Ba Rabuwa

Ba Rabuwa
By Umar M Sharif

Ba rabuwa da ni da ke
Ba rabuwa

Ba rabbuwa alkawarinki na rike
Gamon jini so hadduwar mu yayo daide

Eh ba rabbuwa alkawarinka na rike
Gamon jini so hadduwarmu yayo daide

A ra’ayina ni ke da ke
Zuciyata kauna take

Gunki dai zanzo in fake
In babu ke ni gawa nake

Da kin kira ni zan zo a take
Da kaina ba maganar inyi aike

In zo da mota koko da keke
Mu kewaya duniya da ni dake

Zama dake yanayin daban yake
Ba yanda zanyi in nuna wa duniya su gani ma

Hahaha son ka ya shige a cikin rai ya kwanta
Shi ya zam silar samun lafiyata

Da kai naso in kariya rayuwata
Ka zam mijina ni kuma in zamma mata

Zaman mu dole zai inganta
Tunda ba muyi wa junanmu mugunta

Ka zamo jini ni hanta
Rabuwarmu zai wuya na furta

Farin cikina sai karuwa yake
Ku duba fuska yanayina hakka za ku gani ma

Hamsa’ ina ta miko miki godiya
Tunda kin saka ni ina dariya

Tarbiyarmu ta hanna ashariya
Babu kyau a tayar da hayaniya

Da ke mun zauna lafiya
Da mun saba kuma mun shirya

Ba ja da baya da sonki na tsaya
Kuzo ku koya so abin mu yau ba dama

Eh ka ban farin ciki nima na baka
Tunda dai bani da tamkarka

Ban aminta ba inga ka koka
Bare ace nazama matar ka

Lokachi zai saka
Dani da kai za mu tsallaka

Ka ganni ga ka
Cikin gidanka

Sunnah mudaika
Da tabbacin mun girma