Yar Fillo

Yar Fillo
By Umar M Shareef

War war war yar fillo
Juyo mana yar fillo… fillo
Hahaha
A hah!
Toh kai!
Ahah!
Yar yar yar
Ahah!
War war war
Yar fillo!
Ahah! A’a! Ahah!

War jan juyo mana yar fillo
A kaina ga kwaryan nono
Ruga nima zan je
na biku da shanu niyi kiwo

[Chorus]:
War jan juyo mana yar fillo
Yar fillo akwai tallar nono
Shanu na tatsa
Yar fillo adaji sai kiwo

War jan menene dan yaro
Aje kwaryarki mu sha nono
Ni dai zani riga
ka bar ni a daji nai kiwo

Ni burina in same ki
Ye yeyye yar yan nono
Gidanku su yarda in auranki
Ye yeyye yar yan nono
Yayana su yi kamananki
Ye yeyye yar yan nono
Daga ranar na girma
Yar fillo gidana na kama

Chorus

Yau ka same ni tsakar hanya
Ye yeyye yar yan nono
Farko da agunmu akwai kunya
Ye yeyye yar yan nono
Soyayya a raina nai niyya
Ye yeyye yar yan nono
Da ma dai kai baya
Tallar nono na kawo

Chorus

Yar fillo ki yi mani alfarma
Ye yeyye yar yan nono
Da ganinki gidanku akwai kima
Ye yeyye yar yan nono
Ki yar mun ya ki zan nema
Ye yeyye yar yan nono
Soyayya ban dama
Gonar qauna niyi kiwo

Chorus x 2

Yan samari yau ka rude ni
Ye yeyye yar yan nono
Lafazinka da dadi ya ja ni
Ye yeyye yar yan nono
Soyayya dutse ta yi gini
Ye yeyye yar yan nono
Duk tunani na yai rauni
A kanka nake yin kai kawo

Chorus

Kambun soyayya na daura
Ye yeyye yar yan nono
Lamarin qauna kuma na gyara
Ye yeyye yar yan nono
Lafazi daddada na tara
Ye yeyye yar yan nono
Suma ya qura
Ki yi mini barka na dawo

Chorus

War jan juyo mana yar fillo,
A kaina ga kwaryan nono
in a e i zan je
Na biku da shanu ni kiwo

Chorus

War jan menene dan yaro
Aje kwaryarki mu sha nono
Ni dai zani riga
Ka bar ni a daji nayi kiwo

Chorus