba na mai gashi ba dan yaro
Wasu lunguna-lunguna sai tshoyun mata
Wata wawuyar runguma sai manyan mata

Tshoho da gashin baki ga hurhura ga tsage
Shina cikin dan tohin yarinya
In ya wuce Allah shi ji qai nai malam

Bujeeee…

Tsoho sai da tsohuwa gajera sai gajere
Kai dogo sai da doguwa gajera sai gajere
Kai tsoho sai da tsohuwa yaro sai da yarinya
Kai Tsagami sai da tsohuwa ni kau sai da yarinya
Kai Dili sai da ya Assa ni kau sai da yarinya
Kai duniya mai abun mamaki
Yau ake gobe sai labara
Dan Adam da jibin gomatsi
Nai wani dan zama bias chibi
Nai wani dan doro bias chibi
Nai wani fakaka bias chibi
Kai nai wani qememe bi sa chibi
Kai nai haka nai haka na daga buje
Kai nai haka nai haka na daga chinya
Ashe mata wayo suke mana
Abun dadi na chan kasa kasa
Oh wo woooo

Chorus 2 x 2

Duniya ta yabke ki kullum tana juyawa da yaro

Rabbana Allah gyara ya Allah