Hadiza

Hadiza
By Sa’adu Bori

Intro:
Kai mata!
A riqe darajar aure da kyau
A bar hushi da ikon Allah
Don Ikon Allah ya wuce hushi

[Chorus 1]:
Lale Hadiza lale lale
Hadiza yan malamai
Kun ga Hadiza ta burge ni

Ina cikin yawo na na ga Hadiza ta burge ni
Yara suna kiranta amare mata suna kiranta amare
Ni ina cikin yawo
Na ga Hadiza ta burge ni
Na aure diya ta amare
Zama da kishiya tilas ne ba dan uwar gida na so ba x 2

Chorus

Ko wat taba Raqumi shi ga hauka Jaki bai kula da bugu ba x 2

Chorus

Yara suna kiranta amare mata suna kiranta amare
Zama da kishiya tilas ne ba dan uwar gida na so ba
Ko wat taba Raqumi shi ga hauka Jaki bai kula da bugu ba

Gyara gida Hadiza
Hutu naki ne
Gyara wuri Hadiza
Hutu naki ne
Gyara mujinki Hadiza
Hutu naki ne
Toh ladabi biyayya
Hutu naki ne
Ba ni ruwa Hadiza
Sai ta durqusa
Ba ni hura Hadiza
Sai ta durqusa
Ba ni tuwo Hadiza
Sai ta durqusa
Ruwan wanka Hadiza
Sai ta durqusa (x 2)